Tuesday, December 2, 2014

HATTARA GWAMNATIN KANO: Jihar Kano Bata Karkashin Dokar Ta'baci


HATTARA GWAMNATIN KANO: Jihar Kano Bata Karkashin Dokar Ta'baci

Ranar juma'ar makon da ya gabata 28 ga watan Nuwamba, rana ce da al'umma da yawa a cikin Birnin Kano ba zasu taba mantawa da ita ba. Wannan ita ce ranar da aka kai hari mafi muni a tarihin hare-haren da 'yan ta'adda makiya Allah makiya san zaman lafiya suke kawowa Kano. An kashe dattawa da matasa da yara a lokacin da suke Ibada dan yin munajati tare da ubangijinsu. Ba shakka wannan al'amari muninsa yakai muni. Ina kara yin adduah ga wadan da suka rasa rayukansu a wannan rana, Allah ya jikansu ya gafarta musu ya sa al-jannah ce makomarsu. Masu raunuka kuma Allah ya basu lafiya, ya sa ciwon ya zama kaffara a garesu.

Lokacin da wannan al'amari ya auku, Mai girma Gwamnan jihar Kano wanda shi ne Shugaban Tsaro na jihar Kano (Chief Security) baya Kano yana can kuryar kudancin Najeriya, shima Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Muhammadu Sunusi II shima baya kasar baki daya, haka zalika Kwamashinan 'yan Sanda  na jihar Kano shima baya Kano! Cikin kaddarawar Allah wannan mummunan kaba'ira ya faru.

Faruwar wannan mummanan harin ta'addanci da awa hudu misalin karfe 06:04 Uba Danzainab ya sanar mana a facebook bikin da ake a ofishin mataimakin Gwamna na cike form din takararsa ta zama Gwamna Kano! A irin wannan lokaci da al'umma ta shiga cikin damuwa da rudani, akai wawar asarar rayukan al'umma, masu mulkin da ya kamata ace sunfi kowa nuna  damuwa da rayukan al'ummarsu sama da komai, amma a kyale al'umma a shiga al'amuran siyasa? Yanzu wannan daidai ne?

Haka nan shima Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewar baya Kano lokacin da abin ya faru, sai washegari Asabar da safe sannan muka ji cewar Gwamna yaje Masallacin kofar Gidan Sarki da Asibitin Murtala dan jajantawa wadan da abin ya shafa tare da ganin irin girman barnar a Masallacin Gidan Sarki, amma bamu ji cewa ya halarci jana'izar wadan da aka binne a makabartar Dan Dolo a safiyar asabar din ba.

A wannan ranar ne kuma tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bada sanarwar soke bikin da wasu abokansa suka shirya masa na murnar samun karin shekara da yayi (BirthDay), ya bada sanarwar cewar ya soke bikin ne domin jimami tare da taya al'ummar Kano alhinin abinda ya faru. Ba shakka ko domin siyasa Atiku yayi hakan ya kyauta, domin ya nuna cewa jinin al'ummah yana da kima da daraja a wajensa.

Haka kuma, wani abin mamaki da ya kuma faruwa a lahadin da ta biyo bayan asabar din, sai muka samu sanarwa a facebook daga Baba Dantiye cewar Gwamna Kano yaje bikin auren wasu Yarabawa a jihar Legas! Yaushe za a ce Gwamna wanda shi ne yafi kamata yafi kowa nuna damuwa akan rayukan al'ummar jihar Kano, amma ace har ya fice ya tafi yawan bukukuwa? Shin hakan na nufin tsohon mataimakin shugaban kasa yafi Gwamnan Kano mutunta rayukan al'ummar Kano?

Shin yanzu idan mun zargi Gwamnatin tarayya akan rashin nuna damuwa da rayukan al'umma, su kuma Shugabanninmu na jihohi mu ce musu me? Tsakanin Gwamnatin tarayya da Gwamnatin Kano wa yafi kamata ya fi nuna damuwa da raukan al'ummar jihar Kano?

Lallai ya kamata mu sani cewar Jihar Kano fa bata karkashin dokar ta baci, dan haka Gwamnan Kano shi ne shugaban tsaro Chief Security na jihar Kano, shi ne wanda yake da ruwa da tsaki akan duk abinda ya shafi tsaro a cikin kano musamman cikin birni. A irin wannan halin da aka samu kai aciki, Gwamna baya gari, Sarki baya gari, Kwamashinan 'yan sanda baya gari, shi kuma Magaimakin Gwamna yana can yana bikin ciken form din tsayawa takara. To dan Allah waye ya damu da rayuwar al'ummar da ake shugabanta?

Ina mai amfani da wannan damar wajen yin kira ga Gwamnatin Kano da Mai Girma Gwamnan Kano Engr Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Mataimakin Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, akan su fito su nemi afuwar al'ummar Kano akan wannan rashin ko in kula da aka yi a daidai lokacin da Kano ta fada cikin bala'i. Rashin yin hakan shi ne zai tabbatar mana da cewar masu mulkin ba gaskiya suke ba akan kula da rayuwar al'umma, sunfi damuwa da sha'anin mulkinsu da siyasarsu sama da rayuwar al'ummar da suke shugabanta.

Ina sake amfani da wannan damar wajen kara yiwa al'umma ta'aziyar wannan ibtila'i da ya samemu Allah ya jikan wadan da suka rasu a sanadiyar wannan hari. Marasa lafiyan cikinsu Allah ya basu lafiya ya sa hakan ya zama kaffara a garesu. Masu kai wadannan hare-hare Allah ka sansu kana ganin Allah kai musu abinda yafi dacewa da su. Allah ka amintar da mu a garuruwanmu.

Yasir Ramadan Gwale
02-12-2012

No comments:

Post a Comment