Sunday, June 17, 2012

Muguwar Manufar Obasanjo na Kara Fitowa


Muguwar Manufar Obasanjo Na Kara Fitowa
Batun zargin karbar cin-hanci da aka yiwa Hon. Farouk Lawal (PDP Kano) shi ya mamaye galibin kafafen yada labarai na Najeriya a makon da yagabata. Wannan batu na karbar na goro da Farouk ya yi a hannun hamshakin attajirin nan Mista Femi Otedola, kusan ya zubar da kimar Hon. Farouk Lawal warwas a idon duniya, kamar yadda kowa ya sani ne wannan batu ya biyo bayan rahoton kwamitin da shi Hon. Farouk ya jagoranta, wanda suka fallasa manyan mutane da suke ci-da gumin talakawa, rahoton yace kusan Naira Tiriliyar daya akayi almundahana da su a cikin shekara daya da sunan tallafin manfetur, a karkashin wannan gwamnati ta Goodlucl Jonathan, inda rahotan ya zargi muhimman mutane da suka hada da babban kamfanin mai na kasa NNPC da minister kula da albarkatun mai Madam Dazieni Allasan Maduwake da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa zamanin Obasanjo Amadu Ali da kuma wasu kamfanoni da suka hada harda kamfanin mista Femi Otedola na Zenon Petroleum.
Tun bayan da wannan rahoto ya fito 'yan Najeriya ciki da waje sukayi ta tofa albarkacin bakinsu domin ganin anhukunta ko daukar mataki akan mutanan da rahoton kwamitin Farouk ya kama da laifin cin amanar kasa. Hausawa sunce kayi hankali da kama barawo, domin idan baka iya ka kamashi ba to tabbas zai ruftaka shi kuma ya kama gabansa, kusan wannan shi ne abin da ya faru da Hon. Farouk Lawal, inda aka shiraya masa gadar zare kuma ya hau kanta dodar, dole muga laifinsa domin me ya kaishi gidan Otedola har ya karbi wannan kudi da kansa, duk da rahotannin sun nuna cewa Farouk ya sanar da rundunar 'yan sanda ta kasa akan cewa Otedola yana kokarin bashi hanci, tun bayan fallasar wannan abin kunya ne, majalisar kasa ta yi wani zama na gaggawa domin tattauna batun da ya shafi daya daga cikin manyan shugabanninta, kuma matakin da majalisar ta dauka ya yi dai-dai.
Duk wannan abin da yake faruwa, ko ya faru, ya kara nuna yadda muguwar manufar Obasanjo ta ke kara fitowa fili. Kamar yadda muka sani Hon. Farouk kusan a wuyan Obasanjo yake, domin, shi ne ya jagoranci wata kungiya a majalisa da ake kira Integrity Group wadan da sukayi silar fatattakar kakakin majalisar ta wancan lokaci Patricia Ette, wadda ake mata kallon babbar diyar gaban goshin Obasanjo, bayan samun nasarar tunkude Ette da su Farouk suka yi, sun sake cin nasarar shigo da babban dan adawar Obasanjo da ita Etten a matsayin kakakin majalisar dokokin tarayyar Najeriya, Rt. Hon. Oladimeji Sabur Lawal Bankole wanda ya ci nasarar zama shugaban majalisa da gagarumin goyon bayan 'yan Integrity Group, Farouk Lawal ya zamewa Obasanjo wani karfen kafa, wannan ta sanya Obasanjon yake a kufule da Farouk Lawal da kuma Dimeji Bankole.
Obasanjo da mukarrabansa sunyi dukkan me yi wuwa wajen ganin sun kwashewa Bankole kafafu a zaben 2011. Cikin nasara wannan hakar tasu ta cimma ruwa, Bankole ya sha kasa a hannun ACN, wannan ta sanya aka ringa yiwa Bankole bita da kulli, inda alamu ke nuna cewa da hannun Obasanjo aka yi kokarin shiryawa Bankolen gadar zaren da ya tsallake ta da kyar bayan ya shafe kwanaki a komar 'yan sanda, an zargi Bankole da sama da fadi da kudaden majalisa da suka kai kusan Biliyan 4, kafin daga baya kotu ta wanke shi, shi da mataimakinsa Hon. Bayero Usman Nafada.
Tun bayan da Obasanjo da mukarrabansa da Jam'iyyar PDP suka ci nasarar shatale Bankole, suka shirya tsam domin ganin Hon. Mulikat Adeola da ke zaman 'yar majalisa daya tilo ta jam'iyyar PDP daga shiyyar yamma ta maye gurbin Bankole a matsayin kakakin majalisar kasarnan, nan ma dai su Obasanjo da jam'iyyar PDP basu ji da dadi ba, domin su Farouk Lawal sun takawa abin birki duk kuwa da irin barazanar da akayi musu, inda suka yi nasarar shigo da Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal a matsayin kakakin majalisa ta bakwai, a wannan majalisa ta kasa, wannan ya sake dagulawa su cif Obasanjo lissafi domin duk wani yunkuri da sukayi sai su tarar Farouk da jama'arsa sun tare hanya babu kuma yadda suka iya.
Tun bayan da aka gama waccan sabatta juyatta ta waye zai zama kakakin majalisar kasa ta kare, majalisa ta shiga aiki ka'in da na'in; suma a nasu bangaren Obasanjo da PDP suka shiga nasu aikin ka'in da na'in domin ganin yadda zasu sanya zabari su kamo Hon. Farouk Lawal a cikin komarsu, cikin ikon Allah wannan haka tasu ta cimma ruwa domin Farouk ya yi kasadar fadawa cikin wannan tarko da aka shirya masa, inda bayanai suka tabbatar da cewa ya karbi dalar amerika dubu 620 a hannun Femi Otedola a gidansa da ke Abuja, shi dai Otedola shi ne ya nuna wannan faifan bidiyo da aka ga farouk yana karbar wannan kudi, kuma rahotannin sunce Obasanjo ya yi ta yamadidi da Hon. Farouk da wannan bidiyo inda ya ringa zuwa da kansa yana nunawa muhimman mutane wannan bidiyo.
Hausawa suka ce, ko wane allazi da nasa amanun. Kamar yadda kusan yake a siyasar Najriya, domin idan bamu manta ba, allazin marigayi Umaru 'YarAdua,shi ne Mista James Ibori, wanda ya fada komar jam'an tsaro a landan bisa zarginsa da lartar kudadan haram, wanda yanzu haka yake can yake zaman sarka na kusan shekaru 16 a birtaniya. Haka shima wannan shugaban na yanzu Goodluck Jonathan Femi Otedola, shi ne nasa allazin domin kuwa kafatanin jam'iyyar PDP babu wanda ya taimakawa da GEJ da kudaden da Otedola ya taimaka, wannan ta sanya ya kara samun babbar dama ta cin karensa babu babbaka a wannan gwamnatin, shi dai wannan mutum Otedola idan bamu manta ba yana daga cikin 'yan gaban goshin Obasanjo a lokacin da yake shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, domin cikin kankanin lokaci Obasanjo ya mayar da Otedola mai arzikin gaske, domin bayanai sunce idan har za'ayi kidayar masu arziki a wannan lokacin to tabbas Otedola yana daga cikinsu, domin yana daga cikin tsiraru da aka baiwa dammar safarar manfetur da dangoginsa zuwa ciki da wajen Najeriya, wannan ta bashi dama ya kudance cikin dare daya.
Kamar yadda kowa ya sani duk wani mai kishin kasa ba zai goyi bayan cin-hanci da rashawa ba. Don haka, duk wannan abin da ya faru da Farouk Lawal muna da yakinin makarkashiya ce daga su Obasanjo da kuma wadan da rahoton kwamitin Farouk ya shafa, don haka, tabbas Farouk ya nuna kulafuci da son abin duniya inda ya jefa kansa cikin wannan bakin tarihi, lallai akwai bukatar a gudanar da bincike na gaskiya akan wannan batu, kuma muna fatan a hukunta Farouk Lawal daidai da laifin da ya aikata, domin zama darasi ga 'yan baya.
Idan ambit a barawo to abi ta mabi sawu. Kamar yadda Otedola ya bayyanawa 'yan jarida cewar ya baiwa Farouk Lawal cin hanci, har yace yana da faifan bidiyo da yake tabbatar da ikirarin nasa, shakka babu, kamar yadda dokar kasa ta ce, da wanda ya bayar da cin-hanci da wanda ya karba dukkansu masu laifi ne, muna nan mun zuba ido muga yadda za'a cukumo wuyan Otedola a gurfanar da shi gaban shari'a, domin ya tabbatarwa da duniya cewar ya bayar da hanci wanda kuma laifi ne, duk da cewa ya zuwa yanzu rahotannin sun nuna cewa Femi Otedola zakara ya bashi sa'a domin ya fice yabar kasarnan zuwa birtaniya, lallai muna bukatar a taso keyarsa domin yazo ya fuskanci shari'a akan wannan batu na cin hanci.
Duk da wannan abin da ya faru, bazamu manta da irin alkhaira ko kokarin da Hon. Farouk Lawal ya yi ba, ya kawo sauye-sauye masu yawa musamman a lokacin da ya rike da mukamin shugaban kwamitin kudi na majalisa da kuma shugaban kwamitin ilimi, muna fatan wannan abun da ya faru da shi zai zame masa babban darasi a rayuwa dama sauran 'yan Najeriya baki daya. Sannan zamu ci gaba da kallon Obasanjo a matsayin babbar baraza ga wannan kasar, Allah ya kyauta.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment