Thursday, October 4, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (2)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (2)

Siyasar Amerika tana da fusaka biyu, wato akwai wadda ake yi ta zahiri wadda Amerikawa suka sani kuma suke bibiyarta, wato siyasar Amerika ta cikin gida wadda ta shafi Amerikawa. Da yawan Amerikawa gidadawa ne, ta yadda basu san galibi yadda al’amura ke gudana tsakanin Amerika da sauran kasashen duniya ba. Kamar yadda a kasar Meseddoniya a kullum tarbiyyar da ake yiwa ‘yan kasar shine daga Allah sai mesedoniya, haka itama Amerika, kullum tarbiyyar da ake baiwa Amerikawa shine daga Allah sai Amerika, dan haka ne aka jahiltar da mafiya yawansu akan abinda ya shafi hakikanin alakar Amerika da sauran kasashen duniya, sannan aka dauke musu hankali ta hanyar shagaltar da su da abubuwa na more rayuwa da jin dadi.

Wannan ta sanya kullum Amerikawa basu da wani tunani sai abinda ya shafi aikin yi, jima’i wanda ya hada da morewa da jin dadi da shakatawa da kuma hutun karshen wata ko na karshen shekara. Wannan kusan sune suka damu da yawa daga Amerikawa na zahiri da muke gani, dan haka nema, duk wasu abubuwa na banza da wofi da bata lokaci sai kaga Amerikawa sun basu muhimmanci, kamar kallon karrama taurarin fina-finai na Hollywood, kallon namun daji, linkayawa a bakin kogi (beach) da sauran sharholiya, haka kuma, su Amerikawa wannan shine ya damesu. Dan haka sukeyiwa sauran kasashe musamman na musulmi wani irin kallo a matsayin na Abokan gabar Amerika, saboda abinda ake watsa musu a kafafa watsa labarai kenan.

Kamar yadda dubban mutane suka kalla a ranar larabar nan da ta gabata 3 ga watan oktoba, anyi muhawara ta fako tsakanin Obama da Romney. Wadda a wannan muhawara aka tabo abinda ya shafi siyasar Amerika ta cikin gida. Mista Jim Lehrere na kafar watsa labarai ta PBS Newshour shine ya jagoranci wannan muhawara da ta hada Obama da Romney a karon farko a bainar jama’a, wadda abinda aka tabo a wannan muhawara kusan abubuwa ne da duk wanda yake bibiyar siyasar Amerika ta zahiri ya sansu, wato batun nan mai cike da kalubale na Tsarin kiwon lafiya na Obama (health care), da batun makomar tattalin arzikin kasar Amerika anan gaba (The future of the Economy), da kasafin kudin gwamantin tarayyar Amerika (The federal Budget), da kuma batun bashin da ya dabaibaye Amerika, wanda Amerika ita ce kasar da tafi kowace kasa yawan bashi a duniya (The National Debt) domin yanzu batun da ake suna da bashin da ya kai Dala Tiriliyan goma sha shida ($16t) wanda idan ka kwatatanta da na Najeriya da Gej ya ciwo ($45b) bai wuce kudin shan-shayi ba akan na Amerika.

Haka kuma, batun da Amerikawa suka fi damu da shi shine abinda ake kira da turanci DEFICIT wato abinda Amerikawa suke kashewa yana dara abinda suke samu na albashi, da kuma batun samar da aikin yi yake taka muhimmiyar rawa, yanzu rashin aikin yi a Ameriaka yakai kashi takawas (Unemployment rate 8%), wanda kusan shine agaba wajen abinda ya damu Amerikawa. Sannan da wani batu da aka jima ana yin takaddama da shi tsakanin Obama da Romney shine na batun haraji akan hamshakan mutane da kuma talakawa (Tax cut). Kusan wadannan a takaice sune suka mamaye wannan muhawara da akayi a jihar DENVER, sannan za’a cigaba da wannan muharawa tsakanin ‘yan takarar biyu ranar 16 ga watan Oktoba a jihar New York wadda zata dora akan abubuwan da aka faro tattaunawa akansu ne, sannan kuma da muhawara ta karshe wadda za’a yi a ranar 22 ga watan nan na oktoba za’a karkare wannan muhawara a jihar Florida wadda zata maida hankali akan siyasar Amerika ta daya bangaren mai cike da sarkakiya wato siyasar Amerika da kasashen duniya da suke cewa Foriegn Plocy.

Tun bayan faduwar tsohuwar hadaddiyar tarayyar sobiya (USSR) a shekarar 1991, kasar Amerika ta samu damar shuka irin abinda ta ga dama da kuma shigewa gaba wajen yin yadda taga dama da kasashen duniya wanda ake kira UNILATERALISM, a wannan lokacin Amerika ta yi ta shimfida hanyar da zata mamaye duniya musamman a goman karshe na karni na 20 wato daga 1991 zuwa 1999. Ta shirya tsaf tare da kammala shirinta akan mamaye dimbin albarkatun manfetur da ALLAH ya huwacewa yankin GABAS TA TSAKIYA, domin bayanai sun tabbatar da cewar da akwai gangar danyan man fetur fiye da ganga Biliyan 350 a kwance a kasar IRAQI wanda ya dara man da kasar SAUDIYYA take da shi a yankin gabas ta tsakiya, domin bayanai sun tabbatar da cewar Saudiyya tana da gangar danyan mai da ta kai ganga Biliyan 267. Wannan batu na mamaye albarkatun danyan man da ke yankin gabas ta tsakiya shine ya sanya Gwamnatin Amerika karkashin George Wolter Bush ta shiga Iraqi da karfin tuwo a shekarar 2003, inda suka yaudari duniya da cewar marigayi Saddam Hussain ya mallaki makaman kare dangi. Duk kuwa da cewar hukumar dake kula da makamashin Nukiliya ta duniya IAEA karkashin Mohammed el-Baradai ta tura tawaga mai karfi karkashin Hans Blicks wanda suka je sukayi iya kar bincike basu ga komai ba.

Wannan yunkuri da Amerika take yi na mamaye dumbin arzikin gurbataccen mai da yake kwance a yankin gabas ta tsakiya shine ya sanya da yawa daga cikin kasashen gabas ta tsakiya suke cikin halin yaki kusan tun cikin karni na 20 har kawo yanzu. Kada ka bini bashin rantsuwa domin dukkan wadannan fadace-fadace da akeyi a yankin gabas ta tsakiya shirayyene daga kasar Amerika domin mamaye arzikinsu. Tun bayan da Amerika ta shiga Iraqi kuma ta hambarar da marigayi Saddam Hussein Allah ya jikansa, suka shiga watandar dan yan manfetur din da yake a kasar domin a karon farko anbaiwa katafaran kamfanin mai na Amerika Halliburtun ta hanyar reshensa mai suna KELLOG BROWN AND ROOTS kwangilar yashe tare da tsabtace rijiyoyin manfetur na Iraqi wadanda aka kona, sannan kuma aka sake baiwa kamfanin kwangilar sake samar da wasu sabbin cibiyoyin kula da danyan manfetur a Iraqi wanda ya kai kudi wajen dala biliyan 900.

Babbar alkiblar gwamnatin Bush da ta gabata shine, tana tare da ‘yan Mafiya masu mamaye duk wata harka da ta shafi makamashi da manfetur. Manuniya akan haka shine, daya daga cikin manyan kamfanonin mai na ARBUSO wanda shima Iyalan Bush wato Bush kakan George Bush suke da hannun jari mai karfi a cikinsa, haka kuma suma Iyalan Bin Laden suna da hannun jari mai gwabi a cikin wannan kamfani, wadannan hannun jari da wadannan hamshakan Iyalai suka mallaka ita ce ta haifar da wata alaka tsakaninsu mai cike da rudani, kuma mai cike da sarkakiya da dabaibayi, domin daga baya anrinka samun rashin jituwa wadda tana harsashe zuwa ga abinda ya faru na harin 11 ga watan satumba a 2001, domin jaridar The Los Angels Times ta ranar 8 ga watan fabrairun 2004 ta buga wani labari mai taken “Abubuwan da iyalan Bush suke dauka da daraja sune, yaki da dukiya da man fetur”.

Dick Cheny wanda idan bamu manta ba shine ya yiwa George Bush mataimakin shugaban kasa, shine kusan shugaban wani sashe na katafaren kamfanin nan na Halliburtun kamar yadda muka fada shahararre ne a Najeriya a harkar manfetur da dangoginsa, da kuma wasu kasashe da suka hada da na gabas ta tsakiya gaba daya da kuma kasashen Indonesia da Burma, haka kuma, tsohuwar shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amerika kuma tsohuwar mashawarciya ta fuskar tsaro, har ila yau tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Amerika lokacin gwamnatin Bush, Dr Condolizzer Rice ta taba zama shugabar katafaren kamfanin mai na Chevron a shekarun 1999 zuwa 2000, wanda shima kamfanine na daya daga cikin wadancan shaidanu na Amerika wadanda sune suke juya duk wani shugaban kasar Amerika ya so ko bai so ba.

Dan haka domin wadancan gungu na Corporate Amercan Capitalism su cigaba da mamaye arzikin manfetur dake yankin gabas ta tsakiya sunyi ta yin amfani da wasu mutane a matsayin dodorido domin su sami damar yin yadda suke so, domin gwamnatin Bush ta yi amfani da wasu mutane domin cimma waccan boyayyar manufa irinsu Iyad Alawi a mastayin sabon shugaban Iraqi tun bayan hambare marigayi Saddam Hussein Allah ya jikansa, haka harka zo kan mutane irinsu Nuri A-Maliki da Ibrahim Al-Ja’afari duk wadannan mutane daga Amerika aka daukosu aka basu mukamai domin su sharewa wadancan shaidanu hanyar mamaye danyan man da yake kwance a Iraqi.

Mu hadu a kasida ta gaba.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



No comments:

Post a Comment