Tuesday, August 28, 2012

Kotu a Zamfara Ta Daure Wani Matashi Shekara Daya Saboda Ya Saci Hular Dan Minista


Kotu a Zamfara Ta Daure Wani Matashi Shekara Daya Saboda Ya Saci Hular Dan Minista

Kotun shari’ar Musulunci da ke kanwuri a gusau ta Jihar Zamfara ta zartarwa da wani matashi mai suna Shehu Jiga wanda aka fi sani da Lalo daurin shekara daya a gidan kaso tare da biyan tara ta Naira 20,000 saboda kama shi da laifin Satar hular dan gidan Minista Safiyanu Bashir Yuguda, ita dai hular an kiyasta kudinta da cewar ya kai kimanin Naira 47,000.

Kamar yadda bayanai suka tabbatar, yana daga cikin al’adar danginsu Lalo sukan kai ziyarar barka da Sallah ga ‘yan uwansu da danginsu ciki kuwa harda karamin Ministan ayyuka Alh. Bashir Yuguda, wanda yake zaune a unguwar GRA da ke cikin birnin Gusau.

Kamar yadda aka shaidawa kotu cewa Lalo sananne ne a danginsu ministan, kuma yana daga cikin wadan da suka kai wannan ziyara ta Barka da Sallah zuwa gidan, sai dai bayan fitarsu ne aka lura da cewar hular Safiyanu wato dan ministan ta yi layar zana inda aka nemeta sama ko kasa. Dan haka ne Iyalan ministan suka yi yunkurin bibiyar wadan da suka kawo ziyara a wannan gida da nufin gano wanda ya dauki wannan hula. Daga baya bayanai suka nuna cewar anga wannan hula a wurin lalo inda ya tabbatar da cewar ya dauki wannan hula, kuma ya sayar da ita akan kudi Naira 15,000.

Da yake gabatar da hukunci mai shari’ah Alhaji Hadi Sani, ya ce bisa la’akari da bayanan da wanda ake zargi ya gabatar dan haka kotu bata da wani hukunci illa ta yanke masa daurin shekara daya a gidan kaso tare da biyan tara ta Naira 20,000.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment