Wednesday, July 8, 2015

Muna Cikin Gagarumar Matsala


 MUNA CIKIN GAGARUMAR MATSALA 

Yana daga cikin dalilin aukawarmu cikin wannan mugun hali na tashin hankali da zaman dar-dar, da rashin kwanciyar hankali, shi ne wata gurbatacciyar fatawa da aka yada a tsakanin al'umma cewar karatun Boko da aikin Gwamnati da dangoginsa duk Haramun ne. Hakan ta sanya masu irin waccan fatawa a yanzu suka rikide suka koma KHAWARIJAWA suna ganin kowa bai fahimci addini ba sai su, kuma kowa akan bata yake sai sune kadai akan daidai.

Hakan na faruwa ne  irin yadda wasu kawai dan sun karanta addini basu fahimci komai a cikin abubuwan da suka shafi hukunce-hukuncensa ba (addini ba), kawai sai su fara yiwa al'muma fatawa babu gaira babu dalili. Domin haka siddan Yusuf ya zo cikin tsukakken tunaninsa da gajeren iliminsa, ya dauka cewar shima ya kai wani munzali da zai dinga tara al'mma yana yi musu fatawa. Aka wayi gari suna Halatta Haram suna kuma Haramta Halal. 

Irin hakan ce ta janyo, rana tsaka aka wayi gari suna baiwa mabiyansu fatawar cewar karatun Boko kafurci ne, har hakan ya kaimu ga wannan mawuywcin lokaci da ake cewa Boko Haram. Aka dinga yiwa bayin Allah fatawa cikin jahilci da daskararren tunani da rarraunan hange, aka dinga sanya wasu suka dinga yaga takardunsu, sabida ance musu bai halarta ba a Musulunce.

Wannan kamar wani 'yanci ne, da kusan duk wanda yake jin ya karanta ilimin addini, kawai zai dinga yin FATAWA akan dukkan abinda yaga dama ko duk tambayar da akai masa, ba tare da tunanin matsalar da wannan Fatawa tasa zata janyo ba. Malamai sun sha gaya mana, cewar magabata har gudu suke ana binsu ana rokonsu Allah akan su zo su yiwa al'umma Fatawa.

Amma yanzu muna cikin wani zamani da kowa yana jin cewar shi Malami ne, ya karanta addini yasan addini. Malaman da suka karantar da shi gani yake sunyi kafada da juna, dan haka muka wayi  gari kowa me fatawa ne, kuma kowa me Tafsiri ne musamman a wannan wata na Ramadan.  Da yawa suna nan suna baiwa al'umma fatawa cikin jahilci da rashin sani, wannan ta sanya sai kai ta ganin mutane na yin kwan-gaba kwan-baya, yau mutum yayi Fatawa gobe ya warware ta, ko kuma jibi yace ai fahimtarsa ne ba'ayi ba.

Shi Musulunci addini ne mai tsari ba addini ne da kowa zai kutsa kai cikin komai yana ganin kansa shi wani Mutafannini  ne a cikinsa ba. Lallai yana da kyau mutane su ji tsoron Allah, su dena sanya al'umma cikin halaka ta hanyar yi musu gurbatacciyar fatawa wadda babu abinda yake cikinta sai tsabagen yarinta da shirme da kuma san nuna isa.

Allah ya jikan Malam Jaafar Adam Kano da Malam Abubakar Hussaini Fagge, Allah ya gafarta musu. An sha yiwa Malam Jafar tambaya, amma sai ya bugawa Malam Abubakar Hussein Fagge waya yaji abinda zai ce, duk kuwa da Allah ya baiwa Malam Jaafar daukaka da shahara, sama da ta Malam Abubakar Hussain, amma sabida kiyaye amana ta Ilimi, Malamai suke yin kokarin maida komai zuwa ga asalin sa,  dan kare al'umma daga fadawa muguwar fatawa.

Haka nan,  Sheikh Albans Zaria Allah ya jikan sa, na taba ji yana fada cewar, abin yana bashi mamaki mutum yana Kano ko Katsina ya buga masa waya yana tambayarsa Fatawa, yakan gayawa masu irin wannan, cewar shin a garin ku babu Malaman Sunnah da zasu iya yin wannan fatawa sai ni ko kuwa jin baki ne. To haka ne, Malamai na Allah suke kiyaye amana ta Ilimi. 

Dan haka  yana da kyau mutane su kiyaye kansu daga fadawa hannun fatawar irin wadannan da suka dora al'umma kan karkatacciyar fatawar cewar karatun Boko da dangoginsa b'ata ne kuma kafurci ne. Lallai yana daga cikin ayyukan da ya kamata Manyan Malamai su maida hankali akai na dakile yaduwar irin wannan fatawoyi barkatai da wasu dalibai masu feleke da iya yi suke yi. Ya Allah ka nuna mana gaskiya, mu fahimci gaskiya ce ka bamu ikon binta; ka nuna mana karya mu fahimci karya ce ka bamu ikon kauce mata. 

Yasir Ramadan Gwale 
08-07-2015

No comments:

Post a Comment