Saturday, November 29, 2014

Hattara Jama'a: Idan Hankali Ya Bata Hankali Ke Nemoshi


Allah madaukakin Sarki, yana gaya mana a cikin littafinsa mai tsarki AlQurani sura ta 29 aya ta 2: Cewar "Shin tsammaninku dan kunyi Imani ba zamu jarrabeku ba?" Lallai ku sani al'ummar da ta gabace ku an jarrabesu da fitina da tsoro, da firgici da tsanani da tashin hankali. Allah Subhanahu Wata'ala yana da hikima a dukkan abubuwan da ya saukarwa bayinSa na alkhairi ko sharri, shi yasa ma yace daya daga cikin rukunan Imani shi ne yadda da KADDARA mai kyau da marar kyau.

Ba shakka wasu al'amuran kan faru dan jarraba masu Imani na hakika wadan da suke maida gazawa a garesu tare da kyautatawa Allah zato. Da yawa daga cikin Annabawa, wadan da sune zababbun zababbunSa Subhanahu Wata'ala, an kashesu, kisa na wuulakanci, Allah da ya fi kowa sansu da kaunarsu, yana kallo, amma saboda ya tanadar musu da wata daukaka ta sanadiyar hanyar mutuwarsu, ya sanya mutuwarsu ta kasance a irin halin da ta zo musu.

Allah buwayi ne gagara misali, da babu wani mahaluki da ya isa tambayar dalilin da yasa abubuwansa suke faruwa bisa ikonSa. Allah masani ne ga abinda duk yake boye a garemu ne, babu wani abu da yake fakuwa gareshi Subhanahu Wata'ala.

Mun kyautata zato ga Allah madaukakin Sarki, cewa yana gani kuma yana ji, yasan masu shirya dukkan kaidi da makida akan bayinSa masu kadaita shi da Ibada. Watakila Allah ya yi nufin daukaka darajar wadan da aka kashe a irin wannan yanayi na tashin hankali a ranar gobe alkiyama.

Ya 'yan uwa masu girma. kada mu taba yanke tsammani daga samun rahama da taimakon mahaliccinmu. Shi Allah Assami'u ne kuma Albasiru ne. Babu wani abu da yake kaucewa ganinsa.

Manzon Allah SAW ya fada mana cewa karshen Duniya kisa zai yawaita, tashin hankali zai yawaita, har ta kai matsayin da wanda yake kisa bai san dalilin kisan ba, shima wanda ake kashewa bai san me ya aikata ba aka kashe shi. Munji munyi Da'a a gareka Ya Rasulullah.

Ba shakka a halin da ake ciki a yanzu. kashe kashe sun yawaita a gurare da dama. Wannan kuma duk yana faruwa ne bisa kaddarawar Ubangiji Subhanahu Wata'ala.

Dan haka, yana da kyau a lokacin da mutane ke cikin tsananin firgici da damuwa su kame harsunansu daga furta kalaman da zasu zamar musu nadama a ranar alkiyama da bazata amfanesu ba. Muyi hakuri mu maida lamuranmu ga Allah, muyi gaskiya, muji tsoron Allah gwargwadan Iko, kar muyi shirka kar mu zargi Allah akan abubuwan da suke faruwa a garemu. Mu sani cewar Allah mai ji ne kuma mai gani ne.

Allah da kansa yace kuyi Bushara ga masu hakuri da juriya a lokacin tsanani. Ba shakka abinda yake faruwa a garemu ya wuce duk yadda muke kaddarashi, mu kyautata zato ga Allah, muji tsoron Allah a maganganunmu da ayyukanmu.

Allah da kansa ya korewa kansa zalinci, yace kuma sai ya sakawa duk wanda aka zalunta ko da kuwa wanda aka zalunta baice Allah ya saka masa ba. Ya dan uwa ka sani ko daidai da magana idan ka zalinci wani Allah ba zai yafe ba matukar ba wanda aka zalinta din bane ya yafe. Muji tsoron Allah, mu kiyaye harsunanmu wajen furta kalaman da zasu zama nadama a garemu ranar da nadamar ba zata amfanawa bawa da komai ba.

A madadin Ni Yasir Gwale da Zainab Gwale muna taya al'ummar da wannan ibtila'i ya rutsa da su alhinin wannan al'amari. Wadan da suka rasu Allah ya jikansu ya gafarta musu. Allah ka sa mu cika da Imani.

YASIR RAMADAN GWALE
29-11-2014

No comments:

Post a Comment