Sunday, September 9, 2012

Fim Din Umar!



Fim  Din Umar!

Umar: wani shiri ne na wasan kwaikwayo da gidan Talabijin na MBC 1 suka gabatar a watan Azumin Ramadhan da ya gabata na wannan shekara ta 1433. Wannan fim na Umar kusan ya dauko hoton rayuwar khalifa na biyu bayan Manzon Allah salallahu Alaihi wasallam ne a takaice, inda aka bayar da tarihinta, ta wata irin siga wadda mutane zasu yi saurin fahimtar wanene Khalifa Umar? A cikin wannan shiri anyi bayanin irin Yana yin gwamnatinsa (Umar), da Gaskiyarsa da Adalcinsa a matsayinsa na Amirul mu’uminina, sannan wannan shiri ya yi karin haske akan rayuwar Khalifa  Umar ta kashin kansa, wato rayuwa wadda yake gudanarwa zatiyyan shi da iyalinsa.

Idan ba mu manta ba, a wasu ‘yan shekaru da suka gabata shi wannan gidan Talabijin na MBC1 a cikin watan Azumi ya taba gabatar da wani shirin wasan kwaikwayo irin na tarihin Musulunci mai suna HURUN EIN, wanda malamai da dama a cikin kasashen Larabawa suka soki wannan fim din da kakkausar Murya, dole ta sanya Gidan talabijin na MBC suka janye wannan fim din.

Wannan shiri na Umar kusan ankwashe kwanakin Azumi gabaki daya ana kawoshi sau biyu a kowace rana a tashar MBC 1. Ana  yin sabon shirin da karfe 8:00 na dare a gogon Najeriya, sannan a sake maimaitashi da karfe 8:00 na safe a agogon Najeriya. Shi dai wannan fim kusan na hadin gwiwa ne da gidan Talabijin na Qatar TV, su suka yi hadin gwiwa wajen watsa shi ga daukacin kasashen Larabawa, da kuma wasu daga cikin kasashen Afurka, musamman wadan da suke iya kama tashar MBC din a Nile da Arab Sat. Haka kuma, an watsa wannan shiri a kasar Indonesia kai tsaye daga tashar MBC zuwa gidajen talabijin da ke kasar ta Indonesia inda kuma aka fassara shi da yaren kasar.

Wani katafaren kamfanin shirya fina-finai ne da ke kasar Turkiyya mai suna 03 Production tare da hadin gwiwar ATV Network suka dauki nauyin shirya wannan fim din, a wani waje na musamman da aka tanadar domin shirya wannan fim, da ake kira da sunan Film Village a turance. Akalla ana zaton sama da mutum Miliyan 190 ne suka kalli wannan fim a dukkan kasashen da aka haska shi ko kuma wadan da suke da damar kama tashar MBC ko kuma Qatar TV da kuma mutanan gabas me nisa na Indonesia.

Kusan, daga farkon wannan fim, an nuna irin yadda Khalifa Umar Bin Khattab ya yi rayuwa ta jahiliyya da kuma rayuwa irin ta Musulunci, da kuma irin yadda ya rayu tare da manzon Allah salallahu Alaihi wasallam. Sannan an nuna zamantakewarsa da mu’amalarsa da sauran abokansa sahabbai kamar su Abubakar Bin Abu-Kuhafa da Usman Bin Affan da Aliyu Bin Abi-Talib da sauran Sahabbai. Sannan wannan fim ya yi karin haske akan irin yakukuwan da Umar ya halatta tare da Annabi da kuamirin bajintar da ya nuna.

Haka kuma, an nuna jarumtaka irin ta Umar Bin Khattab da kuma nuna tausayawarsa ga al’ummarsa, da kuma irin tsoron Allah da yake da shi da kankan da kai da tawali’unsa ga Allah subhanahu wata’ala. Kusan duk wani lungu da sako na rayuwar khalifa Umar wannan fim ya tabo ta a takaice.

Sai dai wani fitaccen Malamin Jami’ah da ke a kasar Saudiyya, mai suna Prof. Khalid Al-Muleh da ke a jami’ar nan ta Al-Qassam University ya soki lamirin wannan fim sosai, inda ya bayyana shi da cewa cin-fuska ne ga Amirul-muminina Umar Bin Khattab Allah ya yarda da shi. Shehun malamin a lokacin da yake zantawa da jaridar  Al-Hayat ta kasar Saudiyya ya ce bai kamata a ringa nuna sahabban manzon Allah ta irin wannan siga da aka yi amfani da ita a wannan shiri ba, ya kara da cewa babu nuna girmamawa ko ladabi ga Sahabbai a ringa sanya wasu mutane da sunan cewa wannan shine Umar ko Abubakar da sauransu.

Haka kuma, malamin ya kara da cewar wannan fim din yana iya bayarda da dama ga masu zagin Khalifa Umar Bin Khattab su zageshi, musamman inda ya ce akwai wajejen da bai kamata a ce an nuna su ba, yana ganin miyagu azzalumai masu zagin sahabbai zasu iya fakewa da wannan wajen cin-kasuwarsu wajen zagin sahabban manzon Allah.

Bayan wanna malamin Jami’ah malamai da yawa daga kasar Saudiyya da Bahrain sun soki wannan fim. Inda da yawa suke ganin kamar yadda bai halatta a nuna wani hoto da sunan cewa Manzon Allah  ba ne, haka ba kamata a ringa sanya wasu mutane da sunan cewa wadan nan sune sahabban manzon Allah Salallahu Alaihi wasallam, suka kara da cewar wani zubin akan sanya mutanan da ba Musulmi ba wajen gudanar da irin wadan nan fina-finai, kamar yadda ya faru a fim din tarihin fitaccen dangwagwarmayar nan na kasar Libya wato Umar Mukhtar, suka nuna cewar wajibi ne a kiyaye al-farmar sahabbai ta wannan janibi.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment