Sunday, November 29, 2015

Domin Magance Matsalolin Tsaro Gwamnonin Arewa Su Yi Koyi Da Jihar Gombe


DOMIN MAGANCE MATSALOLIN TSARO GWAMNONIN AREWA SU YI KOYI DA JIHAR GOMBE 

Jihar Gombe na daga cikin jihohin da suka sha fama da matsalolin tsaro, kama daga na tashin bama ba ai musamman a tashoshi mota da kasuwanni da kuma hare hare kuna bakin wake. Gwamnatin Gombe karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, ta yi himmatu wajen ganin ta shawo kan tare da kawo karshen matsalolin tsaro a jihar. Bayan tattaunawa da kuma yin Nazari mai zurfi na bin hanyoyin da za a shawo kan matsalolin tsaron a jihar. Gwamnatin ta yi wani tsari na dauko hanyar mutanan da ake kira Civilian JTF da suke Maiduguri domin taimaka musu a sha'anin tsaro.




 A dan haka ne Gwamnatin Gombe, tayi musu tsari na kula da walwalarsu da basu alawus mai kauri domin wannan aiki. Gwamnatin ta zabe mutane masu Amana, da fatan ganin zaman lafiya ya dawwama a Najeriya ta zuba su a cikin gari a matsayin masu talla ko masu goge takalma, amma suna lura da motsin kowa dan haka da zarar sunga mutumin Borno ko wani Kanuri da suke da shakka akansa zasu cunawa Jami'an tsaro, haka kuma, suna nan a unguwannin da yawa suna yawo a matsayin masu talla. Da farko Gwamnati ta so ta basu motoci da babura, suka shaida mata aikin nasu baya bukatar wannan.


A ranar farko da wadannan mutane suka fara aiki a Gombe, sai da suka gano gidaje kusan biyar a cikin garin Gombe da ake kera Bom, kuma sun kama Bamabaman da aka kera sama da guda dari, bayan an cafke mutanan da suke wannan danyan aiki. Wannan tasa, Gwamnati tayi Nazarin irin hadarin aikin, kuma gashi ba ma'aikata bane na din-din-din da suke da fansho da garatuti, dan haka ne, Gwamna yayi umarnin baiwa wadannan CJTF alawus na Naira dubu goma a kowacce rana, dan haka Gwamna yace duk sati za'a dinga biyansu wannan alawus.

Cikin taimakon Allah, tunda Gwamnatin Gombe tayi wannan tsari har yau Bom bai kuma tashi a Gombe ba. Ba shakka wani tsari abin yabawa ne, duk da cewa rayuwa da mutuwa duk a hannun Allah suke, amma yana daga cikin wajibin hukumomi tsare jini da dukiyar al'umma. Kuma wannan tsari yana da kyau sauran Gwamnatocin Arewa su kwaikwaya, domin tsare rayuka da dukiyar al'umma. Girma da daraja ta Ran dan Adam tafi dukkan abinda za a baiwa mutanan a matsayin alawus. Dan haka, nake kara jinjinawa Gwamnatin Gombe karkashin Gwamna Dankwambo akan wannan hobbasa da tayi domin kula da tsaron rayukan al'umma. Anan nake kira da Babbar murya ga sauran Gwamnatocin jihohin Arewa musamman wadan da suke fama da wannan matsala ta tsaro da su yi koyi da gwamnatin jihar Gombe. 

Domin ko da Gwamnatin tarayya tayi nasarar fatattakarsu daga dajin Sambisa, to wannan ba shi ne yake nuna kawo karshen 'yan ta'adda masu tayar da Bamabamai ba, tilas ayyukan tsaro karkashin jihohi ya cigaba domin amintar da al'umma a gidajensu da masallatai da guraren kasuwancinsu. Haka nan sauran Jami'an tsaro masu kaki, tilas a kula da walwalarsu da basu hakkokinsu akan kari domin samun karsashi da kuzarin yin aiki dan kula da ayyukansu na wajibi da kuma basu kwarin guiwa ta hanyar ziyarar su da karfafa musu guiwa. Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya mai dorewa a jihohinmu da kasarmu baki daya. 

Yasir Ramadan Gwale
28-11-2015

No comments:

Post a Comment