Tuesday, July 26, 2016

Zamani Riga


ZAMANI RIGA 

A lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, Gwamnati ta kuduri aniyar gina katafaren Hotel a Lamba One Ibrahim Taiwo Road, inda yanzu aka mayar makarantar Sakandare. Gwamnati tayi la'akari da yanayin Jihar Kano a matsayin ta na cibiyar Kasuwanci a Arewacin Najeriya dama Yammacin Afurka da kasashen dake kudu da Sahara, amma duk da wannan bunkasa da buwayar da Kano tayi a harkar kasuwancin saye da sayarwa, Kano din babu masauki wadatattu domin saukar baki. Wannan na daya daga dalilin da Gwamnatin Kano ta bayar a wani tsari da suka yi da aka kira Kano Economic Road Map.

Anyi wannan kuduri ne da kyakkyawar niyya dan habakar kasuwancin Kano. Kasancewar gari kamar Kano babu wani katafaren Hotel dan saukar baki irin na Alfarma. Dan haka ne aka sanya wannan damba ta samar da Five Star Hotel Lamba one Ibrahim Taiwo Road. Amma sai wannan abin ya samu mummunar fahimta daga kungiyoyin al'umma da wasu daga cikin shugabannin al'umma a jihar Kano. Inda aka dinga sukar lamirin gina wannan hotel, ana cewa Gwamnati zata gina wajen badala a kusa da cikin birnin Kano.

A haka wasu mutane suka je fadar mai martaba Sarkin Kano Marigayi Alh.  Ado Bayero suka gaya masa karya da gaskiya akan wannan yunkuri na Gwamnati. Daga ciki dalilin a da suka baiwa Sarki Allah ya jikansa, har da cewar wai za'a gina Hotel mai tsawo da baki zasu dinga zuwa suna gane sirrin Kano. Da wasu zantuka marasa tushenmu masu kama da abin dariya. A haka suka gamsar da Sarki Marigayi, dan haka ya ja Hankalin Gwamnati karkashin Malam Ibrahim Shekarau da ta jingina wannan shiri na samar da wannan hotel.

Meye Hotel? Hotel fa ba wani abu bane illa masauki. Kuma akan haka ake gina dukkan wani Hotel, masauki ne domin amfanin baki da zasu shigo su yi wani uzuri, ko kuma samar da wajen yin taruka da sauransu. Amma sai muka yiwa Hotel guguwar Fahimta. Wasu da dama da an ambaci Hotel kawai sai suce wajen fasikanci ne da aikata badala. Hotel masauki ne da mutum zai biya kudi ya kwana. Wanda duk ya kama ya aikata fasadi ko barna ba zai zama adalci a hukunta Hotel da aikin da wani yayi a cikinsa ba.

Yanzu a jiha Kamar Kano, idan ka cire Hotel din Tahir Guest Palace babu wani Hotel da yake biye da shi a daraja. Sauran duk basu wuce alallaba ba. Wannan mutum fa me Tahir ba dan kasarnan bane, amma mu kalli irin mahaukatan kudin da yake samu a Harkar Hotel. Shin yaushe ne zamu yi kishin kanmu wajen bunkasa tattalin arzikin kasarmu da jihar mu? Duk wanda yake matafiyi yasan muhimmancin Hotel, amma duk da haka muna yiwa Hotel Kallon wajen aikata fasadi da barna.

A irin haka muke yiwa komai fassara. Yana da kyau al'ummarmu mu fadada tunani, mu wanke zuciyar mu ta hanyar duba duk wani abu na zamani da yake da Maslaha a rayuwar yau da gobe. Amma kuskure ne mu dinga kafewa akan abinda ba muda cikakkiyar fahimta akansa. Allah ya sakawa Malaminmu Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da alheri, domin a lokacin da ya bayar da fatawa akan daukar hoto ba laifi bane, na san wasu da dama da suka kafa akan Hoto Haramun ne suka sauka daga kan wannan ra'ayin.

Lallai wannan gari namu mai albarka da muke fatan Allah ya tsare mana shi ya yaukaka arzikin sa,  yana bukatar Malamai masu zurfin Ilimi irinsu Dr. Sani da Dr. Bashir da zasu dinga haskawa al'umma abubuwa musamman wadan da zamani yazo da su kuma ake da gajeran tunani akansu, domin shi zamani riga ne, idan yazo dauka ake a saka ba mayar da kai baya ba. Allah ka haskaka zukatanmu wajen karbar gaskiya da kuma aiki da ita.

Yasir Ramadan Gwale 
26-07-2016

1 comment: