Tuesday, April 8, 2014

Shirin Gwamnatin Tarayya Na #YouWin: Anyi Mana Shal

SHIRIN GWAMNATIN TARAYYA NA #YouWin: ANYI MANA SHAL!

A ranar juma'ar da ta gabata ne, hukumar kula da gasar da gwamnatin Tarayya da hadin guiwar wasu kungiyoyi suka kafa dan yaki da talauci da taimakon al'umma dan dogaro da kansu, ta fitar da sakamakon gasar na farkon wannan shekara. Ita dai wannan gasa ana cin kudi kama daga Naira Miliyan Daya har zuwa Naira Miliyan Goma (10M). Abinda kwamatin yake bukata ga duk mai sha'awar shiga gasar shi ne, cikakken bayanin sana'ar da mutum yake son yi idan ya samu Nasarar lashe gasar, wannan a takaice shi ne, abinda kwamatin suke da bukata a karon farko dan samun Nasarar shiga gasar.

Haka kuma, wannan shiri na #YouWin shiri ne da aka yi masa tanadi na musamman, ta yadda babu wanda zai karbi kudin #YouWin ya kwanta akansu, idan kuwa ya yi haka zai iya samun kansa a gidan yari, ya zama dole ga duk wanda ya samu Nasarar lashe gasar ya aiwatar da dukkan abubuwan da ya tsara a takardun shiga gasar da ya gabatarda suka bashi damar lashe gasar.

Ga duk wanda ya kalli sakamakon gasar na ranar Juma'arnan 04-04-2014 da jaridar #DailyTrust ta buga, ya san cewa Mu mutanan Arewa an yi mana kwaf-daya inda aka kwashe mana kafafu, mutanan kudu su ne wadan da suka ci gajiyar wannan shiri inda suka samu Miliyoyin kudi, domin kuwa kaso 80 na wadan da suka samu lashe gasar 'yan Kudu ne kiristoci, a yayin da Mutanan Arewa a cikin gasar ba su wuce kashi 20 ba.

Sakamakon wannan gasar bai zo min da bazata ba, domin kuwa, mutanan Arewa suna da matukar sakaci akan duk wani abun alfanu irin wannan. An jima ana kiran 'yan Boko da suka kammala karatu ba suda aikin yi da su shiga gasar amma da dama suka yi biris, kuma wannan dama ce da babu wadan da zasu shiga gasar sai 'yan boko domin, kowa shi ne zai yi bayanin abinda yake son ya yi, dan masu duba takardun shiga gasar Turawa ne, za su yiwa duk wanda ya gabatar da takardunsa tambayoyi ta yadda indai ba shi ne ya tsara bayanansa ba, to ba zai iya gamsar da su ba. Amma, haka aka yi mana kwaf daya a wannan gasa.

Lallai ya kamata mu farka, mu san inda yake yi mana ciwo, mu kuma sani cewa kanmu muke cuta, muna kara sharewa talauci gindin zama a cikinmu. Babu wani shiri da ake samun makudan kudi kamar wannan shiri na #YouWin amma abin takaici 'yan Bokonmu wadan da ake ganin su ne zasu ci gajiyar shirin amma abin takaici wadan da suka lashe gasar daga cikin kaso 20 da aka bamu raba-dai-dai mukai da 'Yan Kudu mazauna Arewa. Allah ya maganta mana irin wannan rashin kulawa..

YASIR RAMADAN GWALE
08-04-2014

No comments:

Post a Comment