Friday, June 12, 2015

Mutuwa Rigar Kowa


MUTUWA RIGAR KOWA

A 'yan kwanakin nan naga mutane da yawa suna ta bayar da labarin rasuwa nan da can, wasu iyayansu wasu 'yan uwansu, wasu 'ya 'yansu wasu dangi wasu Abokai da sauransu da dama Allah ya jikan Musulmi.

Hakika nima a Makon jiya da wannan satin anyi rasuwa uku da ta girgizani ainun. Abokinmu Muzammil Ahamad Jihar yaro matashi da kuma wasu Abokanmu su biyu da suka rasu sakamakon kad'e su da mota tayi a Makon da ya wuce, rasuwar da ta girgiza mutane da yawa a Khartoum.

Haka kuma a wannan satin na samu labarin rasuwar Shamsiyya Lawal Gwale, Alal hakika naji wannan rasuwa sosai, tare aka sanyamu a Gwale Primary da Shamsiyya, muna mutunci da zumunci har zuwa lokacin da tayi aure. Ina yiwa mijinta Basiru Miller Gwale ta'aziyar rasuwar ta, da kuma 'yan uwa da dangi musamman Babban yayanmu Pharm. Ibrahim Lawal​ Allah ya jikanta ya gafarta mata.

Yadda muke karanta labarin rasuwar wasu haka muma watarana za'a karanta labarin rasuwar mu. Zato zo mana ko mun shirya ko bamu shirya ba, Malamai suka ce babu wani wa'azi ko nasiha ko Jan hankali da ya kai mutuwa, domin ita ce, mai yanke komai, wanda duk ya Rasu to shi kenan haihata haihata tasa ta riga ta kare.

Dan haka irin wadannan labari da muke samu na rasuwa nan da can, tabbas, wata rana muma zata zo kanmu, muna sane ko mun gafala. Dan haka muji tsoron Allah mu sauya halayenmu daga munana zuwa kyawawa, daga masu zafin zuciya zuwa masu saukin rai,  daga masu tsanani zuwa masu hakuri. 

Ya Allah ka jikan mamatanmu,  ka yafe musu laifukan su da dukkan kurakuransu, Allah ka sadar da su da RahamarKa, mu kuma da muka Rage Ya Allah ka sa mu cika da Imani, Allah kasanmu kasan halayenmu, Allah ka yafe mana laifuka da kurakuran da mukai maka muna sane ko mun gafala, Allah kai mai afuwa ne kana son Afuwa, Allah kai mana afuwar laifukanmu,  Allah ka lullubemu da RahamarKa. 

Yasir Ramadan Gwale​
12-06-2015

No comments:

Post a Comment