Monday, April 7, 2014

Su Waye Suke Kai Hare-Hare A Zamfara?



SU WAYE SUKE KAI HARE-HARE A ZAMFARA?

Akwai matukar daure kai da damuwa ace har yanzu an kasa gane ko kama wadan da suke yin irin wannan mummunan kisan gillah a jihar Zamfara. Ya faru ba sau daya ba, ba sau biyu ba, an kashe daruruwan jama'a an kone gidaje da dama an kore dubban shanu, amma har yanzu an kasa gane masu yin wannan aikin Ta'addancin, ina hukumomin tsaron kasa da na jihar zamfara suke?

Babban mashawarcin kasa ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki dan Sokoto ne mai makwabtaka da Zamfara, sannan babban sufeto janar na rundunar 'yan sandan Najeriya Muhammad Dikko Abubakar dan jihar Zamfara ne duk da ya koma Kano da zama, haka kuma, sabon Ministan tsaron Najeriya wanda duniya gaba daya ta shaida gogewarsa da kwarewarsa ta fuskar tsaro Janar Aliyu Muhammad Gusau (Mutumin Kirki) duk 'yan jihar Zamfara ne, ina gwamnan Zamfara Dakta AbdulAzizi Yari suke? Ta yaya duk wadannan gogaggun mutane masana harkar tsaro ta sirri da ta sarari suke, mahaifarsu na ci da wuta ganga-ganga amma ace an kasa shawo ko magance lamarin. Anya kuwa akwai gaskiya a kasarnan?

A dan karamin sanin da na yiwa Janar Aliyu Gusau na san cewa mutumin kirki ne mai kaunar kasarnan da san cigaba, mutum ne mai kokarin kamanta gaskiya a cikin lamuransa. Ina kyautata masa zaton cewa ba zai taba bari a inda yake da iko a cutar da al'ummar Arewa ba, balle kuma mahaifarsa inda aka yanke masa cibiya ba. Lallai ya kamata a yi wani abu dan kawo karshen wannan lamari. Allah ya jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya. Su kuma masu aikata wannan kisan, muna tuna musu fadin Allah Taala cewar. "Ya zuwa gare shi ne makoma ta ke".

YASIR RAMADAN GWALE
07-04-2014

No comments:

Post a Comment