Monday, October 20, 2014

Cire Hula A Coci


CIRE HULA A COCI: Kwanakin baya da naga manyan 'yan Siyasarmu su Gen. Buhari da Atiku Abubakar da Gwamna Kwankwaso a coci sun ciccire huluna a gaban pasto abin ya bani mamaki matuka, kuma ya sanya min tambayoyi a raina dangane da wannan al'amari. 

Yanzu saboda Allah ace arne kamar mai Malafa ya sanya mutane masu kima da daraja shiga coci suna cire hula dan kawai neman Mulki ba dan yin kira zuwa ga addini ba! Shin yanzu idan su basu iya yadda zasu jawo shi Masallaci ba har sa bari shi ya yi silar shigarsu coci su cire hula duniya na gani?

Watakila wani yace ai ba kafurci bane dan sun shiga coci. Nima bance hakan ba, amma dai saninmu ne cewar sun shiga ne ba dan yin kira zuwa ga addinin Allah ba. Sun je ne dan siyasa, watakila da shi Gwamna Okorocha ba a APC yake ba da ba wanda zaka gani a cikinsu.

A kwanakin baya da Gen. Buhari da Gwamna Kwankwaso da Atiku Abubakar duk sun aurar da 'ya 'yansu amma babu wani arne da aka gayyato yazo cikin Masallaci akai daurin auren da shi, kuma Okorocha na nan duk sauran arnan duk suna nan, amma sai mu 'yan ina da biki zamu dinga binsu coci muna tafawa muna dariya, ai idan ni banyi silar zuwanka Masallaci ba a dalilin kawancen siyasa to ba yadda zakai silar zuwana coci na cire hula tunda ba wa'azi na je ba.
Na kuma ga yadda akai ta kokarin bayar da kariya da bada uzuri ga wadan da suka shiga kanisar, amma tambayar da taita yawo a raina ita ce:

Yanzu tsakani da Allah idan Malam Ibrahim Shekarau ne ya shiga coci ya cire hula a gaban pasto shin za'a bashi uzuri kamar yadda aka baiwa su Buhari da Kwankwaso da Atiku?

Idan har Uzuri ne mutum ya shiga coci ya cire hula a gaban pasto dan siyasa, to ba shakka uzuri ne babba mutum ya shiga PDP dan yin siyasa. Allah ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta.

Yasir Ramadan Gwale
19-10-2014

No comments:

Post a Comment