Monday, December 1, 2014

MAganar Gaskiya Dangane Da Kahse-Kashen 'Yan Boko Haram


MAGANAR GASKIYA

Rabin gaskiya ba gaskiya bane. Ba zaiyuwu ba ace akwai magana rabi gaskiya rabi karya. Kodai ta zama gaskiya zalla ko karya zalla. Dole mu tunawa kanmu tarihi dan fuskantar gaskiyar al'amari.

Wadan da suka kashe sahabin Manzon Allah kuma surikinsa, Usman Ibn Affan Alaihis-Salam, Musulmi ne masu fatan samun shiga al-jannah, sun kashe shi yana karanta al-Qurani zancen Allah. Haka zalika, wadan da suka kashe Malam Jaafar Adam Rahimahullah ranar juma'ah yana limancin Sallar Asuba, Sallar da munafukai basa halatta inji Manzon Allah. Nayi imani wadan da suka kashe Malam Jaafar musulmi ne ba arna ba.

Dan haka babu wani dalili da wani zai fito yace mana WAI MUSULMI BA ZASU IYA KASHE MUSULMI A MASALLACI BA wannan ba gaskiya bane. Ya faru a baya kuma yana cigaba da faruwa a yanzu. 

Wadan da suke wannan kisan da ake kira Boko Haram dole mu yarda cewa su Musulmi ne, amma kasancewarsu Musulmi ba shi ke nuna halaccin abinda suka aikatawa ba, kuma aikinsu ba shi ke nuna haka duk Musulmi suke ba. Akwai Musulmin kirki na gari masu tsoron Allah; kuma akwai Musulmin banza gurbatattu marasa tsoran Allah.

Ba yadda zaka kore Musulmi daga Musulunci duk munin aikinsa indai ba shi ya kore kansa daga Musulunci ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yayi alqunutu yana kama sunan wasu Allah ya haneshi, ya gaya masa Subhanahu Wata'ala cewa shiriya a hannunsa take buwayi gagara misali.

Bambancin addini ko bambancin siyasa ba shi zai halatta mana kiyayya da gaba ba. Na gamsu cewa Shugaban kasa baya yin abinda ya kamata ace yayi a harkokin tsaro. Amma kai tsaye a ce shi ne ke kashe mutane wannan ba gaskiya bane.

Dole mu gayawa kanmu gaskiya. Shin tsakani da Allah akwai wani Musulmi ko dan Boko Haram ko ba shi ba da zai yarda ya daura Bom a jikinsa Bom ya tashi da shi dan bukatar Goodluck Jonathan ta biya? Shin arna irin na Najeriya zasu saka Bom a jikinsu su mutu dan bukatar Jonathan ta biya? Akwai wani mai hankali daga cikin Musulmi ko kirista da za ayi yarjejeniya da shi dan shi din ya mutu?

Ya kamata mu fadi gaskiya kuma mu yi adalci a maganganunmu. Idan har zamu dinga baiwa Boko Haram uzuri muna cewa basu bane wasu ne daban. To wallahi wannan abin ba zai taba yin sauki ba sai dai ya karu. Mun shagaltar da kawukanmu da zargin juna su kuma zasu mamaye garuruwanmu. Wanda ya sani ya sani wanda bai sani ba ya sani.

Indai ana san kawo karshen wannan kashe kashe dole abi hanyoyi na gaskiya dan magance matsalar. Amma ba zai yuwu ba a dinga siyasa da rayuwar al'umma. Ko mun yarda ko bamu yarda ba Khawarijawa sun sanyamu yakin da bamu shirya ba. Sarakuna ya kamata suyi abinda ya dace cikin hikima.

Adduah kadai ba zata magance mana wannan halin da muke ciki ba. A cikinmu babu Annabi Musa ko Abu Huraira. Manzon Allah SAW ba adduah kadai yayi ya kwanta Mala'iku sukai masa Badar ba.
Kayi tir ko kai Allah wadai wannan ba zai taba sauya gaskiya ba. Tana nan a matsayinta na gaskiya, haka nan ba zai taba sanya karya ta zama gaskiya ba.

Lallai jagororinmu subi hanyoyin da suka kamata wajen kare salwantar rayukan al'ummah da suke mutuwa ba gaira ba dalili. Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimci gaskiya ce ka bamu ikon binta ka nuna mana karya mu fahimci karya ce ka bamu ikon kauce mata.

Yasir Ramadan Gwale
30-11-2014

No comments:

Post a Comment