Wednesday, November 25, 2015

Magajin Garin Kano Tsohon Mukaddashin Firaminista Ya Kwanta Dama


MAGAJIN GARIN KANO MALAM INUWA WADA YA KWANTA DAMA 

Tsohon Minista, tshon Dan takarar Shugaban kasa, tsohon dan siyasar Jamhuriya ta farko da ta biyu da ta uku kuma Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada ya kwanta dama. Daya ne daga cikin ministocin da suka rage tun Jamhuriyar farko a Nigeria, Malam Inuwa  Wada (Magajin Garin Kano) ya riga mu gidan gaskiya a yau dinnan. Ya rasu yana da shekaru 103 a mafi rinjayen zance. Marigayi Magajin Garin Kano, shi ne mutum na farko da ya fara assasa siyasar Jam'iyya a Arewacin Najeriya. Tun cikin shekarunsa na kuruciya Magajin Gari ya kafa Skawut  (Boy scout) a Arewacin Najeriya baki daya, kafin daga bisani ya zama Babban Jam'in Skawut na yankin Arewa baki daya. 

Magajin Garin Kano da a ne daga cikin mambobin majalisar kasa ta farko kuma tsohon Ministan ayyuka da ma'aikatar sha'anin tsaro. Yana daga cikin kalilan din mutanan da sukai tasiri kuma masu hazaka  a siyasar Jamhuriya ta farko da ta biyu. Ya taba tsayawa takarar shugabancin Najeriya a Jamhuriya ta uku. Ya yi aiki da gaskiya da nuna jarumataka da kwazo sosai a dukkan mukaman da ya rike.

Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada ya taba rike ragamar Najeriya baki daya a lokacin da Marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa ya bashi rikon ragamar,  dan ya zama mukaddashin Prime Minister a lokacin Balewa yayi wasu tafiye tafiye. Yana daga cikin mutanan da ska tsallake juyin mulkin 1966 da yayi sanadiyar rasuwar Sir Abubakar Tafawa Balewa a Lagos da Sir Ahamadu Bello Sardaunan Sokoto Firimiyan Jihar Arewa a Kaduna, ya tsallake 30 jiya da baya lokacin da aka kai harin yana kasar Geneva dan duba lafiyar idonsa.

Marigayi Magajin Garin Kano Malam Inuwa Wada yana da dangantaka ta jini da tsohon Shugaban kasa Marigayi Murtala Mohammed, shi ne mutumin da ya saka shi a makaranta kuma ya rabba shi har zuwa shigarsa aikin sojan da yayi silar zamansa Shugaban Najeriya. Ance Magajin Garin Kano MalamInuwa Wada duk da tsufa da yawan shekaru Sallar Jam'i bata cika wuce shi ba. Allah ya jikansa ya gafarta masa ya yafe masa kurakuransa. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-11-2015


No comments:

Post a Comment