Sunday, December 14, 2014

Kwangwaratuleshans Janar Muhammadu Buhari


KWANGWARATULESHANS JANAR BUHARI

Assalamu Alaikum Warahmatullah. Sunana YASIR RAMADAN GWALE, ina mai yin amfani da wannan dama wajen taya Janar Muhammadu Buhari murnar lashe zaben fidda gwani a karon farko da aka kasa a faifai Janar yayi takara kuma ya lashe zabe. Ba shakka na san Zainab na cike da murnar samun wannan Nasara, ina kara tayata murnar samun wannan Nasara da GMB yayi.

Ina fatan Janar Buhari a matsayinsa na jagora zai rungumi kowa da kowa dan tafiya tare. Nasarar Buhari nasara ce ga Dimokaradiyya, a koda yaushe dimokaradiyya na alfahari da irin wannan damar da ake baiwa al'ummah dan bayyana ra'ayinsu na tsayawa zabe. Haka nan kuma ina taya Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso murnar zamowa na biyu a wannan zabe, ba shakka Kwankwaso yayi kokari ya nuna iya siyasarsa, da yawa na ganin Atiku Abubakar ne zai zo matsayi na biyu, amma kwankwaso ya shammaci mutane. Ina kuma taya Atiku Abubakar din alhinin samun wannan matsayi na uku, na tabbatar ba haka ya so ba amma hukuncin Allah shi ne abin karba, kuma ya burgeni matuka da ya nuna jarumtaka ya karbi faduwa! Wannan ita ce kaiwa makura a dimokaradiyya duk da ba laifi bane neman hakki idan har wani yana ganin anyi masa ba daidai ba.

A daya gefen kuma ina taya tsohon mawallafin jaridar Leadership Newspapers Pharm. Sam Nda-Isiah murnar samun kuri'u guda goma ba shakka, na aminta da irin kishin kasa da kaunar Najeriya da Sam yake da shi, ina masa fatan Allah ya bashi wata dama da zai hidimtawa al'ummar Najeriya.

Haka kuma, Janar Buhari zai kuma fuskantar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan dan yi wannan karon battar a karo na biyu. Tun a zaben da ya gabata na 2011 da yawan 'yan Najeriya masu bibiyar harkokin siyasa sun san lagwan kowa tsakanin Buhari da Jonathan. Fatana shi ne Allah ya saukaka mana al'amuranmu ya zabar mana shugabanni na gari adalai a dukkan matakai na shugabanci. Kuma in sha Allah zan taimaka da Naira 10,000 ga kwamatin yakin neman zaben Janar Buhari na BSO.

Ina taya murna ga 'yan uwanmu abokanmu 'yan Buhariyya musamman wadan da suka tayamu murnar samun Nasarar Malam Nuhu Ribadu da Malam Salihu Salihu Sagir Takai dama wadan da basu tayamu murna ba, da kuma masu yi mana mummunan fata, har da masu yi mana tadiya da mugun baki irinsu Mansur Manu Soro duk muna musu murnakuma muna yi musu adduar fatan alheri. Allah ya taimaki kasarmu Najeriya ya bamu nasara, ya amintar da mu ya bamu lafiya da zaman lafiya.

Cc: Ibrahim Sanyi-Sanyi, Muhammad Aliyu Dutsin-Ma, Kwamared Baban Shareek Gumel, Affan Buba Abuya, Sagir Musbahu Daura Dole, Hussein Abdussalam, Attahiru Muhammad Marnona, Abubakar Aminu Ibrahim, Bashir Ahmad, Sunusi ShehuSunusi Musa, Auwalu Lawan Aranposu, Hamza Ibrahim Baba, Abdulrashid Ahmad, Baba Bala Katsina, Ibrahim D Itsenyabi, Khaleel Nasir Kiru, Lawal Muazu Bauchi, Yamai Muhammad, Hk Yaradua, Husain Husain Kyar'adua, Uba Danzainab.

Bcc:....

Yasir Ramadan Gwale
14-12-2014

No comments:

Post a Comment