Tuesday, June 9, 2015

KWAD'O: Sabon Shugabancin Majalisar Dattawa


KWA'DO: SABON SHUGABANCIN MAJALISAR DATTAWA

Wannan sabon shugabanci na majalisar Dattawa da aka samu a yanzu bai zowa da dama da mamaki ba, domin tuni masu sharhi akan Shugabancin Majalisar sukai hasashe abin da ya faru. Kamar yadda Jam'iyyar APC mai mulki ta bayar da sanarwar fitar da wadan da take son a zab'a a sabon Shugabancin Majalisar, inda suka zabi Sen. Ahmed Lawan A Matsayin Shugaban Majalisa da kuma George Akume a matsayin mataimakina,  haka kuma APC sun zabi Hon. Femi Babanjamila a matsayin dan takarar shugabancin majalisar wakilai.

Kwastam yau da aka tashi zabe, a cikin sanatoci 108 da ake da su, an samu guda 57 sun zabi Abubakar Bukola Saraki​ a matsayin sabon Shugaban Majalisa Dattawa, zab'in da tun farko ya sabawa Shugabancin APC. Hakan dai na nufin sanatoci 51 da basu zabe ba, ba zasu iya wani katabus a a canza wannan sabon shugabancin ba, abin mamaki shi ne yadda PDP ta samu manyan mukaman Majalisar guda biyu, wato mataimakin Shugaban majalisar Dattawa da kuma Shugaban masu rinjaye da ake kira Senate Leader.

Da akwai alamar turka-turka a wannan shugabancin na majalisa, domin David Mark tsohon Shugaban Majalisa ya samu mukamin Senate Leader duk kuwa da cewar ya fito daga PDP da take a matsayin jam'iyyar Adawa a majalisar, abinda kowa zai zura ido ya gani shi ne yadda za'a nada Shugaban marasa rinjaye na majalisar,  shin zai fito daga PDP ne ko kuma daga APC?

Idan har PDP ta sake samun mukamin Shugaban marasa rinjaye bayan samun shugabancin masu rinjaye to lallai PDP nada karfi a wannan majalisa ta takwas, a gefe guda kuma, idan APC ta karbi Shugaban marasa rinjaye to ba shakka ankai keyarta kasa, domin a matsayinta na jam'iya ma mulki ta koma mai adawa a majalisar duk kuwa da cewar ita ke da rinjaye. Tuni dai sabbin shugabannin majalisar da suka had'a da sabon Shugaba Saraki, da mataimakinsa Ike Ikweremadu da Shugaban masu rinjaye David Mark suka sha rantsuwar kama aiki.

Kada mu manta kowa ce jiha a Najeriya nada wakilcin sanatoci uku yayin da Abuja ke da sanata guda daya, haka kuma, kwanakin baya an bada sanarwar rasuwar sabon Sanatan APC daga jihar Borno, abinda yake nuna sanatoci da suke kasa sune 108. Zamu ga yadda wannan sabon Shugabancin Majalisa zai wanye da bangaren zartarwa.

Yasir Ramadan Gwale 
09-06-2015

No comments:

Post a Comment