Tuesday, June 9, 2015

Shugabancin Majalisa: Lissafi Ya Kwacewa Shugabancin APC


ZAB'EN SHUGABANCIN MAJALISA: LISSAFI YA K'WACEWA SHUGABANCIN APC

Abin mamaki ne a wannan lokacin uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta nuna fushi ko damuwa akan zaben da akaiwa Sen. Abubakar Bukola Saraki​ da Dogara Yakubu a matsayin sabbin shugabannin majalisar Dattawa da ta wakilai. Sune fa Shugabannin APC suka dinga bin su Bukola da Gwamnonin PDP biyar da sukai mata tawaye gida gida suna rokonsu Allah su shigo APC, suka amsa wannan kira suka shiga aka nuna musu babu wani bambanci kowa daya ne.

Wadan da suka sha wahalar kafa APC akai fatali da su, aka nuna su ba komai bane, aka fusatasu da gangan suka d'an su fice, aka nuna su Bukola sune mutanan kirki. Sai yanzu da aka kafa Gwamnati ake neman kwashe musu kafa, su Bukola suka had'a kansu suka samarwa da kansu makoma, sannan ne shugabancin APC na kasa suka fahimci cewar wadannan shigogo ne a cikin jam'iyyar? 

Ba shakka wannan zabe da akaiwa Bukola Saraki da Yakubu Dogara ya dace, domin ko babu komai ya nuna tsantsar Demokaradiyya, domin hakan ya tabbatarwa duk wani wanda yake jin cewar shi ne ya mallaki APC sai abinda yake so shi za ai, to zai gane cewa kan mage ya waye, ba kowa bane Bayerbe. Idan ana batun Demokaradiyya to tilas a bar kowa da ra'ayinsa. 

Wannan Zabe da akaiwa Bukola Saraki da Dogara Yakubu yana bisa doron Demokaradiyya, hakan kuma ya dace. Ai idan ba lissafi ne ya kwacewa shugabancin APC ba, jagororinta a baya sune suka zuga 'yan majalisun ACN da ANPP da CPC da wasu daga cikin mambobin PDP akan su bijirewa 'yan takarar da PDP ta tsayar su zabi  Aminu Waziri Tambuwal, kuma akai hakan. Shin tsammaninsu PDP bata dauki darasi akan abinda ya faru ba?

A ganina wannan shi ne tsantsar Demokaradiyya,  domin samun wannan shugabanci zai taimakawa shi kansa Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ wajen aiwatar da aikin sa ba tare da tunanin cewar wani mutum shi kadai ra'ayi sa ya rinjaye na kowa ba, kuma abinda yake so shi za ayi. 

A dan haka wannan babu abinda yake nufi zai tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mutum daya ba zai iya saka al'ummar Najeriya a aljihunsa shi kadai ba, ya zama ba abinda zai faru a Najeriya sai abinda yake so. Ina amfani da wannan damar wajen taya sabon Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ikweremadu murnar wannan zabe da akai musu, haka shima Dogara muna taya shi murna.

Yasir Ramadan Gwale​ 
06-06-2015 

No comments:

Post a Comment