Sunday, April 6, 2014

RWANDA: Hutu Da Tutsi Bayan Shekaru 20 Da Kisan Kare Dangi

RWANDA: HUTU DA TUSTI BAYAN SHEKARU 20 DA KISAN KARE DANGI

Yau al'ummar kasar Rwanda dake Kudancin Afurka suke bikin tunawa da Shekaru 20 mafiya muni a tarihin kasar da suka shude, haka kuma, ana lissafa wadannan shekaru ashirin a zaman daya daga cikin wani mummunan lokaci da duniya ta yi tozali da shi a wancan lokacin. Wannan lokaci da ya shude, wutar kabilanci da tsananin gaba da kiyayya ita ce ta ruru tamkar wutar daji a zukatan al'ummar kasar Ruwanda inda kabilun Hutu masu rinjaye suka farwa kabilar Tusti mai matsakaicin yawa da kisa babu ji babu gani, kamar an aiko su, bayanai sun nuna cewa wannan yaki ya barke ne a ranar 7 ga watan Afrilun 1994 zuwa tsakiyar watan Yuli, ance fadan an shafe kwanaki 100 cif-cif ana zubar da jini, inda aka yi asarar akalla rayukan mutune Miliyan 2 tare da jikkata sama da mutum dubu dari biyar zuwa Miliyan daya a yayinda da dama suka tsere suka bar kasar zuwa makwabtan kasashe domin samun mafaka.

Kasashen duniya tare da majalisar dinkin duniya a wancan lokaci duk sunyi Wadarai da abinda ya faru a Rwanda, inda suka kira lamarin da cewa Kisan-Kare Dangi ne, ko kuma kisan-kiyashi. A yau da ake bikin tunawa da wannan rana, Shokolo Bangoshiya ta fashe da kuka wurjanjan a yayin da take tuna irin abinda ta gani na kisan rashin Imani a dab da shiga birnin Kigali.

Bayanai sun tabbatar da cewa, duk wannan mummunan kisan gilla da aka yi a cikin kwanaki 100, anyi shi ne da kananan makamai da suka hada da wuka da gatari da lauje da gariyo da barandami da matsefata da tsitaka da fatanya da sauransu. Babu shakka jini ya kwarara a kusan dukkanin kasar ta Rwanda, kabilun Tutsi duk inda suke a kasar sun ga ta kansu, musamman inda 'yan Hutu masu rinjaye suke da yawa, haka kuma, ance suma kabilun Tutsi sun dauki fansa a inda suke da rinjaye a kasar.

Wani abin mamaki da Hutu da Tutsi, shi ne, tamkar Hausa da Fulani suke, domin yare daya suke magana da shi wato KINYARWANDA. A cewar wani masanin tarihi bambancin tsawon mitoci ne kadai tsakaninsu.To, amma, sai turawan mulkin mallaka na Belgium suka kara fito da wasu abubuwa da su ka kara fito da wasu bambance bambance kamar katin shedar zama dan kasa, suka kuma fifita kabilar Tutsi daga bisani kuma suka koma suna fifita Hutu. Farko sai da aka fara yada farfagandar kiyayya kan Tutsi cewa sune matsalar Rwanda akai amfani da kafafen yada labarai, akwai kungiya ta musamman da Hutu suka kafa wadda suka sanya ma suna Akai da yarensu ma'ana "masu kai hari tare" kafin daga karshe da kansu su harbo jirgin Habiyarmana.An tafka rashin imani gaban duniya.a farka cikin mace a fito da dan tayi,a fasa ma shi madiga.sai da kogin Tanganyika ya cika da gawarwaki fal.

Wannan kazamin yakin basasa ya shiga kundin tarihin duniya tun kimanin shekaru 20 da suka gabata, haka kuma, al'ummar duniya ta jima tana yiwa al'ummun Hutu da Tutsawa kallon wasu irin mutane marasa Imani da jin-kai.

A yanzu bayan shekaru 20 da wannan kisan kiyashi dukkan al'ummar kasar Rwanda da suka hada da Hutawa da Tutsawa suna yin nadamar irin rashin Imanin da suka nunawa junansu, tare da bayyana takaicinsu akan abinda ya faru. Babu wani alkhairi a cikin yaki face Nadama!

Muna fatan Allah ya kare Duniya daga shaida irin kisan rashin Imani irin wannan. Allah ya kare kasashenmu daga fuskantar Matsananciyar gaba irin wannan.

Yasir Ramadan Gwale
07-04-2014

No comments:

Post a Comment