Friday, September 14, 2012

Akwai Bukatar Sake Fasalta Aikin Dan Sanda A Najeriya



Akwai Bukatar  Sake Fasalta Aikin Dan Sanda A Najeriya

Da farko zan fara da yabawa sifeto janar na rundunar ‘yan sanda Muhamma D Abubakar. Hakika ga duk wanda ya saurari kalaman shugaban ‘yan sanda na kasa tun bayan kama aikinsa zai yaba masa tare kuma da kyautata masa zato cewa lallai da gaske yake, domin shugaban ya fito ya fadi gaskiyar irin munanan halayen ‘yan sandan Najeriya da kuma rashin iya aikinsu, wannan kusan abu ne da duk dan Najeriya yake da masaniya akansa ga ‘yan sanda. A wata zantawa da ya yi da shuwagabannin ‘yan sanda na kasa, ya fito fili ya farke musu laya inda ya zargi ‘yan sanda da cin hanci da rashawa da kuma rashin iya aiki da munanan halaye da sauran dabi’un da basu dace da aikin dan sanda ba, ya kara da cewa ana tura ‘yan sanda ga daidaikun masu kudi da kamfanoni wanda hakan ya sa hukumar ‘yansanda suke rasa jami’an da za su gudanar da aikin samar da tsaro  ga talaka; sannan yace sassan binciken rundunar ‘yan sanda ba za su iya gudanar da ayyuka cikin adalci ba, sai dai in wadanda lamarin ya shafa suna da kudi. Ofisoshin ’yan sandan da sassan binciken miyagun ayyuka (CIDs) da jami’an gudanar da ayyuka sun zamo cibiyoyin hada-hadar kasuwanci da wuraren amsar kudade daga ayyukan da bataliyoyi da rukunnan ’yan sanda da na sama suke kafa su domin amfanin kansu.

Hakika duk wanda ya duba wadan nan maganganu da sabon sifeto ya yi zai sa ran samun gyara a tsawon wa’adinsa. Shakka babu aiki a kasa shi ne zai tabbatar da wannan batu, domin akacewa kare ana biki a gidansu yace mu gani a kasa, don haka muna kyautata zato akansa cewa zai kawo sauye sauye masu ma’ana a rundunar ‘yan sandan Najeriya, ganin cewa kusan adadin yawan ‘yan sanda Najeriya bai wuce 400,000 ba, haka kuma rundunar yansanda tanada akalla babban caji ofis da ake kira Police Division guda 1,115 a duk fadin Najeriya, haka kuma, akwai matsakaitan caji ofis da ake kira police Station guda 5,515 da kuma kananan ofisoshin ‘yan sanda na cikin unguwa da ake kira out post kusan 5,000. Lallai duk wanda ya kalli wannan adadi yasan akwai bukatar akawo sabbin sauye sauye a harkar ‘yansanda na kasa, tare da kara adadin yawan ‘yan sanda da kuma ofisoshinsu, yanzu a Najeriya ana maganar mutum miliyan 167 ta ina wadan nan ‘yan sanda zasu iya lura da wadan nan dumbin al’umma mai wuyar sha’ani.

Sannan duk da haka akwai kusan ‘yan sanda 120,000 da suke a gidanjen masu kudi da kamfanoni da kuma rakiya ga manyan jami’an gwamnati. Wanda wannan wani abin takaici ne a lokacin da ake fuskantar matsalar tsaro amma dagangan aka tura irin wannan adadi suke aikin tumasanci da maula da sunan bada kariya, domin duk dansanda da ka gani kofar gidan wani babban jami’in gwamnati dan jagaliya ne, hakama wadan da suke a manyan kamfanoni da suka hada da bankuna zaka samu kawai kasuwancinsu sukeyi, duk da cewa kudin da aka ware a harkar tsaro a kasafin kudi na wannan shekarar sunada dan karen yawa, wanda idan tsaron ake da gaske, wannan kudi zai isa dan najeriya ya kwanta a kofar gidansa ya yi barci harda minshari batare da yana fargabar ko da cinnaka ba.

Misali a kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012, abin da aka warewa hukumar ‘yan sanda shi ne Naira Biliyan 331.2. wanda wannan adadi ya kunshi ofishin babban ministan ‘yan sanda da kuma rundunar ‘yan sanda da kuma sauran sassan ‘yan sanda. A cikin wannan adadi an ware Naira Biliyan 5.8 domin aikin ofishin ministan ‘yan sanda na kasa, sannan an warewa rundunar ‘yan sanda da manyan bangarorinta kusan Naira Biliyan 307.9, har ila yau kuma an warewa hukumar gudanar da  aikin ‘yan sanda Police Service Commission Naira Biliyan 2.5. idan har za’a rabawa kowane caji ofis na ‘yan sanda a kalla kowanne zai tashi da Naira 696,000, haka kuma, bisa la’akari da wadan nan alkaluma kowane caji ofis zai kashe abinda bai kai naira 2000 a kowace rana domin tsaron ‘yan Najeriya. Wanda wannan abin kaico ne, idan ka dauki mashawarcin kasa na fuskar tsaro wanda ake kira National Security Adviser shi kansa yana da masu bashi shawara kusan mutun 100 wadan da suke lashe kusan Naira Miliyan 950, anya kuwa da gaske ake a harkar tsaro? Musamman dukiya da rayukan talakawa?

Shakka babu aikin dan sanda muhimmin aiki ne da bai kamata a yi wasa ko sako-sako da shi ba. Dan sanda shi ne kusan al’umma suke cikin bukatarsa a koda yaushe, don haka suna da bukatar kayan gudanarwa masu inganci kwarai da gaske. Kamar yadda sabon sifeto ya zargi ‘yan sanda da rashin iya aiki, sai kayi mamaki a Najeriya dan sanda yana cewa mu bamu saba da irin wannan hari na sunkuru ba, ko kuma bamu saba da harin ‘yan ta’addaba, duk wanda yaji wannan yasan da cewa akwai wauta da rashin iya aiki da tsoro, domin a har kullum shi mai laifi ai kokari yake ya yi amfani da hanyar da jami’an tsaro basu santa ba wajen aikata laifinsa, don haka wannan wajibin ‘yan sanda ne su sake dabaru na tunkarar abokan gaba, da kuma iya kwance muggan makai ko abubuwa masu iya fashewa. Misali lokacin da wani Bom ya tashi da wani Dan sanda a jihar kaduna akwanakin baya a kusa da masallacin sarki musulmi Bello, kusan lokacin da akaga wata jaka ake kyautata zaton Bom ne an nuno wani dan sanda hannu rabbana ya tunkari wannan jaka zai bude, kaga ko shakka babu wannan akwai wauta aciki, tayaya hukuma zatabar danta ya sayar  da rayuwarsa a arha ta irin wannan hali, domin ina amfanin ‘yan sanda masu kayan aikin kwance boma bomai da ake kira Anti-Bomb Squard?

Sannan lallai akwai bukatar baiwa ‘yan sanda horo na musamman akan kama mai laifi batare da anhalakashi ba. Abin mamaki sai kaga ‘yan sanda kamar a tsorace suke idan anje inda masu laifi suke maimakon a shirya dabarun kamasu kawai sai dai kaji ruwan harsasai sun bude wuta, wanda bisa ga dokar ‘yan sanda haram ne dan sanda ya harbi mai laifi sai dai fa idan yaga babu yadda zaiyi da shi, kuma shima harbin akwai mataki da ake bi, domin kodai ayi amfani da hayaki maisa kwalla ko harsashin roba, idan kuma ta kama za’ayi amfani da harsashi mai rai to a harbi kafafu; amma abin mamaki shine duk ‘yan sandanmu basa bin wannan mataki, kusan wanda ba’ace suyiba shi sukeyi na harbin mailaifi a kirji ko a kai. Misali, ‘yan kwanakin da suka gabata wasu ‘yansanda a unguwar rijiyar zaki a kano suka budewa wasu mata wuta. Wai da sunan farautar ‘yan Boko Haram, haka kuma, wani dan sanda ya harbe wani yaro har lahira a unguwar Gwale daura da caji ofis na Gwale, wannan ko shakka babu shi ne yake kara nuna rashin kwarewar ‘yansanda tare da rashin ilimi da ya yi musu katutu, rayukan al’ummar kasa yafi komai daraja, domin da babu al’umma da shi kansa dansandan bashi da amfani, shi ya kamata ya salwantar da rayuwarsa domin kare al’umma kamar yadda yake a kundin dokar ‘yan sanda.

Sannan batun samar da ‘yan sandan jihohi wanda yake ta tayar da kura, shima wani muhimmin batu ne da bai kamata siyasa ta dabaibaye al’amarin ba. Domin babu yadda zaka dauki dansanda daga Abakalaki ka kaishi kauran Namoda kace ya baiwa al’ummar wajen tsaro da kariya, domin na farko yarensu ya sha bamban, addininsu ya saba, abinci, sutura da al’adu duk sun bambanta sannan kuma uwa uba baisan takan yadda garin yake ba, taya kake sa ran cewa wannan dansanda zai iya farutar mailaifi a wannan yanki? lallai idan aka sami ‘yan asalin waje to shakka babu su sukafi sanin yadda za’aci lagon masu laifi, kamar yadda babu yadda zaka dauki dansanda daga Malunfashi ka kaishi Otu-oke ko Ikorodu kayi tsammanin zakaga daidai, wannan yasa da yawa daga ‘yan sandan Najeriya matsorata ne na gaske.

Duk wanda ya kalli irin yadda ‘yansanda ke jibge buhunan yashi jibge a kofar kowace haraba ta ‘yansada ta jihohi ya san da cewa a tsorace suke. Dan sanda aikinsa shi ne ya baiwa al’umma kariya ba kansa ba, za kaga sunyi kuri da ido sun zuro kan bindiga waje suna muzurai, wanda kuma wannan yake nuna duk mutumin da ya koma kare kansa a gida, shakka babu ancishi da yaki, aikamata ya yi suyi kokari wajen amfani da kwarewa da fasaha wajen hana miyagu sakat, ta yadda bazasu iya shigowa cikin al’umma su aikata miyagun laifuka da mugun alkaba’i ba.

Sannan lallai a tanadi hora mai tsanani ga duk dansandan da aka samu da sakaci ko sabawa dokar aiki. A kwanakin baya ansami wasu ‘yansanda da sukayi garkuwa da wata budurwa suka dinga aikata zina da ita, wanda wannan mummunan aiki ne, kuma yana bukatar horo mai tsanani, da kuma hukunta dukkan wanda aka kama da laifin harbin kan mai uwa da wabi, irin haka yayi sanadiyar mutuwar matashin nan wanda ya shiga zanga zangar Allawadai da janye tallafin manfetur a legas, inda dansanda ya bude wuta akan ‘yan zanga-zanga.

Haka kuma, harkar jindadin ‘yan sanda wani muhimmin abune da ko kadan bai kamata ayi sakaci da shi ba. Tayaya za’a baiwa mutane bindigogi da harsasai masu rai sannan kuma a hanasu samun kyakykyawar walwala ayi zaton samun abinda akeso, lallai ya zama dole a inganta albashi da alawus-alawus na ‘yansanda, tare da basu horo akai-akai, da kuma, samar da sabbin kayan aiki na zamani da suka hada da kayan sadarwa, da motoci masu silke da marasa sulke, da rigar kariya da ake kira bullet proof da sauransu, duk da mun san akwai su, amma basu wadatar ba.

Sannan yana da kyau a sake duba tsaffin rahotannin kwamitin binciken yadda za’a fasalta aikin dan sanda a Najeriya wanda Alhaji MD Yusuf tsohon shugaban ‘yan sanda na kasa ya yi a shekarar 1994; da kuma wani rahoto da Tamuno ya yi mai suna National Security, da kuma wanda Danmadami da MD Yusuf da Osayande suka jagoranat a shekarun 2001 da 2008 da kuma 2012. Muna fatan  Shugaban ‘yan Sanda zaiyi amfani da kwarewa wajen kawo sabbin sauye-sauye wadanda magabatansa basuyi ba. Akwai tsaffin ‘yan sanda da sun nuna kwarewa kwarai da gaske kuma sun cancanci a yaba musu irinsu Ibrahim Kommasi da MD Yusuf da Nuhu Ribadu da Muhammadu Gambo Jimeta da sauransu. Haka kuma, anyi wadan da suka tafi nan bada jimawa ba irinsu Sunday Ehindaro da Mike Okiro da Obonnaya  Onovo da kuma Hafiz Ringin duk wadan nan ya kamat su zama darasi ga  shugaban ‘yansanda MD Abubakar, yasan wadan da suka kammala aikinsu lafiya kuma suke da kima har yanzu, sannan kuma yasan wadan da suka gama babu yabo babu fallasa da kuma masu abin kunya da Allah wadai irinsu Tafa Balogun.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@hotmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale


No comments:

Post a Comment