Sunday, August 26, 2012

Yadda za a shawo kan matsalar Boko Haram


Yadda za a shawo kan matsalar Boko Haram

Matsalar Boko Haram, matsala ce da kowa yake jin tsoron yin sharhi akanta. Dalili kuwa shine jama’a na ganin muddin suka yi magana akan abinda ya shafi kugiyar watakila ‘yan Boko Haram din su kai masu hari. Amma kuma a matsayinmu na ‘yan Najeriya dole ne mu yi tsokaci dangane da abubuwan da ke faruwa a kasarmu da nufin neman hanyoyin warware wadannan matsaloli tunda yake al’ummarmu ce take shiga cikin tashin hankali da shiga halin kunci da kaka naka yi da asarar rayuka da dukiyoyi. .

Boko Haram ta somo asali yau kusan shekaru 4 da suka gabata, inda ake daukar jihar Borno da Yobe dake Arewa maso gabashin Nijeriya a matsayin hedikwatar su. Ana ganin aikace-aikacen ‘yan kungiyar da cewa kokari ne na ganin an kaddamar da Shari’ar Musulunci a Nigeria kamar yadda suka ce suna ikirari, amma kuma mun san da cewa babu inda addinin musulunci ya yi umarni da tayar da hankali domin samun biyan bukata. 

Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa sun tsananta ne bayan kashe shugabansu 
Mohammed Yusuf da jami’an tsaron Nigeria suka a Yulin 2009. Tun a wancen lokacin ne ‘yan Boko Haram suka sha alwashin daukar fansa tare da yaki da duk wadanda suke ganin makiyin su ne, inda hare harensu suka faro daga Arewa maso gabas.

Yanzu haka dai abu yayi abu, kuma gumu tayi gumu, kowa ya ji a jikinsa, daga bangaren gwamnati da su kansu Boko haram din da kuma Talakawa bayin Allah wadan da basu san hawa ba basu san sauka ba, kuma galibi wadan nan hare hare daga bangaren gwamnati da kuma su ‘yan kungiyar ya fi shafa. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu. A lokacin da ya kai ziyara Amurka, Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyana cewa yana neman a tattauna da ‘yan Boko Haram din, da nufin kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu sassan kasar. Sai dai bayan kalamin na sa, sai aka ambato tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Nigeria Hafiz Ringim yana yin barazana ga ‘yan Boko Haram yana mai cewa karyar su ta kusan karewa, wanda wannan ya nuna baki biyu na gwamnatin Najeriya, shugaban kasa yana magana daban kuma sipeton ‘yan sanda shima yana magana daban, masu sharhi dai sunce kungiyar ta Boko harm ita ce tayi sanadiyar saukar da Hafiz Ringin daga mukaminsa na sipeton ‘yansand. 

Ana dai bayyana cewa wai wannan furuci ne ya tunzura ‘yan Boko Haram suka kai hari a hedikwatar ‘yan sandan Nigeria dake Abuja. Daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwa tana mai daukar alhakin harin bam din da yayi sanadiyyar hasarar rayuwa da dukiya, da ma wasu karin tayar da bama bamai a sassa da dama na Arewacin Najeriya, musamman harin 20 ga watan Janairun wannan shekara da aka kai birnin kano.

To yanzu da aka zo wannan matsaya, ta yaya za’a tunnkari matsalar Boko Haram? Gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da ‘yan kungiyar wanda daga bangaren kungiyar suka amince da Dr. Ibrahim datti Ahamed a matsayin mai shiga tsakani, sai dai daga baya tattaunawar ta watse sakamakon kwarmatawa ‘yan jarida tattaunawar da gwamnati ta ringa yi, wannan ya sa Dr. Datti ya janye daga sasantawar, kuma al’amuran kungiyar suka kara tsananta a yankin na Arewa.

Ni dai har yanzu banga wani wanda a yanzu ya lashi takobin cewa yana da wata cikakkiyar masaniya ba. Amma a matsayin mu na masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kasar mu wajibi ne mu nemi amsa ga wasu mahimamman tambayoyi. Wadannan kuwa sune kashin bayan kawo al’amarin wannan kungiya, tambayoyin sune:

Menene ya janyo matsalar Boko Haram? Su wanene ‘yan Boko Haram? Ta yaya za’a fara tattaunawa da su domin neman sulhu, tattaunawa dorarriyar ba kamar wadda ta ruguje ba? Yaya shugabannin Nijiriya zasu kasance masu tausayin jama’ar su ta yadda jama’a zasu daina yi musu kallon makiya? Yaya ‘Yan Nigeria suke san makomar kasar a gajeren lokaci da kuma a shekarun gaba ya kasance? Wadanna matakai za’a dauka na zahiri wadan da zasu tabbatar da cewa lallai da gaske ake so ake a kawo karshen wannan al’amari na Boko Haram? Sannan su wa ke da alhakin mutanan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar wannan al’amari?

Samun amsar wadan nan tambayoyi zai iya zama digon dambar kawo karshen wannan matsalata Boko Haram. Bayan mun yi wadannan sai mu hada da addu’ar neman Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar mu Nijeriya maidorewa.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment