Friday, August 9, 2013

SHEIKH (Dr.) MUHAMMAD SANI UMAR RIJIYAR LEMO: Bijimin Malamin Sunnah!!!



SHEIKH (Dr.) MUHAMMAD SANI UMAR RIJIYAR LEMO: Bijimin Malamin Sunnah!!!

Tun da nake ban taba ganin mutumin da Marigayi sheikh Jaafar yake girmamawa a gaban idonsa da bayan idonsa kamar Dr. Sani ba.Tun lokacin da Allah ya yiwa Dr. Sani dawowa gida Najeriya daga Saudiyya, Sheikh Jaafar ya gabatar da shi gabatarwa mai kyau a Masallacin Usman BIn Affan, ya yaba masa ya kuma nunawa jama'a irin kwazo da fikra da baiwa da Allah ya yiwa wannan bawan Allah, ta ilimin Hadisi da sauran Ilmai. Sannan kuma, na lura da yadda Malam Jaafar yake girmama Dr. Sani matukar girmamawa, girmamawa ta Ilmi, ban sake tsinkewa da al'amarin wannan bawan Allah ba sai ranar wata Asabar Dr. Sani yana karantar da littafin Tajridussareh a Usman Bin Affan Malam Jaafar yazo domin sauraron karatun, a hanyarsa ta shigowa masallaci ya tarar da wasu makusantan dalibansa suna hira basa sauraron karatun a zaune a kan benci, a wannan lokacin Malam ya yi musu fada, yana nuna musu irin hasarar da suke ta Ilimin da Dr. Sani yake bayarwa.

Hakika, duk wanda ya saurari karatuttukan Dr. Sani yasan dacewa Allah ya ajiye Ilimi a cikin kirjin wannan bawan Allah.  Idan yana yi maka tafsirin Al-qur'ani kai ka ce daman can Al-Qur'anin ya karanta. Allah ya yiwa Dr. Sani baiwa mai yawan gaske, wadda wasu da dama daga cikin daliban ilimi sun sani, wasu kuma sai nan gaba zasu fahimta; Allah ya huwacewa Dr. Balagar iya tsara zance, a cikin hikima da nutsuwa da kwanciyar hankali. Dr. Sani shi ne mutumin da zai daureka da Ilimi da hujjoji da nassoshi wadan da wallahi baka isa ka kunce ba. Zaka rantse da Allah Dr. Sani daman can karatun Tafseer ya yi a iyakar zamansa a Madina, irin yadda yake yin Tafsiri da Ilimi da fayyace bayani dalla-dalla; haka idan ka dauki bangaren Fiqhu sai ka dauka gaba daya rayuwarsa ilimin fiqhu ya karanta, domin duk fatawarda Dr. Sani ya bayar zai yi wahala wani ya kayar da shi a kan wannan fatawa da Ilimi sai dai da son zuciya; wata rana ina Masallacin Al-furqan wani Bawan Allah ya zowa da Dr. Bashir Aliyu Umar da fatawa a daidai lokacin da akace za'a yi hawan arfa a Makkah, sannan za'a yi Idin Layyah a Najeriya, abinda Dr. Bashir yace a lokacin shin meye fatwar Dr. Sani akan wannan matsalar! Wannan ya kara tabbatar da tumbatsar Dr. Sani a fage na Ilimi, duk da cewa Dr. Bashir shima masanin Hadisi ne da fiqhu gangaran, amma sai da ya girmama Ilimin Dr. Sani. 

Haka kuma, duk wanda ya saurarin Khdbar Dr. Sani a ranar da aka kashe Sheikh Jaafar Allah ya kai rahama gareshi, zai san cewa Allah ya baiwa wannan bawan Allah zalakar iya zance da kwantarwa da jama'a hankali a daidai lokacin da hankalinsu ya dugunzuma ya tashi, ya yi maganganu na Ilimi cikin hikima hankalin mutane ya kwanta, ba tare da samun wata hatsaniya ko husuma ba, wallahi samun wanda zai iya shawo kan mutane a wannan lokacin sai an tona. Bayan haka, duk wanda yake sauraron Khudbar Dr. Sani zai sake tsinkewa da al'amarinsa ta yadda yake Khudbah a cikin nutsuwa ga Balagar sarrafa harshen larabci kai ka ce daman can Larabci shi ne harshensa na farko. Dukkan daliban da suke karatu wajen Dr Sani hakika su shaida ne akan irin baiwa ta Ilimi da harshen larabci  da Allah ya huwacewa wannan bawan Allah.

Mutum ne mai saukin lamari, ga saukin kai, ga iya mu'amala da mutane. Zaka jin-jinawa Dr. Sani irn yadda yake da sakin fuska da walwala da jama'a musamman dalibansa, yadda yake kusantarsu da Ilimi, idan kana tattaunawa da shi har baka so wani tsaiko ya shiga tsakaninku, saboda irin yadda yake fayyace maka lamura dalla-dalla, na rayuwa da kuma na ilimi. Wani malami yace wallahi mutanan Kano da sun san waye Dr. Sani wallahi da ba za su taba yin sakaci da bibiyar majalisan karatunsa ba, domin irin yadda yake barin ilimi, abin sai wanda ya gani. Wannan abu ne bayyananne duk wadan da suke da kusanci da Dr. sun san da haka.

Sannan idan ka tabo janibin Aqidah, Ya Salam! Wallahi Dr. Sani gwani ne na gwanye a wannan fage, ya sha ya tumbatsa a fannin Aqidah. Duk wanda ya saurari karatun littafin Al-Ubudiyya zai gasgata wannan zance, wannan karatu kusan yafi tayarwa da 'yan Bidi'ah hankali a baya-bayannan, domin karyar mai karya ya iya kayarda maganganun Dr. Sani da magana ko bayani na Ilimi, wallahi mutum ne ko da me kazo ya sha gabanka, shi yasa da zaka tambayi 'yan Bid'ah gaskiyar lamari wanne Malami ne yafi tayar musu da hankali zasu tabbatar maka cewa Dr. Sani ne, domin baya ga magana ta hankali da zai rudawa rudadde tunani, sannan kuma, ga Ilimi madararsa.

Ya Allah ka tsawaita rayuwar Dr. Sani a duniya, Ya Allah ka amfanar da al'ummar Musulmi da dumbin Ilmin da ka huwacewa wannan bawa naka. Allah ka sanya Albarka a cikin Iliminsa da rayuwarsa da zurriyarsa.

Yasir Ramadan Gwale 
09-08-2013

No comments:

Post a Comment