Saturday, June 30, 2012

Me Ya Sa Tarihi Ke Maimaita kansa?


Me Ya Sa Tarihi Ke Maimaita Kansa?
Kusan a bayyana ya ke cewar amsar wannan tamabaya gajeruwa ce. Shakka babu kamar yadda muka sani sau da dama a rayuwa tarihi kan maimaita kansa daga lokaci zuwa lokaci, muna iya cewa dalilin da ya sanya tarihi ke maimata kansa shi ne, saboda mutane basu cika daukar darasin da ke cikinsa ba, hakika Allah ya halicci dan adam mai yawan mantuwa, wasu lokutan mantuwa takan zama abin so kwarai da gaske, wani zubin kuma mantuwa takan zama abin zargi.
Hakika darasin da ke cikin tarihi, wata makaranta ce babba da kalilan daga cikin mutane ne sukan kammalata da kuma samun kyakykyawan sakamo, wasu kuma sukan fara su kasa gamawa, har mai aukuwa ta auku akansu, a lokacin da wadan da sukaci jarabarwar tarihi ke murna wasu kuma na cizon yatsa da dana sani a lokacin da ba tada amfani.
Idan muka duba tarihi shekaru 42 da Gaddafi ya yi yana mulkin kasar Libiya sunzo karshe ne a ranar 20 ga watan oktoban 2011; lokacin da guguwar sauyi ta kada kuma tayi awon gaba da shi, Gaddafi dai baiyi amfani da darasin da ke cikin tarihi ba don day a kalli wadan da suka gabaceshi da wata kila abinda ya sameshi bai sameshi ba, haka shi ma Saddam Hussein na Iraqi mulkinsa ya zo karshe ne a shekarar 2006, Husni Mubarack na Masar shima mulkinsa yazo karshe ne a shekarar 2011 da su Ben Ali na Tunisiya da Ali Abdallah Saleh na Yemen duk mulkinsu yazo karshe ne a shekarar 2011. Duka wadan nan shugabanni da suka gabata da sun kalli tarihi kuma sun yi aiki da shi da watakila basu fada cikin halin da suka fada ba, kuma abinda ya samesu babban darasi ne ga na baya.
Idan kuma muka kalli shugabanni irinsu Robert Mugabe na Zimbabwe wanda yake akan karagar mulki kusan tun shekarar 1980, da kuma Paul Biya na Kamaru wanda shima ya shafe tsawon Shekaru akan mulki kusan tun 1982 yake a karagar mulki, shima Yuwairi Musaveni na Uganda ba a barshi a bayaba wajen diban dogon lokaci akan mulki wanda shima yake akai tun daga shekarar 1985 har kawo yanzu; lallai wadan nan shugabanni ya kamata suyi karatun ta nutsu kuma su kalli tarihi su yi tunanin gobe da kuma abinda zai faru nan gaba, Shakka babu kamar shekaru uku da suka gabata, idan kace ka yi katarin haduwa da Husni Mubarack na Masar a sansanin shakatawar nan na Sham el-sheikh ka ce Muhammad Mursi shi ne magajinsa a shekarar 2012 watakila ya ce maka haka bazata taba faruwa ba, amma da yake tarihi baibar komai ba yau ga Mubarack na raye kuma yana kallon wani yana shugabancin Masar ba shi ba.
Shugaba Fidel Castro na kasar Cuba kusan shi ne ya yi katarin gamawa da mulkinsa lafiya. Hakika zaka iya cewa Castro ya taki sa'a, domin yabar karagar mulki ba dan al'ummarsa sun juya masa baya ba kamar yadda ya faru da Mubarack da Ben Ali da sauransu, hakika tsufa ya yiwa castro shigar sauri a lokacin da duniya ta ke kara komawa sabuwa kuma sabbin al'amura ke kara faruwa, tunani ke kara fadada, shakka babu da ba dan tsufa ba da Castro ana nan ana damawa da shi a harkar shugabanci da siyasa, to haka dai tarihi ke tafiya da al'amura daban daban, dukkan wadan nan abubuwa da suka faru tarihi ne yake ta maimaita kansa, sai dai wasu da yawa musamman daga cikin masu mulki sun gafala daga daukar darasin dake cikinsa.
Lallai masu Mulki su sani kuma su hankalta cewa babu wani mulki ko shugabanci da yake dawwama face mulkin ubangiji(tsarki ya tabbata a gareshi) subahanahu wata'ala, lallai duk wani mai mulki da yayi zaton zai dawwama shakka babu ya yaudaru da rudin duniya, kuma tunaninsa ya gaya masa karya, shuwagabanni da dama da suka gabata sunyi kokarin cigaba da kasancewa bisa karagar mulki amma kodai mutuwa tayi musu yankan hanzari irinsu marigayi Sani Abacha, ko kuma cutar nan da bata jin magani ta cimmusu basu shirya ba wato tsufa, ko kuma su fuskanci bore daga al'ummarsu duk kuwa da cewar sun kyautatawa al'ummar tasu wajen samar musu da abubuwan bukata kamar irinsu Gaddafi.
Mukam munyi katari a Najeriya ba mu da irin wannan matsala ta masu son tsawaita mulki. Hakika muma shugabanninmu ba dan basu da wancan tunani ne yasanya basa tsawaita mulki irin na su Mugabe ba, sai dai Najeriya ta sha bamban da sauran kasashen duniya, watakila saboda yawan kabilu da mabambanta ra'ayi da kuma yanayinmu na kudu da Arewa ko Muslmi da Kirista.
Inda Najeriya ta yiwa sauran kasashen Afurka shal shi ne muguwar sata da zamba da rubda ciki akan dukiyar al'umma da kuma cin hanci da rashawa da ya yi mana katutu. Shakka babu idan mutum yace babu wata kasa a duniya da ta ke da gungun barayi a matsayin shugabanni kamar Najeriya bai yi karya ba, irin satar da aka dibga a Najeriya bana jin akwai wata kasa a Nahiyar Afurka da za'a yi mata irin wannan satar ta kai labara. Tundaga lokacin da aka samu mulkin kai 1960 zuwa yau irin kudin da 'yan Najeriya suka sata daga aljihun gwamnati ya isa a rushe kasashen Afurka gabaki daya a sake gina sabuwar Afurka mai dauke da dukkan ababen bukata na rayuwar yau da kullum.
Hakika Allah ya albarkaci Najeriya da dumbin arziki na fitar hankali, tun daga albarkatun kasa da ma'adai babu iyaka ga man fetur da dangoginsa ga kuma albarkar jama'a sannan a gefe guda kuma ga mugayan barayi miyagu azzalumai. Cutar da ta ke damun 'yan Najeriya kusan tafi ta kowace kasa a Nahiyar Afurka, duk da cewa a Uganda da Kamaru da Zimbabwe da muka bada misali da su shugabanninsu sun tsawaita wa'adi da wakaci ka tashi amma sun wadata al'ummarsu musamman da wutar lantarki idan ka kwatatnta su da Najeriya. Abin da ake kira wutar lantarki dan Najeriya sai dai ya gani a wata kasar amma shikam ta gagareshi samarwa a kasarsa duk kuwa da arzikin da Allah ya huwa cewa wannan kasa tamu.
A kasar Brazil da kwanan nan shugaban kasa ya je, kuma tafiyar ta tayar da kura, a lokacin tsohon shugaban kasar Luis Inacio Lula De Silva sun kashe kudi kimamin dalar Amerika Biliyan Biyar ($5B) wajen samar da wutar lantarki mai karfin mega watt 120,000 a cikin shekara daya kacal, haka nan kurkusa ma kasar Afurka ta kudu sun kashe dala biliyan daya ($1B) wajen samar da wuta me karfin mega watt 5,000 acikin shekara daya suma. Idan kuma muka dawo gida Najeriya gwamnatin da ta gabata ta Cif Obasanjo ta kashe kudi dalar Amerika biliyan goma sha shida ($16B) akan samar da wutar lantarki, amma yanzu zancen da muke babu kudin kuma babu wutar lantarkin, haka nan Allah ya jarrabemu da muggan barayi a matsayin shugabannin.
Bana jin a duniya akwai wasu mutane da suke yin laftu na kudi suna kaiwa kasashen waje suna ajiyewa kamar 'yan Najeriya. Shakka babu irin yadda 'yan Najeriya suke daukar kudi niki niki abin sai wanda ya gani, ban sani ba ko gaskiya ne, ance akwai wani hamshakin attajiri a Najeriya sai da ya ciko kwantaina guda shake da daloli zuwa Najeriya daga Turai da Amerika, wannan bai bani mamaki ba, domin kuwa akwai wani yaro dan Najeriya da yaje wata jami'a a wata kasa yana neman admission suka bashi hakurin cewar sun rufe sai wata shekarar, amma da yaron nan ya tashi sai ya ce a nuna masa ofishin shugaban jami'a da yaje wajensa akwati ya dauko ya bashi cike da dalar Amerika yace masa ka dauki abinda kake so ka bani adimission, kaga kuwa duk abinda aka ce dan Najeriya zaiyi da kudi babu abin mamaki.
A irin wannan hali ne shugabanninmu suke yawo zuwa kasashen turai da Amerika karkashin tawaga mai tarin yawa da sunan neman masu zuba jari a Najeriya, kaji shugaban kasa ya kwashi mutane sama da dari (100) wai sun tafi neman 'yan kasuwar da zasu zo Najeriya don zuba jari, kudin otal din da za su kwana kwai ya isa arzikin wani kauyen a wata kasar, sai kayi mamaki shin su masu zuba jari mahaukata ne zasu kwaso kudinsu su zo su zuba a hudajjan aljihu, shugabanni a Najeriya sun kwashi dukiya sunkai kasashen Turai da Amerika saboda can yafi tsaro, amma kuma suna son wani ya kwaso dukiyarsa ya zuba a inda babu tsaro, alhali kuma duk kan kasashen da za'a nemo su zuba jari suna da ofishin jakadancinsu a Najeriya suna sanar da su irin halin da ake ciki a Najeriya na satar baki 'yan kasashen waje tare da yin garkuwa da su, idan da karar kwana akan kashe wasu daga cikinsu, shin su mahaukata ne kamar shugabanninmu zasu kwashi dukiya su zuba a cikin hudajjan aljihu?
Mafiya yawan jajayan fatar da suke kwaso kudi su zo Najeriya, idan ka bincika kodai suma barayi ne ko kuma kudin ainahi daga dukiyar 'yan Najeriya aka ranto a zo Najeriya a kara samun wata dukiyar ta banza, idan ka kalli badakalar kamfanin Halliburton zaka tabbatar da haka, galibin turawan da suke aiki a matatun man fetur suma barayi ne, ko kuma kaga bature dan tasha watakila a kasarsu shi ba komai bane, kawai ya kwaso sufanu da gajeran wandonsa yana budawa waishi injiniya yana karbar kudi a banza.
Shakka babu duk irin yadda zaka misalta barayi miyagu azzalumai to shuwagabannin Najeriya sun dara nan, har sai da ta kai tsohuwar shugabar EFCC take tuhumar hankalin shugabannin Najeriya saboda abinda ta gani ya shallake hankalin dan adam. Allah ya ce baya canzawa mutane sai mutane sun canzawa kansu kuma yana  baiwa mutane shugabanni dai dai dai da su, ba zai zama kuskure ba idan ka ce shugabannin Najeriya sunyi dai dai da 'yan Najeriya, domin dukkan irin waccan satar da muka ambata sai ka rasa waye mai gaskiya acikinmu, domin idan ka dauki kowa ka karkade shi sai kaga ashe shima wani karamin barawo ne dama ce kawai bai samu ba, duk wanda ya kalli badakalar cin hanci ta Farouk Lawan zai tabbatar da haka, domin mai dokar barci ne ya bige da gyangyadi, kuma Farouk ba shi kadai bane irinsa suna nan kamar jamfa a Jos.
Lallai 'yan Najeriya, idan muna son ganin gyara na hakika sai munji tsoron Allah mun gyara halayenmu tsakaninmu da ubangiji sannan mu sami abinda muke nema. Kullum muna kiran gyara da fatan samun shugabanni na gari masu adalci, amma akan kanmu bama yiwa juna adalci, ga zalinci tsakanin talakawa ya yi yawa ga gulma da munafurci da tsabar rashin tsoron Allah da karya da yaudara da ha'inci duk sunyi mana katutu, ga zinace zinace ga shan giya ga fyade ya karu, ga duk wani aikin badala ya karu, ga kuma uwa uba kisan kai na mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba, duk wannan abubuwan da suke faru sai mun gyara halayenmu sannan mu sami abin da muke nema na shugabanni adalai.
Suma a nasu bangaren shugabannin Najeriya su sani adalci shi ne zai zaunar da kasarnan lafiya, rashin adalcin da muke yiwa juna shi ne musabbabin dukkan irin halin da muke ciki, shugabanni basa jin dadi, talakawa basa jin dadi, to waye yake jin dadi a Najeriya? Lallai muna bukatar shugabannin suji tsoron Allah su yi adalci a tsakanin dukkan 'yan kasa, babu wanda ya fi karfin doka, don haka dukkan wanda ya karya doka a yi masa hukunci dai dai da abinda doka ta tanada.
Bahaushe ya ce abinda ya ci doma to fa bazai bar Awe ba, don haka misalin shugabannin da suka gabata darasi ne da dukkan wani mai hankali ya kamata ya kalla kuma yaji tsoron Allah ya gyara tsakaninsa da Allah, Masu Magana suka ce dukkan wanda yaki ji to bazai ki gani ba, gani ga wane . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment