Saturday, August 18, 2012

Harshen Hausa Na Ci-gaba Hausawa Na Ci-baya



 Harshen Hausa Na Ci-gaba Hausawa Na Ci-baya

Hakika a wannan karni na 21 Harshen Hausa ya samu ci-gaba sosai kuma me ma’ana. Tabbas duk wanda ya kalli irin yadda al’amura ke gudana a duniyar Harshen Harshen Hausa dole ya yi murna da cewar wannan Harshe yana kara samu ta gomashi sosai, misali ada can jaridar da take fitowa da Hausa akusan kasarnan ko ma ka ce duniya gabaki daya itace Gaskiya Tafi Kwabo wadda kamfanin buga Jaridu na Arewa ke bugawa na NNN, amma kuma yanzu adadin jaridun da ake bugawa da Harshen Hausa ya karu sosai da gaske, domin yanzu muna da jaridu da suke karade kasarnan baki daya kamar Aminiya da Leadership Hausa da Rariya da suransu, haka kuma ta bangaren mujalluma ansamu ci gaba sosai domin kamar yadda duk me bibiyar lamuran mujallun Hausa ya sani ya san  da cewa Mujallar Fim kusan itace mujalla daya tilo da take fitowa da Harshen Hausa amma yanzu adadi na mujallun Hausa na karuwa cikin sauri.

Hakika wannan yake kara nuna bunkasa da buwayar Harshen Hausa a tsakanin Harsunan Najeriya. Domin ko wane Harshe yana bunkasa ne ta hanyar rubuta shi da kuma karantashi, kuma wani abun farinciki shi ne adadin masu karanta Hausa shi ma yana karuwa cikin sauri, duk wanda ya ke bibiyar inda ake hada-hadar jaridun Hausa zaiga yadda ake wawasonsu, domin irin yadda Harshen Hausa yake da sauki a wajen Bahaushe akwai wadan da sun iya rubutawa tare da karanta Hausa ba tare da sunje wata makaranta sun koya ba, sabanin sauran Harsuna wadda sai mutum ya yi da gaske sanna ya kware wajen rubutu da kuma iya karantawa.

Wani bangare kuma da yake kara nuna bunkasar Harshen Hausa shi ne irin yadda ake samun sabbin kafafen watsa labarai masu watsa shirye-shiryensu da Hausa. Sanin kowa ne cewar kusan sama da shekaru 50 ana watsa shiri da Hausa a gidan radiyoyin kasashen Turai da Amerika kamar BBC HAUSA da DW HAUSA (docabele) da VOA Hausa (Muryar Amerika), amma ya zuwa yanzu adadin gidajen radiyon da suke watsa shirinsu ga duniya da Hausa shi ma ya karu domin yanzu akwai sabbin gidajen Radiyoyi kamar RFI Hausa (faransa) da Radiyo Taiwan da Radiyo Sin da Muryar Afurka na kasar Masar da sauransu. Duk wannan yana kara nuna mana cewa lallai Haurshen Hausa yana samun bunkasa da ci-gaba.

Haka zalika inda Harshen Hausa ya yiwa sauran Harsuna zarra shi ne, bayan karantar Harshen na Hausa kuma ana iya Nazarin Al’adun Hausawa da kuma Adabi (Language, Literature and culture) sabanin sauran Harsuna da dama, misali Harshen Turanci da ba’a iya nazarin al’adun turawa da sauransu, wannan ya tabbatar da cewar Lallai Harshen Hausa yana bunkasa sosai kuma ya tserewa sa’a.

Lallai kamar yadda muka fada cewar Harshen Hausa yana bunkasa, a gefe guda kuma Hausawa na ci-baya! Domin duk wanda ya kalli ko ya nazarci yanayin Hausawa yanzu zai ga cewa suna komawa baya ta fuskar wannan Harshe. Misali wadan da ake kallo sune ‘yan Boko basu Baiwa Harshen Hausa wani muhimmanci ba, hasalima kalilanne daga cikin ‘yan Boko wadan da zaka taras suna karanta rubuce-rubucen Hausa, ko yin rubuce-rubuce da Hausa, wannan ya ke kara maida Hausawa baya domin sun nuna fifiko akan wani Harshe sama da nasu wanda ya dara wanda suke kodawa.

Shakka babu wannan maganar haka ta ke ya dan uwa mai karatu, domin idan ka shiga Jami’o’inmu sai ka tarar cewar kusan daliban Hausa ne kawai ke mu’amala da takardun Hausa, daliban da suke karanta sauran fannonin kimiyya da tattalin arziki da fasaha duka da wahala kaga suna karanta wani abu na Hausa a jami’a sun gwammace su karanta takardun turanci ko da kuwa rabin abinda suka karanta zasu fahimta.

Kuma bayanai suna kara nuna cewar hattana daliban da suke karanta Harshen Hausa a jamio’I su kansu da yawa ba suna karanta Hausar bane domin it ace zabinsu na hakika. Wasu da dama suna karanta Hausa ne domin kodai basu ci kyakykyawan sakamakon jarabawar NECO da WEAC ba da zai iya basu damar karanta wani fannin na daban ko kuma abin nan ne da ake neman takardar shaidar kammala DIGIRI dan kare yawa, cewar nima nayi digiri ba wai dan hakika tun farko sun zabi su karanta Hausa ba domin bunkasar Harshen.

Wani abu da yake kara nuna cewar Hausawa na mayar da kansu baya ta fannin Harshen Hausa shi ne cewar, ko a jami’o’I da kwalejoji zaka samu Malaman Hausa suna yin amfani da Harshen Ingilishi wajen karantar da Hausa, sai kayi mamaki malamin da yake karantar da Hausa yana ta yiwa dalibai turanci, wasu malaman sukanyi haka ne suma domin kare yawa dan kada dalibai su dauki cewar malamin da yake karantar da Hausa bai iya turanci sosai ba, su kuma dan su kare kansu daga wannan kaskanci na dalibai sai kaji malamin Hausa ya zage yana ta turanci da dalibansa a cikin aji ko a wajensa, ko kuma suma Malaman neman burga ce da rashin kishin ainihin Harshen Hausar.

Haka kuma, ga duk mai bibiyar irin muhawarorin da ake tafkawa a shafukan sada zumunta na facebook da Twitter da Googl Plus da sauransu zai ga cewa galibi ‘yan Boko basa karanta Hausa ko yin rubutu da Hausa, mafiya yawan wadan da suke yin rubutu da hausa kodai basu iya turanci ba wannan ta basu damar yin rubutu da Hausa, ko kuma sun iya turanci amma basu kware ba, domin suma su kare yawar kada a yi musu dariya sai suyi rubutunsu cikin Harshen Hausa, ko kuma ka samu wadan da suke rubutu da Hausar irin wadan da suka koyi karatu da rubutu ne a sama.

Wata matsala kuma it ace ta yadda Harshen Hausa yake gurbacewa. Shakka babu Harshen Hausa yana gurbacewa sosai ta yadda zakaji Hausawa suna Magana da Hausa amma kuma a zahirin gaskiya turanci suke yi, domin kalmomin turanci suke fassarawa kai tsaye suke Magana da su, misali Bahaushe zai gaida kai sai ya ce maka ‘ya kake’ kaga a Hausa babu gaisuwa ya kake, kai turanci ne ko wani yaren aka fassara shi kai tsaye, da sauran irin yadda ake yiwa Harshen Hausa dandantsa irin haka.

Dole ne duk mai kishin Harshen Hausa ya ji kwarain gwiwa a duk lokacin da yaga mutane sun dauki wannan Harshe na Hausa da muhimmanci. Akwai mutanen da ko wasika ka rubuta musu da Hausa bazasu karanta ba, kuma Hausawa ne, amma duk irin maganar da ka rubuta mara ma’ana da rashin tsari indai da turanci ne sai kaga ana bata lokaci ana karantawa, Haka suma wadan da suke aiki da kafafen watsa labarai na Hausa da muryoyinsu suka cika gidajen Radiyoyi suma sunfi gwammacewa su yi maka rubutu ko karatu da turanci akan abinda ya shafe su.

Sannan yana daga cikin ci-bayan Hausawa kuma ci-gaban Harshen Hausa shi ne irin yadda ahankali wadan da ba Hausawa ba ke mamaye Radiyon Murayar Amerika. Ga duk wanda yake bibiyar Muryar Amerika yasan da cewar da Sunday Dare ne kadai wanda ba Bahaushe ba yake a wannan gidan radiyo harma ya zama shugaban sashen Hausa na VOA wanda abin kunya ne a ce wanda ba Bahaushe bane yake shugabantar irin wannan gidan radiyo na sashin Hausa, yanzu haka akwai akalla mutum biyu a wannan kafa ta Murayar Amerika wadan da suke karanta labarai da Hausa kuma ba Hausawa bane, ko shakka babu wannan ci-gaba ne ga Harshen Hausa kuma ci-baya ga Hausawa, domin zakaji suna fassara turanci da Hausa gurbatacciya irin yadda suka ga dama, tun Hausawa suna jin banbarakwai har ya zama jikinsu.

Sanin kowa ne, Babban abin da fassara ke bukata shi ne lakanta sosai ta harsunan guda biyu  wanda za ka yi fassara daga gare shi da wanda za ka fassara zuwa gare shi. sannan Yana kuma da kyau ka san wani abu na al’adun wadanda ke magana da wannan harshe, domin wani lokaci sanin ma’anar kalmomin kawai ba zai ba ka cikakkar fahimtar da kake bukata ba don yin fassara. A fassara kuma, ma’ana ce ya kamata a fi baiwa muhimmanci ba kalmomin da aka yi magana da su ba. Misali, Ingilishi da Hausa sun sha bamban da juna. Don haka, ba kome ba ne mutum zai iya fassarawa kai tsaye. Mu dauki bankwanan bature a lokacin tafiya barci, “Good night”; in aka fassara kai tsaye cewa za ka yi, “Dare mai kyau” abin da zai iya sanya Bahaushe yin dariya idan ya ji. Amma in ka fassara da “Sai da safe” ko kuma “Mu kwana lafiya”, to a sannan ne Bahaushe zai fahimce ka. Kuma bature yakan amsa “Good night” ne, ko kuma “Night” kawai, abin da zai kasance shirme a Hausa in ka fassara shi da “Dare” kawai. Shi ma bature zai ji abu banbarakwai idan ka fassara masa “Ina kwana?” kai tsaye.

A ‘yan kwanakin da suka gabata angudanar da gasar OLYMPIC a birnin landan kuma ‘yan najeruya sun shiga wannan gasa. Wani abu da ya bani mamaki shi ne daga cikin wadan da aka dauka domin nishadantar da ‘yan Najeriya da wakokinsu harda wani mai suna EMMANUEL wanda yana daga cikin masu waka da Hausa, anyi hira da shi a filin taba-kidi-taba-karatu na BBC Hausa, kuma ya yi waka da hausa, abin gwanin ban dariya kuma abin haushi domin na farko Hausar yanayinta tsararo wato a gaggatse, amma kuma bunkasa Hausar yake yi. Zaka samu yanzu Bahaushe dan Boko yafi jin kunyar ya yi kuskuren turanci akan ya yi kuskuren hausa, idan mutum ya yi kuskuren turanci aka yi masa gyara sai kaga duk ya damu, amma idan Hausa ce sai kaga ya zama abin raha da dariya.

Kamar yadda sauran Harsuna suke da ka’idar rubuta su haka ita ma Hausa ta ke da irin wadan nan ka’idoji wanda yanzu da yawan Hausawa babu ruwansu da kiyaye wadannan ka’idoji, misali, ka’idojin rubutun Hausa suna taimakawa matuka wajen saukaka karatu, da kuma saukakawa me rubutawa ko kuma me neman kwarewa, dan gane abin da kai kanka kake cewa, da kuma fahimta daga shi wanda kake rubutawa ko kuma karantawa idan misali Radiyo ne. Babbabn abu shi ne sanin yadda ake harhada bakake a tada kalma.

Hakan ya hada da sanin cewa idan ka hade kalmar da ya kamata ka raba za ta bayar da wata ma’ana daban da wadda kake so. Misali, idan ka rubuta “koyaushe” a matsayin kalma guda, ma’anarta na nufin kowane lokaci, amma in ka rubuta “ko yaushe...”, ka soma da yin tambaya ke nan, wanda watakila, ke bukatar kammalawa ko amsawa. Misali, “Ko yaushe Musa zai zo?” kaga wannan tambaya ce, amma Idan aka yi kuskuren rubuta wadda ba ita ba ce, to za a faro karatun ba daidai ba, sai daga baya a gane ashe ba haka ya kamata a dauko karatun ba.

Haka batun dangantaka ko mallaka. Idan ka ce “rigarta” kana nufin wadda ta mallaki rigar kenan, amma idan ka ce “rigar ta...” to mai karatu ko kuma mai sauraronka idan Radiyo ne zai jira ya ji abin da rigar ta yi. Salon karanta su ma daban yake. Da yake ba kowa ne ya san ka’idar rubutun Hausa ba sosai, shi ya sanya rubutun wani da Hausa, wanda aka yi ba kan ka’ida ba, yakan yi ma wani wuyar karantawa.

Lallai ne mu Hausawa mu sani duk wanda ya sha inuwar gemu bai kai ya makogaro ba. Domin duk wani wanda ba Bahaushe ba ya kaiga son ya bunkasa Hausa bai kai Bahaushe ba, domin akwai al’adu wandan da duk yadda mutum ya kai ga nakaltar Harshe ba zai iya saninsu ba idan dai ba harshensa bane, kuma dole Hausawa su nuna martaba da kimar Harshen Hausa wannan shi ne zai jawowa Hausawa martaba da kima a idan duniya. Tabbas karatun turanci abu ne da Duniyar Hausawa ta ke bukatarsa sosai da gaske, amma kuma wannan ba zai zama dalilin da zai zubar da ajin Harshen Hausa ba. Bahaushe yana cewa kowa ya bargida  . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

1 comment:

  1. Masha Allah. hakikanin gaskiya, nai matukar karuwa da wannan mukala taka. kuma insha Allahu za muyi kokarin yin gyara game da yanda muke mu'amalar mu da harshen hausa da hausancin. Allah Ya taimake mu baki daya.
    Bissalam
    Naka Ahmad Aminu

    ReplyDelete