Wednesday, October 10, 2012

ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (5)



ZABEN AMERIKA: Abinda Mutane Da Yawa Basu Fahimta Ba (5)

Harin 11 ga watan satumba na 2001 da aka kai tagwayen gine-gine cibiyar kasuwanci ta duniya a New York cike yake da abin mamaki da kuma tuhumce-tuhumce. Lokacin da abin zai faru annunawa duniya cewa ga wani jirgi nan da ba na yaki ba, ya taho ya tunkuyi wannan gini, a zahiri wannan shine abinda aka ringa bayyanawa mutane a kafafan watsa labai, to amma wani abu mai cike da sarkakiya shine, bayan da aka doki wannan gini babu ko alamar wannan jirgi, wanda abin mamaki ne kwarai da gaske, ace jirgi ya doki gini amma kuma babu baraguzan jirgin, wannan ya sanya shakku sosai dangane da ainihin abinda ya doki wannan gini, shin jirginne da gaske? Ko kuwa wani abune daga cikin ginin ya tarwatsa shi? Bugu da kari, bayan da aka ce jirgi ya doki ginin a hawa na can sama, sai gashi ginin dake hawa na daya da na biyu duk sun kama da wuta, zai zama abin mamaki kwarai da gaske ace irin haka ta faru, sannan kuma da abin ya faru ginin ya kama zagwanyewa yana yin kasa, duka wadannan abubuwan mamaki ne, domin ya akayi baraguzan jirgin suka bace bat sama ko kasa? Sannan ta yaya gine-ginen kasa suka kama da wuta? Sannan tayaya akayi daga dukan gini sai ya zagwanye gabaki daya? Yana da kyau mai karatu ya sani duk wannan anyi ne domin a rudi duniya da sanya shakku a tattare da mutane.

Yana da kyau mu fahimta duk wannan abin da ya faru fitina ce wadda CIA suka shirya ta, tare da manyan kiristoci domin su tayar da hankali duniya, kuma akayi amfani da rubabbun musulmi masu son abin duniya domin cimma wannan mugun nufi na matsafa ‘yan mafiya. Kuma duk sunyi karatunsu a Amerika aka yi amfani da su domin cimma wannan boyayyar manufa, daga cikin mutanan da Amerika tayi amfani da su akwai Shugaban Afghanistan na yanzu Hameed Karzai wanda Ba-Amerike ne dan Aghaninstan yana aiki a kamfanin mai a Amerika aka dauko shi domin a yi amfani da shi wajen rusa musulunci da Afghanistan, lokacin da ya zo ko birnin kabul bai gama sani, sannan kuma Amerika sunyi amfani da wani mutum Zalmey Khalil Zadeh a matsayin jakadansu a Afghanistan; a can kuma munga yadda aka yi amfani da su Nuri Al-maliki da Iyad Alawi a Iraqi.

Da aka tambayesu (Amerika) cewa ina buraguzan jirgin da ya doki wannan gini? sai suka ce ya narke ya shiga cikin karikitan ginin. Wanda kamar yadda muka sani mafi yawan hatsarin jirgi idan ya faru yakan bar sassan jikinsa, amma wannan da ya faru babu ko da kusa daga cikin sashin jirgin, kuma suka yi amfani da kafafen watsa labaransu suka sanya mutane suka yarda cewar sassan jirgin sun narke a cikin baraguzan ginin.

Kamar yadda bayanai suka nuna, shi wannan gini ba dai-dai yake da sauran gine-gine ba, domin babu kasa kokadan a cikin ginin, karafane da gilasai da alminiyo a cikin gini gabaki daya. Wanda bayan wannan abu ya faru munga kura da hayaki sun turnuke, ta ina aka samu kura da hayaki a cikin ginin da akayi da karafa da gilasai? Mazon ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam ya ja hankalin al’umma akan yadda a karshen zamani fitina zata kasance kamar kura da hayaki, kuma Alamu ne na zuwan mahadi yadda kura da hayaki zasu turnuke, daga nan kuma sai wasu fituntunu su biyo baya (Al-muttaki al-hindi, Al-burhan fi alamat al-mahdi Akhiriz zaman) Dan haka wannan hayaki da ya biyo bayan rubzawar wadannan gine-gine alama ce da take nuna zuwan fitina, wadda ya zuwa yanzu ta bayyana kowa ya ganta.

Daga cikin hikima ta injiniyoyi, ta nuna cewa wannan ginin ya tsufa yana iya faduwa, ginin yana bukatar a rushe shi a sake gina sabo. A gurare da dama a duniya akwai irin wannan hikimar ta rushe tsohon gini, sukan yi amfani da na’ura mai rushe gini, kamar yadda wannan na Pentagon ya faru, sannan a kama mutane da laifi, bayannan a sake su rana a tsaka, bayan ankama wanda ake son kamawa tun can usuli, wannan shine kusan abin da ya faru. A saboda ana zargin musulmi ne da kai wannan hari wannan shi ne zai bayar da damar mamaye Afghanistan da Iraqi da sauransu?

Domin mai karatu ya sake tabbatar da cewar wannan abu da ya faru duk shiri ne, na mafiyawan Amerika, ita wannan cibiya bayanai sun tabbatar da cewa wadannan Yahudawa barbarar yanyawa sune kusan suke mamayeta a kullum da harkoki na hada-hada, amma ranar da abin zai faru babu ko daya daga cikinsu da yaje wajen, sannan kuma anga wasu mutane daga nesa da suke ta dauko hotunan ginin ‘yan mintoci kadan kafin faruwar wannan al’amarin, abinda ya sake tabbatar min da cewa Amurkawa ne da kansu suka rusa wannan gini. Akwai wani fim mai suna THE SWORD FISH, ina fatan mai karatu ya samu dama ya kalli wannan fim din shakka babu zai tabbatar da cewar wannan abin da ya faru na rushewar wannan ginin daman can shiryayye ne. Kawai suna amfani da kafafan watsa labarai ne sun cin duniya da buguzum.

Bayan da wannan abin na 11 ga satumba ya faru, sai majalisar dokokin Amerika suka yi wata fargar jaji, inda suka kafa wata hukuma mai suna The National Commission On Terrorist Attack Upon The Us wadda aka fi sani da  (9-11 Commission) inda nan da nan Shugaba Bush ya sanya hannu dan tabbatar da wannan hukuma domin ta bayyana hakikanin abinda ya faru a wannan rana ta 11 ga satumba, inda suka dauke hankalin duniya daga ainihin inda gaskiya take zuwa sai abinda suka fadawa mutane, wannan hukuma sun saki wani rahoto na kanzon kurege akan abinda ya faru, kana iya duba wannan rariya domin ganin abinda suka ce http://www.9-11commission.gov/report/index.htm duk wannan ba komai yake nunawa ba illa kaiwa makura na makircin Amrika ga kasashen musulmi da kuma mamaye arzikinsu.

Haka kuma, marubucin littafin The Ghost Wars, mista Steve Call ya yi wasu bayanai masu sarkikiya a cikin wannan littafi da ya wallafa a shakarar 2004, inda ya yi bayanin cikakke akan kungiyar leken asiri ta CIA da kuma bayanin yadda gwamnatin Bush ta shiga Afghanistan da kuma abinda ya shafi Bin Laden. A wani fim Documentary wanda gidan talabajin na Al-jazeera suka haska acikin watan Yuli mai suna I KNEW BIN LADEN wanda suka yi isharori masu sarkakiya akan abinda ya faru, domin anyi hira da mutane na kusa da Bin Laden.

Kungiyar leken asirin Amurka ta CIA kusan ta fara aikin leken asiri a kasashen duniya kusan tun zamanin shugaban Amurka na farko wato George Warshington, amma bata zama cikakkiyar hukuma ta gwamnati ba sai zamanin da akayi yakin duniya na biyu inda ta rika bada rahotannin asiri, a lokacin ne shugaban Amurka na wancan lokacin Franklin D Rooservelt ya nada babban lauyan binrnin New York Williams J Danovan  a matsayin shugabanta na farko, wanda tsohon masanin yaki ne, kuma tsohon masanine a harkar da ta shafi binciken kwakwaf.

CIA kusan babu wata kungiya mai hadari a duniya sama da ita. Wannan kungiya kusan dukkan kasashen duniya babu inda bata aiki, sannan babbar hanyarsu ta samun bayanai sune ta hanyar amfani da jakadunsu dake kasashen duniya domin aiko musu da rahotannin yadda al’amura ke kasancewa, suna amfani da mutane da yawa a cikin kasashen su domin su ringa basu bayanai na asiri, ba tare da wadan da ake aikin da su sun san me ke faruwa ba. A shekarar 2004 shugaba Bush ya sake inganta aikin CIA inda ya sanya hannu a ranar 14 ga watan Disamba akan gyaran fuska da akayiwa dokokin CIA da suka kira Terrorism Prevension Act.

Tambayar da wata kila wasu ‘yan uwa zasu iya yi ita ce wannan abinda ya faru na 11 ga satumba shine silar mamaye Afghanistan da Iraqi ko kuwa akwai wata manufar daban? Kuma ina matsayar yunkurin kamfanin Unocal na shimfida bututun iskar gaz a Afghanistan ya tsaya? Insha ALLAH zamu zo da bayani akan haka, anan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

   

No comments:

Post a Comment