Sunday, December 21, 2014

Siyasar 2015 An Kai Arewa An Baro


SIYASAR 2015 AN KAI AREWA AN BARO

Shi fa yaki irin na siyasa dan zamba ne, dole ayi shirin tunkararsa indai da gaske yakin za'a yi. Dole kayi nazarin kanka a karon farko, kasan waye kai me zaka iya, meye karfinka, meye rauninka, meye manufarka, me kake san cimmawa; sannan kuma, sai ka nazarci abokin fito na fito, meye karfinsa, meye yake nema da zai iya cin lagonka da shi, wanda daman kai tuni ka gama sanin wadan can hanyoyi ka gama nazartarsu, dan haka ko da abokin fito na fito ya taso maka kana da dukkan dabaru da kai tanadi na kare kanka daga duk wani yunkuri irin nasa. Dole kuwa kai haka, domin kaine ka taro yakin ba shi ne yazo ya sameka ba, dan haka ne aka Ruwaito Manzo SAW idan zai fita Yaki yakan nufi Gabas alhali kuma inda zai tunkara a yamma yake, wannan dabara ce ta yakin da ake neman cin nasara da gaske.

Manyan 'yan Siyasa daga Arewa tun lokacin da aka fara fuskantar 2015 sukai ta batun dole sai mulkin Najeriya ya koma Arewa. Alhali babu wani shiri da akayi dan hakan, wace Manufa Arewa take da ita gamammiya idan Mulkin ya dawo Arewa? duk da dai kawai yaudara ce kawai ake yi da sunan Arewa, kuma galibi Talakawa sune ke bata lokacinsu da sunan Arewa, dan nasan babu wani dan siyasa da zai ce yana yin siyasar Neman Mulki kuma yace da sunan Arewa yake yi. Shi yasa galibin masu kiran Arewa, kodai 'yan Siyasar da ba neman Mulki suke ba, kawai basa san a manta da su ne shi yasa suke kiran Arewa, ko kuma wasu mutane ne da ba zasu iya sanyawa ako hana komai ba. Daman kuma Talaka maganarsa bata cika tasiri ba a wajen masu mulki.

Shin masu fatan mulki ya dawo Arewa wane tanadi suka yiwa hakan? Idan Mulki ko Shugabancin Najeriya ya dawo Arewa me suke san cimmawa, ko kuwa kawai muna san Mulki a suna ace wane dan Arewa shi ne Shugaban kasa alhali kuma babu wani abu da zai iya kullawa! Na farko dai tun ran gini tun ran zane, wadan da suka ginamu akan kabilanci sunyi kuskure. Shi yasa aka wayi gari babu wani da yake batun Najeriya a siyasance, dan kudu fatansa dan kudu ko da kuwa babu wani abu da za'a tsinanawa mazabarsa, haka shima dan Arewa, ai bincike ya nuna cewa da dama daga cikin mutanan kudu maso kudu suna cikin mawuyacin halin rashin aikin yi da rashin karatu, duk kuwa da cewa sitiyarin da ke jan Najeriya dan garinsu ke tukashi.

A ganina da wahala Mulkin Najeriya ya iya dawowa Arewa a hannun jam'iyyar hamayya, idan maganata gaskiya ce, to Gwamnonin nan guda biyar ko bakwai da suka tada kayar baya a PDP kuma daga karshe suka fice suka koma APC sune suka kai Arewa suka baro! Wannan dai ra'ayi da tunani na ne, kuma gwargwadan abinda na gani na fahimta. Sai nake ganin kamar muna da saurin mantuwa, mun rudu da yawanmu alhali kuwa a Najeriya ba'a zaben gaskiya a matakin Shugaban kasa! Batun Arewa da Yarabawa kuwa aganina wani abu ne adukunkune mai rikitarwa, dan kuwa mai yasa ba'a dauko Kayode Fayemi da ya fadi zaben Gwamnan Ekiti an bashi mataimakin Buhari ba? Duba da cewa sananne ne kuma anga kamun ludayinsa, amma aka dauko tsohon kwamashina alhali ga Gwamna da yake da dukkan kwarewa ta Mulki! Wannan fa wata katuwar ayar tambaya ce, amma duk aka ja baki akai gum... Zan cigaba In sha Allah.

Yasir Ramadan Gwale
21-12-2014

No comments:

Post a Comment