Wednesday, March 5, 2014

Boko Haram

BOKO HARAM: Daga lokacin da 'yan Arewa suka yarda cewar Masu kai wadannan hare-hare 'yan Boko Haram ne, ba CAN ko Gwamnatin Tarayya da ake zargi bane, sannan ne aka fara gano bakin zaren warware matsalar. Amma, Muddin muka cigaba da kawar da kai daga masu laifi, muna dorawa wasu na nesa laifin, to, lashakka, cewar har furfura ta riskemu zamu cigaba da fama da wannan tashin hankali Allah ya kiyaye. Dole a fadi magana ta gaskiya akan abubuwan da suke faruwa a Arewa Maso gabas, da dama wadan da ba a Maiduguri ko Yobe suke ba, ko kuma ba su da alaka da yankin sukan yi tutsun cewar SAM wannan abin ba 'yan Boko Haram bane, wasu suce CAN ne; wasu su ce Shugaban Kasa ne da sauran zantuttuka irin wadannan.

Na tabbata, babu yadda CAN ko Shugaban kasa zasu shirya mana irin wannan makarkashiya a ce mun kasa ganewa, duk da muke zargin Shugabanninmu da gazawa wajen kare muradunmu, Tabbas CAN ko Shugaban kasa ba zasu shirya mana haka ba su yi shiru su zuba ido, ai lalacewarmu bata kai haka ba, gidadancinmu bai iso wajen ba.

Idan zamu ga laifin Gwamnati akan wannan batu bai wuce na rashin bin sahihan hanyoyin magance matsalar ba. Domin ita gwamnati tana daukar mataki ne bisa la'akari da rahotannin masu yin Sharhi akan al'amuran tsaro, wadan da galibinsu a Abuja ko Legas suke, suna kwance suke fadin abinda basu fahimci hakikaninsa ba.

Sannan wasu, musamman 'yan siyasa daga Arewa, suka ki fahimtar gaskiyar lamarin da gangan saboda siyasa. Lallai ya kamata mu fahimci cewar, shifa Shugaban Kasa wannan al'amari gobarar titi ne a gareshi, domin idan akwai abinda yake akan rikicin bai wuce "taking advantage" ba, muna cigaba da yiwa batun tutsun fahimta, muna kara basu damar zaftare makudan kudaden da ake warewa akan tsaro.

Ya rage namu, ko dai mu tsaya mu fahimci wannan ala'amari a zahirin yadda yake, dan tunanin mafitarsa, ko kuma, mu cigaba da yiwa abun gurguwar fahimta, muna kara kwana da tashi cikin tashin hankali da zullumi. Allah ya kiyaye.

YASIR RAMADAN GWALE
05-03-2014

No comments:

Post a Comment