Monday, April 7, 2014

KWANAKI 100: Gwamnatin Kasar Masar Na Tsare Da Ma'aikatan Gidan Talabijin Na Al-Jazeerah

KWANAKI 100: MA'AIKATAN GIDAN TALABIJIN NA ALJAZEERAH NA TSARE A KASAR MASAR

A dan wannan lokacin kasar Masar ta zama wata kasa mafi hadari ga 'yan jaridar kasashen waje. Tun bayan turka-turkar da ta kawo haramtacciyar gwamnatin Adly Mansur karkashin jagorancin Abdel-Fattah Alsisi dan kama karya, kasar Masar ta shiga takun saka da dukkan wasu 'yan jaridu masu tsage gaskiyar abinda yake faruwa a kasar Masar din. Mafiya yawancin 'yan jaridar da suke bayyana ra'ayin talakawan kasar Masar na can kasa akan halin da kasar take ciki, sun fuskanci matsi da kyara da dauri da duka da kisa daga haramtacciyar gwamnatin Masar.

Kusan duk wani dan jarida da zai bayyana gaskiyar abinda ke faruwa, to kai tsaye Gwamnatin Mansur da take samun umarni daga Al-Sisi dan kama karya, zasu kirashi a matsayin mai goyon bayan kungiyar Ikhwanul Muslimin da aka kwace musu Mulki ta karfi da yaji. Gwamnatin Masar ta fara garkame ma'aikatan gidan Talabijin na Al-Jazeerah tun kusan watan Augustan bara inda suka kama Abdallah Al-Shami wanda dan asalin kasar Masar din ne suka daure shi a kurkuku, saboda zarginsa da ake yi da nuna goyon bayan Hambararriyar Gwamnatin Mursi a irin rahotannin da yake aikawa sashin Larabci na AlAl Jazeera Mubasher Misr قناة الجزيرة مباشر مصر, wannan ta sanya gwamnatin ta rufe tashar a kasar, kuma aka hana mata watsa dukkan wasu shirye shirye a kasar.

Bayan dan lokaci kadan, kuma aka sake kame wasu ma'aikatan Al-Jazeerah da suka hada da Peter Greste wanda yake aiko rahoto ga sashin turanci wanda kwararren dan jarida ne tsohon ma'aikacin BBC, daga nan aka kame Bahry Muhammad da Muhammad Fahmy 'yan kasar Masar din masu yiwa sashin Turanci na Al-Jazeerah aikai, har kawo yau din nan da suka cika kwanaki dari suna cigaba da kasncewa garkame a gidan kurkuku. Akan zalinci.

Kamar yadda muka sani ne, gidan Talabijin Na Al-Jazeerah mallakar Gwamnatin kasar Qatar ne, wadda ke zaman Kasa daya tilo a a cikin manyan kasashen larabawa da suka yi na'am da gwamnatin Mursi da kuma kungiyarsa ta Ikhwan duk kuwa da adawar da suke nunawa da wanzuwar Mulkin dimokaradiyya a yankin kasashen Larabawa, to wannan shi ne abinda bai yiwa su Al-Sisi dan kama karya dadi ba, dan haka suka sanya kafar wando da duk wani mai goyon bayan Morsi, dan haka laifin kasar Qatar ya shafi gidan talabijin na AlAl Jazeera English.

Iyaye da dangin 'yan jaridar da ake tsare da su sunyi ta yin kiraye-kiraye akan a sake musu 'yan uwa, amma abin tamkar bara a gidan bebe, gwamnatin kama-karya ta Masar ta yi kememe ta ki sauraronsu, duk kuwa da irin tofin Ala-tsine da aka yi akan keta hakkin 'yan jarida a Warshinton da London da Brusels da New York, amma gwamnatin Masar taki sauraron kowa.

Al-Jazeerah dai na cigaba da kiran a sakar mata ma'aikata ba tare da wani sharadi ba, domin basu aikata wani laifi da ya keta dokar kasar Masar ba, a cewarsu.

YASIR RAMADAN GWALE
07-04-2014

No comments:

Post a Comment