Saturday, September 15, 2012

Sunana Al-Majiri Dalibin Tsangaya



Sunana Al-Majiri Dalibin Tsangaya

Ni al-majiri ne dalibin tsangaya, Tsangaya nan ne makarantarmu inda muke karatun al-qur’ani mai tsarki, waje ne da muke kwana mu tashi, babu rufin kwano, wani zubin idan lokacin damina ya zo bama iya barci musamman idan ana ruwa da daddare haka muke fakewa a labe a jikin garu kamar kadangaru har sai ruwa ya dauke, sannan mu sharce inda zamu kwanta. Tsagaya dai makarantar mu ce ba kamar irin makarantar boko ba ce, da ake karatu a zaune akan kujeru da litattafai da biruka. Mu a tsangaya muna amfani ne da allon katako wanda muke yin rubutu da alkalami da tawada, kowa yana da allonsa, kuma karatun kowa daban da na kowa.

Zan gaya muku kadan daga cikin tarihin rayuwata a matsayina na Al-majiri, da irin yadda muke rayuwa a tsangaya, da yanayin karatunmu, da kuma dalilin da ya sanya muke fita bara domin neman dan abin kalaci. Sannan zan gaya muku shakku na dan gane da hukumomi akan shirinsu na mayar da makarantun Allo irin na tsangaya wajen su yi dai-dai da na boko, sannan zan sanar da ku wasu hanyoyi da nake ganin idan anbi za’a taimakawa rayuwar al-majirai.

Bari na fara da gaya muku hakikanin ma’anar sunana wato AL-MAJIRI. Wannan suna na al-majiri, kusan zance suna ne wanda ake gayawa duk wani dalibi da yabar garinsu zuwa wani gari domin neman karatun al-qur’ani, inda zai hadu da sauran yara da suka zo daga garuruwa mabambanta. A mafi yawancin lokaci idan za’a kai yaro al-majiranci, yakan tafi ne da ‘yan tsummokaransa na sawa da tabarmar kwanciya da kwanan abinci da kuma Allo na katako, kusan wadan nan sune abinda aka san al-majiri yana zuwa da su daga gidansu, ‘yan gata daga cikinmu sune wadan da ake hadosu da sabulun wanka da na wanki, wadan da kalilan ne kwarai da gaske a cikin al-majirai, kasancewar galibinmu Al-majirai ‘ya ‘yan talakawa ne, iyayanmu basu da wani karfi da zasu iya yi mana dawainiya.

Al-majiri ba shi ne yake zaben makarantar da za’a kaishi ba, sau da yawa wasu daga cikin iyayanmu ma basu san makarantun da muke karatu ba, domin wani zubin amanarmu ake dankawa a hannun wasu daga cikin wadan da suka tumbatsa a harkar al-majiranci, inda suke kaimu makarantun allo mu hadu da sauran dalibai, wani lokacin sai dai kawai a sanar da malamin tsangaya cewar ankawo sabon dalibi wani zubin ko kauyensa ma wani al-majirin ba’a fada, kasancewar Tsangaya makaranta ce da ba’a cike form idan za’a shiga, ba’a bukatar takardar haihuwa ballantana ace za’a bada admission ko maganar biyan kudin makaranta.

Lokacin da babana ya kawoni tsangaya, bayan da ya hannantani ga Alaramma, ko kudin kashewa bai bani ba, ban kuma tambaya ba, haka kuma malaminma bai tambaya ba, kuma bana ganin kowa daga cikin dangi na, har sai shekarar ta zagayo sannan ne zamu ci sa’a mu tafi gida inda zamu yi sallah karama ko babba tare da iyayenmu da ‘yan uwanmu, ba kowa ne daga cikin al-majirai yake katari da irin wannan damar ta zuwa gida sallah ba, akwai wadan da idan suka fito daga gida wata kila su da komawa har gaban abada, wasu wadan da basu yi sa’a ba, saisu yi shekarar da shekaru babu ko mutum daya daga cikin danginsu da ya taba waiwayarsu, kar ka so kaji yadda irin wadan nan ‘yan uwannawa al-majirai suke cikin damuwa.

Lokacin da aka kawoni makaranta a rana ta farko, rannan na zama mai cin gashin kaina, domin zan shiga sahun ‘yan uwana da na tarar wato kolawa wadan da gaba daya shekarunmu daga 7 zuwa 15, bamu kai matsayin Garada ba; gardi shi ne al-majirin da ya balaga, kuma ya dan nu-na a karatun al-qur’ani, garada yayyanmu ne, domin suna aikenmu muna zuwa idan muka yi musu laifi wani zubin har horo suke yi mana, sai dai ba me yawa bane.

A wajen ‘yan uwana kolawa zan sami gamba na koyi yadda ake fike al-kalami da yadda ake rubutu, sai dai lokacin da aka kawomu Alaramma ne yake yi mana rubutu domin ba mu kai waladaina ba, za dai mu ringa yin rubutu a cikin allon-sha dan hannunmu ya fada, kafin mu koma yi da kanmu. Wannan shi ne kadan daga cikin rayuwar da muke a tsakaninmu kolawa da yayyenmu garada.

Bari kuma yanzu na yi muku bayani dangane da bara. BARA dai kolawa ne suke yin ta domin fita waje su samo dan abinda aka ci aka rage, kolawa saboda su yara ne shi yasa suke yin bara, amma duk mutumin da ya kai matsayin gardi baya yin bara. Kolawa sune wadan da ko mai gida ya shigo ya gansu a gidansa suna bara ba zai ji wata damuwa ba, sabanin idan gardi ne, domin ya balaga, mutane bazasu bari ya shigar musu gida yana bara ba.

Muna shiga gida gida ne, muna cewa ko dan kanzo iya, ko dan dago dago iya, iya nine danki muhammadu. Wannan dai su ne kalaman da kolawa suka fiya yi a duk gidan da suka shiga yin bara, sai dai yanayin wasu garuruwan yakan sha bamban da na wasu haka kuma, irin kalaman da ake fada suma akan samu sauyi daga wani wajen zuwa wani wajen. Akan kirawo mu da ALMAJIRI KAWO KWANON KA, mukan samu ragowar tuwan da aka ci aka rage wato tuwo miyar kuka ko kubewa wani zubinma muka sami shinkafa da wake ko dai wani abincin da aka ci aka rage. Wannan abincin da muka samu shi muke ci, sannan mu yo guzurin wani zuwa makaranta, kolawa idan sun dawo daga bara sukan zo da abinci kala-kala, anan ne wasu daga cikin garada da suke tsangaya zasu zabi wanda suke so su ci suma, haka kuma idan aka yi dace da samun wani abinci mai dadi akan kaiwa Alaramma ya sanya albarka.

Sau da yawa abin da muka barato da daddare shi ne muke ci da safe, wato Karin kumallo. Domin almajirai basa yin bara da safe, duk almajirin da ka gani yana bara da safe to ba al-majirin tsangaya bane, domin na tsangaya suna da lokuta kayyadaddu da suke fita yin bara. Mukan fita bara ne daga karfe 11 na safe zuwa karfe 2 na rana domin mu sami abincin da zamu ci na rana (lunch) sannan mu sake komawa bara daga karfe 8 na dare zuwa karfe 9 na dare, wadan nan sune lokatan bara. Duk al-majirin tsangaya baya bara da yamma kamar yadda na ce baya yi da safe ko bayan sallar magaruba, duk wani al-majiri da kuka gani yana bara a wadan can lokuta da nace ba’a bara to shakka babu ba al-majirin tsangaya ba ne, ma’ana ba mai neman karatun al-qur’ani bane.

Kolawa basa yin bara dan a basu kudi, ko ka gansu akan titi suna wanke gilashin motoci, al-majirai muna bara ne kawai domin samun abin da zamu ci. Muna yin uwar daki wato gidan da muke zuwa muna yi musu aiki kama daga debo ruwa da zubar da shara shima ladanmu shi ne a bamu abinci ba kudi ba. Haka kuma, idan kuka ga al-majiri a kasuwa ko tasha ko kan danja wato mahadar tituna to ku tabbaci hakika ba al-majirin tsangaya bane, ba mai neman karatun al-qur’ani bane. Wannan shi ne bayani dangane da bara.

Abu na gaba kuma, zan yi muku bayani dangane da yadda muke karatu. Kamar yadda na fada tsangaya dai makaranta ce da ba’a bukatar ka cike wata takarda domin samun izinin shiga, haka kuma, babu wata takardar shaida da ake bayarwa ga duk wanda ya kamala karatunsa na tsangaya. Muna rubuta al-qur’ani ne da hannu sannan mu hardace shi, wannan zata bamu damar mu wanke allo sannan mu kuma yin wani rubutun haka za ayi ta yi har sai an sauke al-qur’ani, idan kuwa aka sauke to har da haddarsa gaba ki daya aka sauke.

Wasu suna karatu hade da yin darasu, wasu kuma sai sun gama sannan zasu ringa rubuta al-qur’ani da ka, sannan su je wajen malami ya yi musu darasu, malam baya yarda ko kadan ka leka takardar al-qur’ani a lokacin da ake yi maka darasu, za’a yi maka gyara ne ka haddace shi da ka! Daga lokacin da mutum ya kamala darasu to ya zama alaramma shima, idan yaso sai ya koma ya tuso tilawa, daga nan kuma ya rubuta al-qur’ani idan kuma aka ci sa’a ya rubuta kuma ya haddace ba tare da anci gyaransa ko da na fataha bane to wannan ya zama GWANI kenan. Allah ya bamu albarkacin Al-qur’ani.

Daga nan kuma sai mu matsa zuwa zauruka domin daukar karatun litattafai a wajen malamai na soro ko zaure. Anan ne zamu koyi kaw’idi da ahalari da litattafan fiquhu domin mu san hukunce-hukuncen addini. Daga wannan lokacin kuma sai Alaramma ya shiga duniyar neman ilimin addini, yana bin zauruka da masallatai yana daukar karatu na ilimi.

Idan zamu iya tunawa mai girma shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taba cewa tsarin karatun tsangaya shine silar sukurkucewar al’amuran tsaro, kuma shi ne kashin bayan kungiyar Boko Haram. A wannan gabar nake gayawa shugaban kasa cewa ya yi babban kuskure akan wancan ikirari nasa. Ni al-majiri dalibin tsangaya ina tabbatarwa da shugaban kasa cewa ni ba dan Boko Haram bane, haka kuma tsangaya bata koyar da kowa Boko Haram. Sai dai kamar yadda ake iya samun bata gari a cikin al’umma da Dukkan bangarori na rayuwa, to ana iya samun bata gari a cikin ‘yan uwana al-majirai daliban tsangaya.

Me Tsngaya ta ke bukata? Abinda Tsangaya take bukata shine cikakken tsarin koyo da koyarwa wanda ya dace da addinin musulunci da kuma al’adar Hausawa, komai kyan tsari indai bai dace da irin al’adarmu ba, shakka babu ba zai samu karbuwa ba. Muna bukatar a inganta mana tsangayu da samarwa alarammominmu cikakkiyar kulawa da samun walwala. Muna bukatar samun makewayi, domin daga cikin irin hantarar da jama’a suke yi mana shi ne cewar muna bata musu gurare da kasha da fitsari, wannan kuwa ba laifinmu bane, domin kowa yasan kasha da fitsari larura ce da ta ke kan kowa, kuma hukumomi basu yi mana tanadin makewayi ba, sannan kuma, muna bukatar samun famfuna inda zamu ringa samun ruwan sha da na wanka da kuma wanke ‘yan tufafinmu, wannan dangane da muhalli kenan.

Idan kuma muka juyo ta bangaren walwala da jin dadi. Al-majirai muma ‘ya ‘ya ne, muna da bukatar mu ringa cin abinci kamar yadda dan kowa yake ci ba ragowa ba, anan ina nufin a samar mana da masu dafa abinci da kuma shi kansa abincin da za’a dafa mana, da bamu tufafin da zamu ringa sauyawa, da sabulun wanka da na wanki.

Makarantun tsangaya bamu da bukatar tsarin karatu na tantebur (time table). Domin wannan tsari ne da ya ci karo da irin yanayin da muka taso da karatun al’qur’ani tun tale-tale, haka kuma, bamu da bukatar sai ansamar mana da litattafai da kujerun zama a tsangaya, mun fi bukatar tabarmi akan kujerun da ake so a samar mana.

Ya mai girma shugaban kasa, ta ya ya za’a ce mu biyo wadan nan hanyoyi na karatu a tsangaya, rana a tsaka za’a dauko ‘yan boko wadanda wani ma bai taba yin karatun allo ba tun da uwarsa ta haifeshi ace sune zasu tsara mana yadda karatun tsangaya ya kamata ya kasance, muna da tsari, muna da alarammomi, sun san Dukkan abubuwan da makarantun tsangaya suke da bukata, indai taimako za’a yi mana na fisabilillahi, sai a tuntubemu a ji ra’ayinmu. Sannan mu kanmu al-majirai a ji tabakinmu domin muna da abin fada da yawa.

Kamar yadda na fada tsangaya bata da bukatar cike wani form idan za’a shiga! To me ya sa aka ce wannan tsari na makarantun tsangaya na zamani da gwamnati ta kuduri aniyar samarwa a daukacin jihohin Arewa sai Al-majirai ne kadai zasu ci gajiyarsu? Anya kuwa babu wani lauje cikin nadi? Indai  gaskiya ne abar abin kofa bude mana duk mai sha’awa ya kawo dansa shima ya zo ya zama kolo, kuma mu da muke karatun al-qur’ani bamu da bukatar sai an koya mana turanci a tsangaya.

A kyale mu mana muje makarantar boko kamar yadda ‘ya ‘yan kowa suke zuwa makarantar boko, muma ‘ya ‘ya ne muna son karatun zamani. Amma danme aka waremu aka ce sai mu kadai, a barmu mu shiga makarantun da muka ga dama mana, mu zauna tare da sauran yaran al’umma, muma mu ci gajiyar ilimin zamani. Indai har da gaske hukuma ta ke, to daga yau ta ce Dukkan wani al-majiri ya je Dukkan makarantar da yake son karatun boko gwamnati zata dauki nauyinsa, Alabashshi abar mana tsangayunmu yadda muke karatunmu.

Daga karshe, ina son na tambayi shugaban kasa da mukarrabansa shin menene hakikanin gaskiyar wannan al’amari na gina makarantun tsangaya guda 100 a Arewacin Najeriya? Shin anyi ne domin taimakon tsangaya da daukaka darajar tsangaya ko kuwa anyi ne domin dakushe tsangaya da karatun al’qur’ani? Kamar yadda muka ji ance gwamnatin tarayya ta ware kudi har Naira Biliyan Biyar (5B) domin giggina wadan nan makarantu. Lokacin da mai girma shugaban kasa ya je Sakkwato bude makarantar tsangaya ta farko da gwamnatin tarayya ta gina, munji ance sauran ragowar suna dab da kammaluwa, domin anci kasha 75 na aikinsu, shin me ya sa har yanzu bamu sake jin mai girma shugaban kasa ya kuma bude wata makarantar tsangaya ba?

Sannan wane tabbaci muke da shi cewar wadan nan kudade da aka ware domin wannan aikin ba za’a sace su ba, kamar yadda aka sace kudin samarwa ‘yan Najeriya wutar lantarki zamanin Obsanjo har kusan Naira Tiriliyan daya da Biliyan uku, haka kuma, muna da masaniyar yadda aka sace kudin fanshon ‘yan sanda har kusan naira Biliyan talatin da shida (36B) duk wadan nan sunfi al-majirai kima da daraja a idon gwamnati amma aka sace dukiyarsu ko kuma hakkinsu, inaga namu mu al-majirai da bamu da wani gata sai mahaliccinmu.

Kuma ni a matsayina na al-majiri ina ta jin mutane suna korafi cewar harkar ilimi ta tabarbare gabaki daya ta yadda ‘yan makarantar boko basa iya cin jarabawa, malaman kuma basu da wani ingancin da zasu koyar, amma duk da wannan surutu da balokoko da al’ummar kasar nan suke yi, gwamnati bata ware wasu makudan kudade ba, wajen ingantasu sai makarantar Tsangaya, zance na gaskiya ina cike da shakku mai yawa akan wannan al’amari na inganta makarantun tsangaya, ban sani ba watakila saboda ni al-majiri ne shi ya sa nake irin wannan tunani.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale 

No comments:

Post a Comment