Saturday, July 4, 2015

Fahimtar Matsalar Boko Haram


BOKO HARAM: Da yawan mutane an gurbata tunaninsu an yi Nasarar amfani da farfaganda ta karya akan Boko Haram akansu, mutane sun dimauce sun gaza gane hakikanin lamura sai bagauniya suke sun kasa gane me ke faruwa. Wasu da dama tunaninsu yana basu cewar idan an jingina aikin ta'addanci zuwa ga 'yan ta'adda da suke yi sa,  sai tsukakken tunaninsu ya basu cewar ai duk kokari ne na tsarkaka Goodluck Jonathan​, amma duk zargi da farfagandar masu farfaganda ba zai sanya karya ta zama gaskiya ba. 

Ka kan fahimci jahilci mutane karara a lokacin da suke nesanta Musulmi daga aikata ta'addanci irin na Boko Haram, wasu a zatonsu babu yadda za ai Musulmi ya iya kashe Musulmi, da yake basu san tarihi ba, kuma basu san su waye Khawarij ba a cikin Musulunci, sannan sun manta su waye suka kashe Sayyaduna Usman Bin Affan. 

Ko dai mu yadda mu aminta cewar wadan da suke wannan ta'addanci Musulmi ne 'yan uwanmu da suka kauce hanya da gangan ko da ganganci,  ko kuma mu cigaba da zargin wasu daga can nesa muna ji muna gani al'umma daruruwa suna rasa rayukan su a lokaci guda, zargin da muke babu abin da zai haifar sai bakinciki da takaici.

Muna yiwa Gwamnati da sojojin mu addu'ar fatan alheri da fatan samun nasara akan wannan Yaki da suke da wadannan miyagun Azzaluman 'yan ta'adda marasa tsoron Allah.

Yasir Ramadan Gwale 
04-07-2015

No comments:

Post a Comment