Saturday, June 2, 2012

Shin Ko Ya Dace Iran ta Mallaki Nukiliya?



 
Shin Ko Ya Dace Iran ta Mallaki Nukiliya?
Kusan anjima ana ta sabatta juyatta akan wannan lamari na mallakar makamashin Nukiliyar Iran. tun lokacin tsohon shugaban hukumar binciken makamashin Nukiliya ta duniya IAEA Muhammad el-Baradai ake ta kai ruwa rana da kasar Iran akan wannan nufi nata na sarrafa makamashin Uranium wanda shi zai bata damar mallakar Makamashin Nukiliya. A yanzu haka kasar Iran na aikin sarrafa makamashin Uranium daya kai kashi 20 cikin dari, wanda shi ne hukumar IAEA karkashin sabon shugabanta Yukiyo Amano suka yarjewa kasar ta sarrafa.
Abu na farko sai mu fara da tambayar menene makamin Nukiliya? Hakika makamin Nukiliya kusan a wannan duniyar babu wani makami daya kaishi illa, domin illarsa ba wai kawai wadan da aka harbawa ba kadai harda mutanan da zasu zo nan gaba wannan makami na iya yi musu illa, bayaga ga halaka dubban rayuka a lokaci guda, da hasarar dimbin dukiya da sauransu. Idan muka koma baya muka duba yadda Amerika ta gwada wannan makami a shekarar 1945 akan kasar Jafan a garuruwan Hiroshima da Negasaki inda masana suka ce ya kashe akalla mutane kimanin 200,000, wannan makami yayi musu mummunar illa kwarai da gaske, wanda masana suke cewa wannan illar tana binsu haryanzu.
Tun bayan wannan mummunan harin ta'addanci da Amerika takaiwa kasar Jafan ne kungiyar kasashen NATO da kasashen duniya suka zauna inda sukayi yarjejeniyar mallakar makai wadda ake kira da sunan Kyoto Convention ko Kyoto Protocol, inda akayi yarjejeniya tsakanin manyan kasashen duniya da kananan kasashen da ake kira Third World Countries da kuma matsakaita, hakika wannan yarjejeniya cike take da tsabagen zalunci da son kai, da kuam rabon kura( wato idan aka baiwa kuara rabon nama, sai ta ware mai yawa ta sa agabanta, sannan tace kowa ya dauki na gabansa) wannan shi ne abinda Amerika da NATO da kuma kwamitin tsaro na majalisar Dinkin duniya sukeyi, domin wannan yarjejeniya ta yarda wasu kasashe su mallaki wannan makami, sannan kuma ta hana wasu mallaka, sannan wasu kuma da suka riga suka mallaka aka daga musu yatsa akan cewa to ya isa haka, kasashen da suke da wannan makami sun hada Amerika, Ingila, Faransa, Rasha, Cana, Indiya, Pakistan, Italiya, Jamus da Israela da sauransu.
Shin ana iya sarrafa makamashin Nukiliya ta wani fanni na ci-gaba? Hakika, wannan batu haka yake, ana iya sarrafa wannan makamashi na Nukiliya domin samar wutar lantarki da dangoginta. Don haka ne a farkon lokaci kasar Iran ta dage akan cewa ita wannan makamashi nata na zaman lafiya ne inda tace zata sarrafa domin samar da wutar lantarki da wasu abubuwa na ci-gaban zamani, amma da yake su kasashen Turai da Amerika sun san mece gaskiyar manufar Iran akan wannan nufi nata sukayi ta Tirjiya.
Me yasa Iran ta dage akan sarrafa makamashin Nukiliya? Ya zama wajibi a yi wannan tambayar shin meye ya sanya kasar Iran ta dage akan mallakar wannan makami ko makamashi, Na farko sanin kowane kasar Iran itace kasar da bata Larabawa ba kuma tafi kowacce kasa kusanci da kasashen Larabawa da suke a yankin Gabsa ta Tsakiya, kamar kuma yadda yake a bayyane cewa kasar Iran kasace ta 'yan Shi'a Rafilawa, sannan kuma kowa yasan da cewa kasashen da Iran take makwabtaka da su kasashen Musulmi ne Sunni, kuma manufar Iran akan musulmi sunni ba boyayya bace, wannan yake kara nuna cewa lallai akwai abin tsoro idan kasar Iran ta mallaki wadan nan makamai, kasancewar kasashe irin su Saudiyya da Bahrain da Qatar da Kuwat da Iraqi da United Arab Emirate kusan duka wadan nan kasashen musulmi ne sunni wadan da suke zaman doya da manja da Iran don haka mallakar wannan makami ga kasar Iran babbar barazana ce ta zaman lafiya ga kasashen Gulf ko gabas ta tsakiya.
Shin idan Iran ta mallaki makamashin Nukiliya a wane mataki take? Sai mu yi tambaya shin da gaske ne, cewa wannan makami da Iran ke shirin mallaka barazana ne ga Israela? Ko kuwa barazana ne ka kasashen musulmi sunni? Shin Iran a wane matsayi zamu kalleta da wannan makami, shin kamar yadda ake cewa Pakistan itace kadai kasar Musulmi da ta mallaki Nukiliya; itama Iran idan takai ga mallaka za'a sanyata ne a sahun kasashen musulmi masu Nukiliya ko kuwa a zaman kasar Shi'awa mai makamin Nukiliya? Saud a yawa nakanyi nazarin wannan tambaya shin a wane matsayi zamu ajiye Iran dangane da batun Nukiliya, bantaba zaton Iran bazata yiwa kasashen Musulmi barana da wannan makami na Nukiliya ba idan har takai ga mallakarsa. Sannan anya kuwa ba kura ake kokrin lullubowa da fatar akuya ba, a nuna mana cewa Amerika na adawa da Iran akan wannan batu, amma kuma daga gefe guda sun sahalemusu, domin ayi amfani da Iran wajen farautar 'yan ta'adda a kasashen musulmi, kamar yadda ya bayyana cewa dukkan irin abin day a faru da marigayi Saddam Hussein da taimakon kasar Iran aciki dari bias dari, Allah dais hi ne masani mai hikima, muna rokon kuma yak are rayukan musulmi daga barazanar wannan Nukiliya na Iran.
Sannan kuma, a daya bangaren akwai kasar bani Yahudun Israela wadda da ita da Iran suka sanya Larabawa a tsakiya, itama dai kasar Israela tana da wannan makami na Nukiliya, sannan kuma tana dari-dari da Iran a yadda ake nuna mana, amma kuma a zahirin lamari Iran da Israela bakinsu daya ta wasu fannoni da daman gaske, na farko Amerika a yadda suke nunawa suna tsoron wannan makami na Iran barazana ne ga kasar Israela wadda ke zama 'yar lelen kasar Amerika, don masana sunce makamin Nukiliyar Iran zai iya zuwa har Tel Aviv idan an harboshi daga Iran, wanda kuma wannan babbar barazana ce ga cigaba da mamayar da kasar Israela keyiwa kasar Palasdinu, amma a fadarsu.
Haka kuma, masana sunce akalla ana bukatar makamashin Uranium ya kai kashi 90 kafin a sarrafa makamshin Nukiliya, wanda ya zuwa yanzu Iran tana aikin dafa ko sarrafa kashi 20, Shugaban Hukumar IAEA na yanzu Yukiyo Amano ya jagoranci wata tattaunawa a birnin Baghdad na kasar Iraqi akan makamashin Nukiliyar Iran, inda anan ne ya bayyana cewa zai je Tehran don ganawa da hukumomin gwamnatin Ahmadi Nejad akan wannan batu, kuma tuni akajiyo saukar Amano a Tehran inda ya gana da Ali Larjani akan wannan batu kafin ya wuce don ganawa da AhmadiNejad.
Abin tambaya wace iran Dimokaradiyya Amerika da majalisar Dinkin Duniya suke yi da ta hana wasu kasashe rawar gaban hantsi?  Misali  da yawanmu muna sane da yadde ake kara samun takun saka da kasar Amerika da kuma Koriya ta Arewa akan wannan batu na mallakar Nukiliya, itama dai wannan kasar dake can yankin gabas mai nisa, ta mallaki wannan makami mai hadarin gaske. Amerika itace kasar da tafi kowace kasa kurarin Dimokradiyya shin wace irin doka ce ta baiwa Amerika damar mallakar dukkan irin makamin da ta ke so amma ta hana wasu kasashe? Duk da surutan karya da sakataren tsaron Amerika Leon Paneta da Suzan Rice da Hillary Clinton da Ban-Ki Moon suke ta yi akan wannan batu, ya kamat idan har da gaske dimokaradiyyar ake son yi ta gaskiya to bai kamata wata kasa ta ringa dannewa wata kasa hakki ba ko kuma hanata rawar gaban hantsi.  Ya Allah ka kare al'ummar musulmi daga barazanar wadan nan makamai masu matukar hadari a doron kasa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment