Saturday, August 18, 2012

Bikin Sallah Ba Bikin Nuna Tsiraici Ba Ne!



Bikin Sallah Ba Bikin Nuna Tsiraici Ba Ne!

Haka Allah yake ikonsa komai yayi farko tabbas koshakka babu yana da karshe, haka abin yake ga kowane irin lamari na rayuwa, Bayan kamala azumin watan Ramadan mai dumbin falala da tarin albarka sai kuma ashiga shagulgulan bikin karamar sallah. Hakika lokacin sallah karama lokacine na farin ciki da ciye-ciye da lashe-lashe tare da ziyarar dangi da sada zumunci tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki.

Haka kuma lokacin sallah lokaci ne da ya halatta ashariance asanya sabbin tufafi da fesa turare mai kanshi da sabbin takalma da dukkan wasu al’amura da zasu nuna wal-wala da jin dadi tare da iyalai ammafa bisa koyarwar sharia. Amma abin mamaki wani yanayi da muke ciki yanzu ko kuma zamani na nuna waye da kaiwa matuka wajen nuna burgewa da cigaba. Galibi lokacin bikin sallah samari da ‘yan mata kan fita ko zaga dangi da ziyarar ‘yan uwa ko kuma zuwa gurare na shakatawa da gwangwajewa ko kuma zuwa wajen wasu bukukuwa na gargajiya kamar hawan da masu martaba sarakuna kanyi a fadojinsu koma wani abin da ba wannan ba cikin shiga ta fitina da tashin hankali.

Abin da kamfaru yayin bikin sallah shi ne galibi da yawa yara ko kuma samari da ‘yan mata kan soma lalacewa ne a ranar sallah domin kuwa alokacin bikin sallah ne zaka ga mata da dinkuna na tashin hankali duk wai domin nuna burgewa, abin takaici shi ne iyaye kan sakarwa ‘ya ‘yansu mara alokacin bikin sallah suyi duk abin da suka ga dama babu kwaba, ba tankawa. Galibi abin yafi kazanta acikin birane inda zakaga ana bajekolin futsara da rashin kunya afili, samari anan ina nufin ‘yan mata kan fita cikin ado da kwalliya mai dauke da janhankalin duk wani baligi mai hankali, ta yadda wani lokacin sai ka kasa bambance tsakanin budurwa da matar aure, da yawan ‘yan mata kan fake da zuwa gun samari da sunan karbar goron sallah inda zaka iske budurwa ta je dakin saurayi cikin shiga mai motsa sha’awa wai da sunan taje karbar yawan sallah ne wanda shi kuma idan akayi rashin sa’a mara tsoron Allah ne yafito da kudi ya nuna mata amma ya ja hankalinta sosai kafin ya bata daga nan Allah ya kiyaye kaji labarai marasa dadi.

Da yawa daga cikin ‘yan mata kanyi dafe-dafe ga samarinsu da sunan barka da shan ruwa inda zaka ga dukkansu sunsha ado da kwalliya inda galibi akanyi amfani da wannan lokaci wajen aikata badala, wata budurwar idan tayi maka wata shigar zakaga batada maraba da tsirara kuma ta fita gaban iyayanta duk da sunan murnar sallah, haka kuma abin bai tsaya ga samari ‘yan mata ba harda kana nan yara inda zaka ga an caba musu ado da kayayyaki masu ban sha’awa da kayatarwa wanda anan ma ana samun bata gari masu fakewa da daukar yarinya da sunan zasu bata goron sallah su kaita dakinsu daga karshe kaji labarin aikata badala da ita; lallai Manzon Allah ya yi gaskiya inda ya ce a karshen lokaci mata za su ringa yawo da kaya amma a tsirara suke yace kasiyatun ariyatun .

Kamar yadda nace yara da yawa na fara lalace wane alokutan da ake bukukuwan sallah domin anan ne kanan yara kan koyi zukar taba sigari samari kuma da suke dan busa taba kan cigaba zuwa busa tabar wiwi, ‘yan wiwi da shalisho kuma kan kurba ruwan  kamru uwar laifi, haka kuma a wannan lokacin akan motsa sha’awa tsakani samari da ‘yan mata wai da sunan Happy Sallah, wanda daga nanne yara kan zarce da fitsara da rashin kunya domin kuwa galibi samari da ‘yan mata kowa da dan kudi a kugunsa sukuma mata ga kwadayi da son abin duniya, zaka ga yarinya bata iskanci amma arudeta da cewa yau kawai akarshe kaga shaidan yayi rinjaye yarinya ta bada kanta.

Haka abin yake idan kaje gidajen shakatawa inda zakaga abin ma yafi muni anan gurin domin guri ne inda kowa bashi da mafadi galibi abubuwa marasa dadin ji kan faru a irin wadannan gurare na shakatawa, musamman ma idan akace akwai dan karamin kududdufi da zaka shiga kayi linkaya inda zaka iske karti mata da maza cikin ruwa wai suna wasa ko kuma yana koya mata ruwa Allah ya kiyaye.

Haka kuma lokacine da ake fitowa kallon sarki akan fito cikin ado da kasaita da nuna bajinta da iya kwalliya da yawan iyaye kanbar ‘ya ‘yansu zuwa kallon sarki amma basu san irin illar da hakan kan haifarba domin guri ne da ake cika mata da maza babu wani guri da aka ware na maza daban ko na mata daban a gwamatse ake tsayuwa irin munanan abubuwan da suke faruwa a yayin hawan sallah kunne bazai so jinsu ba.

Anan nake son nayi amfani da wannan dama nayi kira na farko ga samari musamman ‘yan mata da maza da suji tsoran Allah sudaina shiga mai bayyana tsiraici da surar jiki, kusani mutuncinku shi ne ku sanya sutura ta gari wadda zata suturce jiki gaba daya, kuma wallahi kisani ko dan iska burinsa shi ne ya auri tagari ba sai kin nuna albarkar jikin ki zai sa samari su soki ba, duk wani saurayi daya rudeki da cewa shigarki tayi kyau kisani wallahi yaudararki yake yi, Don Allah ayi shiga da ta dace da Addininmu da kuma al’adarmu kisani komabayan tunani ne kiringa kwaikwayon turawa da indiyawa.

Haka kuma ina kira ga tailoli da suji tsoron Allah aduk al’amuransu kuma su sani cewa zasu kasance ababen tuhuma ranar gobe kiyama a wajen Allah, domin  sune suke bada wannan damar ga ‘yan mata ta nuna albarkar jiki, ta hanyar yi musu dinkuna na tashin hankali.

Abu na uku shi ne Iya ye yaka mata su sani ‘ya ‘ya fa amana ne Allah ya baiwa kowane magidanci kuma zai yi masa tambaya akan yadda ya gudanar da harkar iyalansa. lallai ne asanya ido sosai akan yara aga ina suke zuwa kuma wace irin suturace ke jikinsu kuma su wane suke yawo tare dasu idan har sukayi haka wallahi sunyi abin daya dace kuma zasu kubuta har gaban Allah, dafatan za’akiyaye da wdan nan ‘yan shawarwari nawa, kuma Allah yasa ayi bikin sallah lafiya agama lafiya Allah kuma yasa ibadun da mukayi awatan Ramadan karbabbune.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment