Thursday, September 5, 2013

RIKICIN PDP: Bamu Ci Nanin Ba, Nanin Ba Zata Ci Mu Ba!!!


RIKICIN PDP: Bamu Ci Nanin Ba, Nanin Ba Zata Ci Mu Ba!!!

Tun bayan da rikicin cikin gida ya balle a cikin jam'iyyar PDP da yawan 'yan Najeriya da kafafan yada labarai suka mayar da hankali kacokan akan al'amarin. Wannan rikici na PDP kamar yadda su 'yan jam'iyyar suka sha nanatawa cewa ba sabon abu bane a wajensu, daman sun saba da irin wannan yakin cacar bakin lokaci bayan lokaci, amma sanin kowa ne wannan rikicin ya sha bamban da duk wanda jam'iyyar ta taba fuskanta a baya, kasancewar ya hada manya-manyan duwatsun cikin jam'iyyar. Kuma a bayyane take cewar wannan rikita-rikita da dambarwa da ta dauki hankalin kusan dukkan 'yan siyasa dama wadan da ba 'yan siyasa ba, su masu kafsawa suna yi ne gaba dayansu domin neman mafitar kashin kansu, ba wai mafitar halin da Najeriya take ciki ba. 'Yan PDP kwararru ne wajen juyar da hankulan da dama daga cikin 'yan Najeriya musamman talakawa, domin wannan rikici ba wai zuwa ya yi bagatatan ba, daman can ana sane da wannan kwantacciyar a kasa, ana sane da dukkan wani zaman doya da manja da akeyi, sai da suka bari al'amarin zaben 2015 yana kara tunkarowa sannan suka kwanto wannan ruwan domin samun farin jinin talakawan da basu san yadda abubuwa ke wakana ba.

Su wadannan masu cewa sune sabuwar PDP karkashin Jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da wasu gwamnoni; da kuma su wadan da ake ganin su ne 'yan tsohuwar PDP, duk cikinsu babu wanda ya sanya halin da al'umma take ciki a gabansa, kamar yadda suka sha fada kowa na yunkurin rike madafun iko ne. Su masu kiran kansu 'yan sabuwar PDP suna yaudarar talakawa akan suna rigima da fadar shugaban kasa da kuma shugaban jam'iyyar Bamanga Tukur. Kusan idan ka cire Gwamnan Ribas Rotimi Amaechi (Wanda shima sun Arewantar da shi) kusan dukkansu 'yan Arewa ne, suna kallo aka dinga bankawa Arewa wuta; ana yayyanka mutane babu ji babu gani; ana tayar da bomabomai; ana karya tattalin arzikin Arewa, ana kashe manyan mutane amma babu wanda ya fito ya kalubalanci gwamnatin tarayyar da alhakinta ne ta karewa dukkan 'yan Najeriya rayukansu da dukiyoyinsu. Suna ji suna gani aka dinga bin unguwannin talakawa a Borno da Yobe da Kano da Bauchi ana daddasa musu Bamabamai mutane suna mutuwa babu kakkautawa, amma babu ko daya da ya nuna yatsa ga gwamnatin tarayya, balle ya yi fito na fito da ita.

Wannan ta nuna mana cewar wadannan mutane ko mun tausaya musu ko mun kusancesu, to kada ka ji da wai su ba Arewa ko al'ummar Arewa ce a gabansu ba. Tunaninsu shi ne ya za'a ayi kada shugabanci ya kubuce musu, kada damar da suke da ita ta tursasawa talakawa 'yan takara bata sunce daga hannunsu ba. Batun fitar da talaka daga cikin kangin talauci da rashin makarantu da rashin asibitoci duk ba shi ne a gabansu ba, ya isheka abin misali ga kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU tana fama da yajin aiki akan abinda suka kira hakkinsu, galibi kuma dalibanmu na Arewa ke cutuwa da wannan yajin aiki amma babu wani daga cikinsu da ya nemi kawo karshen abun, ko ya je Abuja yana zagin gwamnatin tarayya akan yajin aikin. Su duk wani mawuyacin hali da talaka zai shiga wannan ba damuwarsu ba ce. Su kuma talakawa da dama sun ara sun yafa, wasu tuni garkuwar jikinsu ta fara yin rauni wajen tausayawa wadannan gungun mutane, wasu sun fara yabo da yin kirarari ga wadannan mutane, alhali su ba su ma san talaka yana yi ba, da ka yi da kada ka yi duk ba agabansu kake ba, kana da amfani ne kadai lokacin da bukatunsu suka taso irin wannan lokacin.

A ranar 11 ga watan 5 na wannan shekarar Sashen Hausa na BBC a cikin shirinsu na Gane Min Hanya, sunyi hira da Atiku Abubakar inda ya tabbatar da cewar dukkan kudaden da ake warewa wajen tafiyar da tsaro sacewa ake yi, ya fada balo-balo, kuma wannan batu na tsaro Arewar da Atiku ke ciki ita ce wannan al'amari ya shafa amma babu wani mataki da suka dauka na ganin an kare rayukan al'umma. Suna ji suna gani tattalin arzikinmu yana durkushewa, kasuwanninmu suna komawa bayawa, harkar noma na sukurkucewa, babu wani wanda ya damu da hakan tunda suna da kamfanoninsu a kudancin Najeriya da kasashen waje. Amma saboda rashin sanin inda kai ke ciwo talakawa har murna suke tare da yabawa wadannan mutane wanda ba su damu da duk yawan mutanan da za'a kashe a jihohinsu ba. Haka suma masu gwamnati ba al'umma bace a gabansu. Muna ji aka ce wasu magoya bayan PDP da suka je taronsu na musamman a Abuja daga Adamawa su 9 suka yi hatsari kuma duk suka mutu amma ko zancen baka ji an daga ba, domin su ba ta talakawa suke ba, amma kuma a haka talakawa ke bata lokaci akansu. Lallai dole mu tashi mu san inda yake mana ciwo!

Atiku Abubakar ya bar PDP babu irin sunayan da bai kirata ba ya kafa AC, amma daga baya ya yi mata kome, kuma mutanan da ya dinga zagi sudin dai ya sake tararwa da ya komo ba wasu ne sababbi ba. Duk wannan bai isa ya nuna mana cewar wadannan mutane ba damuwarsu bace duk irin mawuyacin halin da muke ciki na matsin rayuwa. Dan haka da Bangaren su Atiku da su Bamanga Tukur duk uwarsu daya ubansu daya, babu wani nagari a kashi, da busasshen kashi da danye duk kashi ne, ita daman kura tun tana jaririya sunanta ya baci, babu yadda za'a zo daga baya bayan ta girma tayi dukkan irin barnar da ta yi, ta samu wanda ya fi karfinta sannan a ce mana ai daman ita ta gari ce. Dan ahaka mu namu ido, sai dai muce musu Allah ya karawa Barno dawaki, Allah kuma ya kara dalili.

Yasir Ramadan Gwale
05-09-2913

1 comment:

  1. Bashakka wannan ra'ayinaka zaiyi deadai da ra'ayin duk wani mutumin dan Nigeria daka bibiyan abin da ke faruwa a kasarnan.
    Wannan ra'ayi naka nima shine ra'ayi na. Allah yasa dukkan talakawa sugane cewa duka bangarorin PDP dake rikici da juna bawai dan talaka suke ba, kawai dan bukatunsu suke.

    ReplyDelete