Monday, March 17, 2014

NAJERIYA: Abu Biyu Ne Zai Iya Faruwa Bayan Zaben 2015!

ABU BIYU NE ZAI FARU BAYAN ZABEN 2015

Mai kwarmin ido da wuri yake fara yin kuka inji 'yan magana. Yana da kyau mu kalli zaben 2015 da ke tafe mu kuma fadawa kanmu gaskiya. Ga duk wanda ya kalli yadda siyasar 2015 ta ke tafiya ya san cewa babu wani abu da zai iya hanawa shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan cin zaben nan sai KADDARAR ALLAH, domin alamu sun tabbatar da cewa muddin an zuba zabe sai ya koma shugabanci a karo na biyu, ko da kur'ar Halal ko da ta Haram. Wannan wani abu ne sananne, wanda ba a boye yake ba.

Yanzu alamu sun nuna cewa Shugaban kasa, yafi 'yan Hamayya kwarin guiwar cin zabe mai zuwa, domin abinda ake kira "Body Language" dinsa ya nuna haka, a yayin da a gefe guda, masu ikirarin hamayya basa nuna wani kwarin guiwa akan zaben, idan banda hayaniya a kafafen jaridu da Internet. To mai zai faru idan Shugaban kasa ya kuma cin zabe? Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da mutane da dama zasu iya bayar da amsarta, idan aka dubi abinda ya biyo bayan sakamakon zaben 2011.

Abu guda biyu ne zai iya faruwa idan Shugaban kasa ya wuce a karo na biyu. Abu na farko, shi ne, irin Misalin abinda ya faru a kasar THAILAND, inda masu adawa da Shugaban Kasar Yunlak Shinwatra suka fito kan tituna suna bore tare da kona tayoyi da yin tofin Alla-tsine ga shugabar. Sai da ta kai, masu zanga-zanga sun dangana har zuwa fadar Shugaban kasar, inda suka yanke wutar lantarkin da ta shiga fadar, suka sanya siminti suka tottoshe kokfofin shiga fadar, suka farfasa tagogi da gilasai da daddaye tile din da aka shimfida akan tituna, suka yi zaman dirshan, ba shiga ba fita an baiwa mahaukaci gadin kofa, har dai, daga karshe suka saduda suka koma gidajensu ba tare da bukatarsu ta Tunbuke  shugabar ta biya ba.

Abu na biyu da zai iya faruwa, shi ne, abinda ya faru a kasar UKRAINE, inda masu zanga-zanga suka fito cikin tsananin sanyin dusar kankara suna kiran, shugaba Victor Yunokovich ya sauka. Wanda daman sun taba yin haka a 2004 inda suka kori Shuagabn lokacin Yushechenko. Sun kona tayoyi tare da bankawa gine-ginen gwamnati wuta. Har dai shugaban yaga babu sarki sai Allah, ya arzce ya kama gabansa. Masu zanga-zanga suka ci nasarar fatattakar shugaban kasa. Wanda hakan ya yi sanadiyar ballewar wani yanke da ake kira CRIMEA, inda kasar RUSSIA da ke san dawo da karfin tsohuwar rusashshiyar SOVIET ta mamaye yankin. Duk da cewa yankin ba shi da wani muhimmanci ta fuskar Tattalin arziki, ba zai nakasta Ukraine ba ko da kuwa ya koma karkashin Russia.

Daya daga cikin biyun nan na iya faruwa a Najeriya bayan zaben 2015. Ko dai masu zanga-zanga su ci nasarar korar Shugaban Kasa kamar yadda ya faru a Ukraine, wanda abu ne mai kamar wuya wai gurguwa da auren Nesa. Ko kuma, irin abinda ya faru a kasar Thailand ya faru a Najeriya, masu zanga-zanga bayan sun gama bore a titunan biranen Kano da Kaduna da Bauchi da Sokoto da Katsina su koma gida bayan sun gama artabu da jami'an tsaro, wadan da zasu mutu sun mutu, wadan da zasu karye sun karye a zubawa Sarautar Allah ido, a kuma yi tunanin tarawa a 2019 ga mai yawan RAI.

Babban abin tsoron, shi ne barkewar rikicin kabilanci da na Addini a musamman jihohin Arewacin Najeriya. Wanda za'a shiga gaba kura ne . . . , dan ga hare-haren da ake cewa ba'a san ko su waye suke kaiwa ba, kuma ga al'amuran bayan zabe. Allah ya kiyaye ya kare asarar dukiya da ta rayuka.

YASIR RAMADAN GWALE
17-03-2014

No comments:

Post a Comment