Tuesday, October 2, 2012

HAPPY BIRTH DAY: Yasir Ramadan Gwale @ Goma sha Goma Gare kan Gare!



HAPPY BIRTH DAY: Yasir Ramadan Gwale @ Goma sha Goma Gare 
kan Gare!

Assalamu Alaikum warahmatullahi Wabarakatuh. Alhamdulillah, ina mai amfani da wannan dama na yi godiya ga Allah subahanahu wata’ala da ya kawoni wannan lokaci mai cike da kalubale a rayuwata, lokacin da muke ta fadi tashin ganin ansamu rayuwa ingatacciya. Allah ta’ala ya fada acikin littafinsa mai tsarki cewa “ban halicci Dan-Adam da Al-jani ba sai dan su kadaitani da bauta” . . . Hakika manufar halittar Dukkan wani abu mai numfashi a ban kasa, shi ne ya kadaita Allah da bauta, Allah madaukakin sarki ya umarcemu  ta hanyar da’a ga dokokinSa, da kiyaye shari’ar da ya sanya mana, wanda ya aiko Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya zo mana da ita. . . . . . .  Allah abin godiya.

Kusan, ni namanta da cewa a ranar 2 ga oktoba aka haifeni, sai da wani dan uwa jiya ya aikomin da sakon inbox yana yi min tuni da cewa gobe fa ranarka ce, da naga wannan sakon da farko ban fahimce shi  ba, sai da wani ya sake aikomin da HBD sannan na fahimta. Na yi addu’ah kuma na roki Allah ya bani ikon ganin goben, Alhamdulillahi yau gamu a goben jiya.
Tunda sanyin safiyar yau Turakata(wall) ta fara daukar harami, abinda ya fara daukar hankalina shine yadda naga jama’a na ta makalamin abin FALFALI wanda yake nuna cewa lallai yau akwai DANASHA kena, wasu masu himma har ALIBIDI naga sun kawo, dukka ina godiya da farinciki a gareku.

Nasan da yawa ba suna tayani murna bane akan na kara tsufa, domin rayuwar yanzu aka fara insha Allah, sai dai abinda na lura da yawa suna min murna shekaru sun kara tafiya, girma na kara zuwa, ni kuma ina kallon cewa ina kara kusa ne zuwa ga Ajalina, domin kwanaki na  da shekarun da aka dibamin a duniya, naci wani adadi a cikinsu yazuwa yanzu.

Alhamdulillah, ina godiya kwarai da gaske, bisa soyayya da ‘yan uwa suka nunamin, sannan ina cewa AMIN da babban baki ga wadan da suka yimin addu’a ta fatan alheri da samun nasara a rayuwa. Allah ya sadamu da alherinsa duniya da lahira. Nima ina addu’ah ta fatan alheri gabaki dayanku. A madadin Yasir Ramadan Gwale (Abu-Uthman) da Ummu-Uthman muna cewa mun gode, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Haka nan bazamu manta da zazzagawa ba suma sunyi abin kwarai, sai dai bamu ga soyayyun doyoyi suna ta karakaina ba . . . . Lol
Nagode.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment