Tuesday, April 1, 2014

Ko Ranar Lahira Sai Anyi Bincike Balle Funtua!!!


KO A RANAR LAHIRA SAI ANYI BINCIKE BALLE KUMA A FUNTUA!!!

Batun da na yi jiya dan gane da abinda ya faru a FUNTUA, ya sanya wasu da dama suka kasa fahimtar abinda na fada, watakila bisa ga Jahilci ko Son Rai. Wasu da dama sunyi maganganu na zagi da cin mutunci da makamantansu wadan da daman na yi tunanin masu fama da tsukakken tunani zasu yi hakan. Laifi na kawai na ce YA KAMATA A YI BINCIKE KAFIN DAUKAR DUKKAN WANI MATAKI. Sau da dama rashin gudanar da bincike na Adalci ya sanya muke yin kwakyariya akan abubuwan da ba haka zahirinsu yake nufi ba, daga baya kuma a ji kunya. Wasu su farma wadan da ba suda laifin fari balle na baki.

Ya na da kyau mutane su sani cewa ko a ranar lahira Allah bazai yiwa kafirai hukunci ba sai ya binciki Annabawa da Manzannin da ya aikowa Bani-Adama ko sun isar da sako, tare da cewa shi Allah shi ne masani abinda yake fake da wanda yake boye, ya san da cewa Annabawa da Manzanni sun isar da sakonSa ga Talikai, amma dan saboda ya kafawa Bani-Adam hujja sai ya bincika ko Annabawa da Manzanni sun isar da sakon da aka turo su da shi Tsarki Ya Tabbata A Gareshi Subhanahu Wata'ala. Shi ya sa ko a Hajjin Bankwana sai da Manzon Allah SAW ya tambayi taron Sahabbai HAL BALLAGHTU? Shin Na Isar Da Sako A Gareku, suka amsa da cewa Ka Isar Ya Manzon Allah, Nan ta ke Manzon Allah SAW ya yi addu'ah ya ce ALLAHUMMA FASH-HAD Ya Allah Ka Shaida, Sahabbai sun yiwa Manzon Allah SAW Shaida cewa ya isar da sakon Ubangiji.

Haka kuma, dukkan sauran Manzanni Allah zai tambayesu shin sun isar da SakonSa ga Talikai, idan sukace sun isar sai Allah ya tambayesu waye shaidar ku, sai suce, shaidarmu shi ne cikamakin Annabawa Muhammad Dan Abdullahi Allah ka yi dadin tsira a gareshi da zurriyarsa da Sahabbansa da wadan da suka bi tafarkinsu da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako Sallallahu Alaihi Wasallam; daga nan sai Allah ya tambayi Manzon Allah shin Annabawa sun isar da sako, sai yace eh! Allah kai da kanka ka bani labari cikin alqur'an kace Manzanni sun isar da sako, sannan sai Allah yayi hukunci ga kafirai. Duk wannan bincike ne Allah da kansa zai yi Ranar Alkiyama domin ya kafa hujja ga kafirai.

Al-Qur'ani tun daga farkonsa har karshensa cike yake da kissoshin Annabawan da suka Gabaci Manzon Allah SAW da bayanin sakon da Allah ya turo su da shi. Dan haka min babi Aula idan har Allah da kansa zai yi bincike dan tabbatar da zahirin abinda ya faru, ace Bil-Adama a Funtua zai dauki hukunci da moolanka ya zartar ba tare da yin wani bincike ba. Allahumma sai dai fa idan bincike ya nuna cewa ga abinda mutum ya aikata kuma aka yi masa hukunci dai-dai da abinda ya aikata, wannan ba'a zalince shi ba.

Dan haka, duk wadan da suke zaton cewa kawai dan wani al'amari ya zo musu zasu dauki hukunci ba tare da yin sahihin bincike ba, su yi duk abinda suka ga zasu iya, to su sani Allah baya zalunci, kuma sai ya sakawa duk wanda aka zalunta ko da kuwa Musulmi ne ya zalunci wanda ba Musulmi ba.

YASIR RAMADAN GWALE
01-04-2014

No comments:

Post a Comment