Sunday, August 18, 2013

HASSADA: Sheikh Abdulwahab Abdallah Kano Ya Ce:


HASSADA: Sheikh Abdulwahhab Abdallah Kano Yace:

Wata rana an tambayi Sheikh Abdulwahab Abdallah dangane da HASSADA. Sai Malam ya yi bayani kamar haka: Ita Hassada wani ciwo ne wanda dukkan 'ya 'yan Adam da Hauwa suna dauke da ita. Malam ya yi bayanin cewar akwai Hassadar da zata iya kai mai yinta zuwa Al-Jannah, Malam ya buga misali da Abubakar Ibnu Abi-Kuhafa RA da Umar Bin Khattab RA, ya ce sun kasance suna yin rige rige wajen aikata ayyukan alkhairi, domin faranta ran Manzon Allah SAW da kuma neman yardar Allah, haka suka dinga rigegeniya wajen ciyar da dukiyarsu. Malam ya kara da ce, akwai daya bangaren Hassada wanda yana kai mai aiktawa zuwa ga Halaka da tashin hankali a ranar kiyama, Malam ya cigaba da cewa, daya bangaren shi ne mummunar Hassada wadda ta ke dauke da kyashi da bakinciki da mummunar niyya, ya ce, mummunar Hassada kusan a yanzu ita ta fi damun wannan al'ummar tamu, ta yadda Malamai da Sarakuna da 'yan Siyasa da Masu kudi da Dalibai da Masu yin Facebook da sauransu da dama kanci duniduniyar juna dan ganin bayan juna wajen aikata alkhairi, Malam ya cigaba da cewar hanyar da Mutum zai rage radadi da kafin Hassada a tare da shi shi ne ya dinga kokarin tunawa zuciyarsa Allah da shagaltar da ita zuciyar da zikiri da karatun al-kur'ani da tadabburi da shi. Daga karshe Malam ya kara Jaddada cewar dukkanmu muna da dauke da Hassada a zukatanmu sai dai wani yana iya danne zuciyarsa a duk lokacin da Hassadarsa ta motsa, wani kuwa baya iya jurewa har sai ya bayyana Hassadarsa a Fili, ta yadda Jama'a zasu dinga cewar wane kaza yana da Hassada. Allah ka bamu ikon danne zukatanmu.

Yasir Ramadan Gwale
18-08-2013

No comments:

Post a Comment