Friday, November 28, 2014

SHAIDU: Yadda Harin Boko Haram Yai Ta'adi Ga Masu Ibada A Kano

SHAIDU: Yadda Harin Boko Haram Yai Ta'adi Ga Masu Ibada A Kano

Naman mutane ya warwatsu a harabar Masallacin Juma'a na kofar gidan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II. Wani mutum ne da yayi jigida da bamabamai ne yai yunkurin kutsa kai cikin Masallacin a lokacin da Liman yake jagorantar Sallar Juma'a a yau dinnan. 

Gawarwakin mutane sun warwatsu a farfajiyar masallacin, ko dai wadan da harin bom din ya kashe kai tsaye ko kuma wadan da suka mutu ta sanadiyar harbin binduga ko kuma wadan da suka rasu sakamakon turmutstutsu. 

Sai dai wata majiya daga fadar Kano tace Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi yana kasar Faransa a lokacin da wannan bala'i ya auku, majiyar tayi karin bayanin cewar Sarkin ya tafi Faransa ne domin binciken lafiyarsa, haka kuma, manyan 'yan majalisar Sarki sun halarci wannan Sallah tare da Liman a cikin masallaci.

Bom na farko ya tarwatse ne a daidai lokacin da liman ya fara Sallah. Wani dan kunar bakin wake ne da ya makare wata karamar Toyota da bamabamai ne ya yo kan masallata a daidai lokacin da liman ya kabbara Sallah, inda ba tare da wata wata ba Bom din ya tarwatse. Bom na biyu kuma ya tarwatse ne a kusa da sahun da mutane sukai dan bin Sallah, haka kuma, Bom na uku ya fashe ne a cikin harabar Masallacin.

Sannan kuma, wani da abin ya faru akan idansa yace yaga wasu matasa suna harbin kan mai uwa da wabi a tsakanin masallata, abinda ya haifar da guje-guje da turmutstutsu. Mutumin ya kara da cewar naga mutum biyu dauke da bindigogi sun nufi cikin masallacin suna harbin kan mai tsautsayi, daya daga cikinsu ma naga yana dura harsasai a cikin kwansan bindigar, a cewar Umar Farouk wani matashi da abin ya faru a gabansa.

Wani ganau kuma ya kara da cewar bayaga gawarwaki da suke yashe a kasa, yaga yadda guntattakin naman mutane da jini yadda suka dinga makalewa a jikin kofofi da tagogin shiga Masallacin. Mutumin yace, duk da tsawo da ginin masallacin yake da shi, yaga naman mutane makalkale a saman masallacin ga jini face-face ko ina yana diga.

Ya Allah muna tawassuli da kyawawan ayyukanmu wadan da ka karba daga garemu Ya Allah ka dube ba dan halinmu ba ba dan mun kasa ba. Allah ka dubi raunana daga cikinmu, da kananan yara da marayu Ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da bala'i. Allah ka jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya a wannan hari. Na ruwaito daga shafin Jaafar Jaafar.

YASIR RAMADAN GWALE
28-11-2014

No comments:

Post a Comment