Friday, June 5, 2015

Tatsuniyar 'Yan Shiah Kan Salman Rushdie


TATSUNIYAR 'YAN SHIAH AKAN SALMAN RUSHDIE 

'Yan Shiah sun kasance suna yaudara mutane da yawa ta hanyar gaya musu cewar, akwai wani mutum da yayi kalaman batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da addinin Musulunci mai suna Salman Rushdie, wanda yake zaune a England. A dan haka Shugaban addininsu na Iran Ayatoulla Kumeini ya sanya lada na rabin dukiyarsa ga duk wanda ya kamo ko ya sare masa wuyan Salman Rushdie. 

Ayi ta nunawa kauyawa da basu fahimci Shiah ba, wai irin kaunar da su 'yan Shiah suke da ita ga Ahlulbaity da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Kaga mutanen da aka yaudara suna ta kabbara suna ihu tare da jinjinawa Khumeini. Amma kuma wannan a bayyana take a garemu cewar yaudara ce tsagwaronta suke yi. Haka su Zakzaky ke ta yiwa mabiyansu wannan Tatsuniyar akan Salman Rushdie. 

Sai gashi 'yan Tijaniya a Kano sun zagi Manzon Allah Sallallahu Alaihi WaSallam,  amma bamu ji Zakzaky ya bayar da rabin dukiyarsa ga wanda ya kamo ko ya sare wuyan Abdul Inyass ba. Wannan na daya daga cikin dalilin da ke tabbatar wa da al'umma karya da yaudara da 'yan Shiah da 'yan darika ke yi na cewa sune masu kaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. 

Wallahi duk wanda ya kama bin hanyar wani ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ba, zai yi nadamar da bazata amfani shi ba a ranar gobe kiyama. Bin Tafarkin Manzon Allah shi kadai ne dacewa, Riko da Sunnah shi ne hakikanin shiriya. Allah ka tabbatar da mu akan bin Sunnar ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah kayi dadin tsira a gareshi da Alayensa da Sahabbansa da wadan da suka biyo Tafarkin su da kyautatawahar ya zuwa ranar sakamako.

Yasir Ramadan Gwale 
06-06-2015

No comments:

Post a Comment