Friday, August 31, 2012

CPC Ba Su Da Kwarin Gwiwar Cin-zaben 2015



CPC Ba Su Da Kwarin Gwiwar Cin-zaben 2015

“Ina fatan duk mutumin da zai yi min martani ya tabbata ya karanta abinda na rubuta har karshe.”

Bisa ga dukkan alamu wannan zaben na 2015 da yake tunkaromu Jam’iyyar Hamayya ta CPC bata shiryawa cin zaben da gaske ba. Don bayanai da rahotanni suna tabbatar da cewar kwarin gwiwar da CPC suke da shi, shi ne idan aka samu hadewa da jam’iyyar ACN, kusan mafiya yawancin ‘yan cpc wannan shi ne tunaninsu cewar idan an hade za’a iya cin zabe. Shakka babu Jam’iyyar ACN jam’iyya ce da ta ke da tsari musamman a inda tayi kakagida wato yankin Kudu maso Yamma ko ka ce yanki Yarabawa, hakika duk wanda ya kalli irin yadda suka mamaye wannan yanki dole ya tabbatar da cewar suna da kyakykyawan shiri, da tsari karkashin Jagorancin Shugabansu Asiwaju Bola Ahmwd Tinubu.

Karkashin Jagorancin shi wannan mutum Tinubu ACN ta karbe ragamar iko daga PDP a jihar Ogun, jihar da ke zaman mahaifa ga tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo. Wanda wannan ba karamin aiki suka yi ba na karbe ragamar ikon wannan jihar daga hannun PDP duk kuwa da cewar Obasanjo shi ne kusan ya yi uwa ya yi makarbiya a PDP amma kuma jiharsa ta gagareshi, Wani abu da zai baka mamaki da shi wannan mutum (Tinubu) wai shin kudi yake rabawa mutanan yamma suke zaban jam’iyyarsa? Ko kuwa tsabar iya zance ne da iya siyasa? hakika wannan tambaya ta jima tana yimin zillo a raina.

Alamu sun tabbatar da cewar ACN ba burinsu su kafa gwamnati a Najeriya ba. Kawai suna bukatar kasancewar yankin yarabawa ya kasance karkashin Jam’iyyar hamayya, domin a yadda suke ganin sun fi kowa wayewa da sanin ilimin boko, kuma zaben da ya gabata na 2011 ya kara nunawa cewa basu da burin kafa gwamnatin tarayya, kuma da wahala su yarda su yi tarayya da sauran ‘yan Najeriya a cikin Jam’iyya daya, tabbas yau ko da a ce ACN zata kafa Gwamnatin tarayya, lashakka yarabawa sai sun balle sun kafa jam’iyyar hamayya ta daban, domin su sumfi gwammacewa su yi ta kasancewa ‘yan Hamayya ko Adawa, kamar yadda Hausawa muke musu kirari da cewa “Yarabawa masu kwalo-kwalo” shakka babu suna da kwalo-kwalo sosai da gaske. Kamar yadda na ce, duk wanda ya kalli zaben da ya gabata, ACN ta fi mayar da hankalinta ne akan yankin Yarabawa ya ci zabe, sabanin sauran jihohin Najeriya wanda suna ganin idan tayi ruwa rijiya idan kuma bata yi ba daman haka ake zato.

Idan muka kalli yadda ACN suka yi ruwa suka yi tsaki akan shari’ar da suka kai ta jihar Osun wanda Rauf Aregbesola yake zame musu dan takara, nu nace akan wannan shari’ah kwarai da gaske har sai da hakarsu ta cimma ruwa, amma kuma idan muka kalli zaben da ya gabata na jihar Benue shedu da bayanai sun tabbatar da cewar ACN ita ce ta samu nasara a wannan jihar, amma uwar jam’iyyar ta kasa basu maida hankali akan shari’ar wannan jihar ba  kamar yadda suka yi a jihar Osun, wannan ya kara tabbatar mana da cewar ba burinsu su mamaye Najeriya ba illa yankinsu kawai.

Idan kuma, muka sake duba Arewa muka kalli Jam’iyyar CPC da Jagoranta Gen. Muhammadu Buhari, zamu ga cewar tabbas babu wani shiri a kasa na kafa gwamnati a 2015, kullum kawai surutai ake yi a kafafen yada labarai, da tunanin waccan hadewa, babu wanda zai yi shakkar cewa CPC bata da dumbin magoya baya a Arewa, tana da su na ban mamaki kuwa, amma zaka iya kiransu da cewar taron tsintsiya ne babu shara, domin mafiya yawan ‘yan Jam’iyyar nema suke jam’iyyar ta taimaka musu, ba wai su su taimakawa jam’iyyar ba. Kusan tun kafuwar CPC ta kafu da rikici da hayaniya, domin da yawan mutane sun shiga Jam’iyyar da tunanin samun makoma, wasu na ihun sai sun zama shugabanni a Jihohi wasu a kananan hukumomi wasu a mazabu, wasu kuma suna son su zama ‘yan takara ko ta halin kaka. Wannan rikicin ya hana CPC katabus a Arewa, kuma idan ba hankali aka yi ba shine zai ci gaba da mamaye Jam’iyyar har zuwa lokacin zabe mai zuwa.

Akwai dubban mutane suna nan sun dana tarko jira suke lokaci ya yi su zo domin su shiga Rigar Buhari ko suma zasu dace da al’farmarsa domin ‘yan Najeriya su sahale musu, kuma kamar yadda ake kyautata zato ga Jagoran Jam’iyyar Gen. Buhari mutumin kirki ne, haka ya kamata mutanan da ke cikin jam’iyyar su kasance, amma kusan akasin haka ya fi faruwa, domin anyi sake da karnuka da kuraye da muzurai da aladu duk sun shiga cikin jam’iyyar sunyi kaka-gida kuma suna ta yi mata kafar ungulu tare da nuna cewar su sun shigo Jam’iyyar ne saboda Buhari, wanda a zahiri halayyar su da dabi’unsu da ayyukansu sun sha bamban da na Gen. Buhari. Saboda irin wannan kwamacala da rikita-rikitar jam’iyyar CPC ta sanya ala dole, jagoran Jam’iyyar Gen. Buhari ya dauki Jam’iyyar dungurungum ya mikata ga tsohon ministan Abuja Mallam Nasiru el-Rufai ya yi mata garambawul, saboda yakini da yake da shi cewar el-Rufai kwararre ne da zai iya saita jam’iyyar ta zauna kan turba.

Mafiya yawan ‘yan Najeriya duk zatonsu shi ne cewar jam’iyyar CPC ta Gen. Buhari ce. Sai gashi mutane irin su Sule Yahaya Hamma da Rufai Hanga suna ikirarin cewar Jam’iyyar tasu ce su suka kafa ta da sunansu su suka samarmata da ofis da sunansu aka kafa wannan jam’iyya, dan haka sai wanda suke so shi zai tsaya takara a cikin jam’iyyar, wannan ya haifar da yin jabun katin shiga jam’iyyar a nan Kano inda na fito, kai rahotanni ma sun nuna cewar har jabun katin tsayawa takara aka yi tun daga matakin unguwanni har zuwa kananan hukumomi zuwa Jiha, wanda wannan batu kusan haka ya faru a jihohin Kano da Bauchi da katsina da Neja kamar yadda muka karanta a Jaridu kuma wannan ne dalilin da ya sanya uwar jam’iyyar dakatar da zaben shugabannin jam’iyyar a wadancan johohi a ranar Asabar 11 ga watan Disambar 2010.

Kamar yadda muka sani tsarin jari hujja shine linzamin siyasar wannan lokacin. Shakka babu, duk harkokin siyasa baza su yiyuba sai da kudi, to yana daga cikin abinda CPC ta rasa shine wadan da zasu taimakawa Jam’iyyar ko da badan Allah bane. Domin dai dole ka bude ofis a kusan galibin mazabu dole a samar da abinda ake fada da yaren siyasa wato kayan aiki, dole ayi abubuwa da dama wadan da suke bukatar kayan aiki, amma manyan masu kayan aiki da suke a cikin jam’iyyar irinsu Sanata Rufai Hanga da Sule Hamma duk sun shagaltu da yiwa juna kafar ungulu da shatile kafafuwan Jam’iyyar matukar ba nasu bane suka sami takara ba, haka kuma jam’iyyar ta yi wawar asarar mutane irinsu Adamu Aleiru da Gari Mallam a jihar kebbi, da Gamaliya dan takararta na Gwamna a Jihar Taraba da sauransu da dama, ita asarar magoyin baya a siyasa ko da babu abinda yake tsinanawa matsala ce, indai har zai fita bainar jama’a ya ce yabar wannan tafiyar.

A nata bangaren ita ma Jam’iyyar PDP a shirye ta ke na kare kambunta na ci-gaba da rike madafun iko. Shakka babu PDP aiki suke yi tukuru domin samun Nasarar jam’iyyar a 2015, dan haka ne ma suke ta kokarin hadiye ‘yan CPC din. A loakcin da CPC suke ta dogon turanci da yawan mitin tsakanin kaduna zuwa Legas shin a hade tsakanin ACN da CPC ko kuwa, su kuma a nasu bangaren PDP suna nan suna raba dare suna mitin akan ya zasu samu nasara a 2015, Bahaushe ya ce shirin zaune yafi na tsaye, tabbas cpc shirin tsaye suke a yayin da PDP suke shirin zune.

Idan muka kalli zaben gwamnonin da akayi a jihohi biyar wato Sokoto da Adamawa da Kogi da Bayelsa da Cross-Rivers, ya nuna cewar PDP sun shirya tsaf domin fuskantar CPC a 2015, domin da zaben sokoto ya zo kusan ‘yan jam’iyyar musamman gwamnonin Arewa tarewa suka yi a sokoton har sai da suka ga Alu ya kai labari duk kuwa da ana kallon kamar yana takun saka tsakaninsa da shugaban kasa a wannan lokacin, kuma wani abu da zai tabbatar da yunkurin PDP na sake kafa gwamnati, kusan idan mun lura ita PDP duk danta sai ya yi mata aiki, ko da kuwa ba’a zaman lumana da shi a jam’iyyar, idan muka kalli zaben Adamawa kowa yasan akwai tsamin dangantaka tsakanin Atiku Abubakar da Murtala Nyako tun kusan zaben fitar da gwanin da aka yi tsakanin Atiku da Jonathan, amma sai da Atiku ya fito ya taya Nyako yakin neman zabe domin samun nasarar Jam’iyyar PDP.

Kamar yadda Sanata Gemade ya fada a karshen wannan makon cewar tattaunawar CPC da ACN zata sake wargajewa ne, wannan magana ce mai yuwuwa. Domin mutumne ya samu fili ya gina gida yana cikin gidansa sai abokinsa ya zo ya ce ya fita daga cikin wannan gidan nasa ya zo su kafa wani sabon gidan mai kayan alatu! Kaga abu ne da kamar wuya, to kusan haka batun CPC yake da ACN, domin ni kam bantaba zaton cewa ACN zasu saki jam’iyyar da suka sha gwagwarmayar rayata a yankin kudu maso yamma ba, rana a tsaka kuma su ce sun barta sun koma CPC wannan kam da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Ko dai shi Buhari ya yarda ya koma ACN dan ya zama dantakararsu na shugaban kasa, ko kuma a dauki dogon lokaci ana ta mitin tsakanin Legas da Abuja da Kaduna har lokaci ya kure daga karshe kuma tattaunawar ta sake karyewa. A sake komawa gidan jiya.

Idan ance za’a hade shin jam’iyya biyu za’a zaba da dantakara guda daya wanda wannan ya ci karo da tsarin hukumar zabe, ko kuwa kamar yadda na fada yarabawa ne zasu bar ACN su koma CPC ko kuwa Gen. Buhari da magoya bayansa ne zasu bar CPC su koma ACN? Lallai amsar wannan tamabayar zata nuna alkiblar inda aka dosa, hakika halin da muke ciki yanzu lokaci yana kara tafiya, kuma yana kara yiwa CPC karanci. Domin dai tsarin hukumar zabe ya ce sai dan takarar ya samu kashi 25 na kuri’ar da aka kada a jihohi 23 sannan ya iya zama shugaban kasa, mu dauki yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas shakka babu CPC tana da karfi kuma zata samu fiye da wannan kashin da tsarin hukumar zabe ya yi tanadi, mu dauka ma CPC tana da goyon bayan jihohin Arewa 19 wanda ana bukatar sauran jihohi hudu kenan domin samun zabe, wanda kai tsaye wani zai ce dan jihohi hudu ai ba matsala bane, wanda gagarumin aiki ne samun wadan nan kuri’u a jihohi hudu daga kudu, domin kowa yasan cewa mafiya yawancin jihohin kudu dangwale ake yi ba zabe ba. Kuma kar mu manta a Arewa muna da jihar Plateau da Benue wanda ko ana ha-maza ana ha-mata baza su zabi Dan Arewa musulmi ba.

Kuma suma a nasu bangaren masu adawa da CPC zasu yi ta hura mata wutar rikici, su hana jam’iyyar sakat ta yadda zasu sami lagon jam’iyyar a zaben. Tabbas alamu sun nuna cewar wannan shugaban me ci wato Goodluck Jonathan yana son tsayawa wani zaben a 2015, wanda abu ne mai yuwuwa, amma PDP suna da hasashe kuma suna da zurfin tunani, domin idan suka ga cewar GEJ zai kada Jam’iyyar to shakka babu zasu fitar da dan takara daga Arewa wanda zasu marawa baya dan ganin bata bare musu ba, kamar yadda rade-radi yake bayyana cewar ana yunkurin tsayar da gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido da Gwamnan jihar Rivers Rotimi Ameachi, wanda a turance wannan shi ne Plan B na jam’iyyar PDP, domin da su rasa gara su dauko wanda suke ganin zai iya cin zabe ko da kuwa a wajen Jam’iyyar yake.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment