Saturday, October 18, 2014

Kudin Form Din Takarar Janar Muhammadu Buhari


KUDIN FORM DIN TAKARAR BUHARI

Naji cewar Buhari ya sayi takardun cikewa shiga zabe akan kudi wajen Miliyan 27.5! Hakika wannan kudin yayi yawa sosai. Hakan kuma na kara nunawa al'umma cewa al'amarin Mulki ko Shugabanci a Najeriya ba na Talaka ba ne. Duk kokarin da ake yi shi ne na tsame hannun talakawa daga sha'anin Mulki.

Yanzu idan a Apc nake kuma zanyi takarar Shugaban kasa sai na biya wadannan Miliyoyi bayan kudin da zan batar na harkar yakin neman zabe? Apc ce fa ake ganin jam'iyyar Talakawa da ta zo dan sharewa talaka hawaye! Wannan karara lasisi ne ake baiwa zababbu su yi sata san ransu. 

Na zata kudin Form a Apc ba zai wuce 'yan dubunnai ba dan kusanto da abin ga talakawa, amma dai zatona ba gaskiya ba ne. Kuma ni abinda ya fara zuwa raina shin yanzu idan Buhari bai samu nasara ba shi kenan yayi asarar wadan can miliyoyi? Dan naji ance bashin Banki ya ciyo dan sayan takardun.

Wannan ta sanya na tuna kwanaki da naji wasu na ikirarin zasu sayawa Buhari takardun shiga zaben, shin kudin ne yayi musu tsada ko kuwa! Allah masani. Shin idan Buhari bai ci zabe ba magoya bayansa zasu taimaka masa biyan wannan bashin?

Bana yiwa Buhari mummunan fata. Adduah ta ita ce duk wanda zai fi zama alheri a garemu a wannan zabe Allah ka bashi.

Yasir Ramadan Gwale
17-10-2014

1 comment:

  1. Hmmmm Malam Yasir kenan, wannan gaskiya taka tana kama da son rai, tun da dai General Buhari ba dan PDP bane shi kenan.

    ReplyDelete