Thursday, August 25, 2016

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu Ya Tsage Gaskiya Akan Gwamnatin Buhari


SHIGA LAFIYA ALFANDA: MAI MARTABA SARKI MUHAMMADU SUNUSI II YA TSAGE TA

Ba shakka Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu ya tsage gaskiya mai mugun daci  game da kudurorin wannan Gwamnati kan batun tattalin arzikin Kasa. Lokaci yayi da wannan Gwamnati zata bi shawarwarin kwararru domin ceto tattalin arzikin kasarmu daga halin tangal tangal din da yake. Idan ba haka ba kuma, labarai marasa dadi ne zasu ci gaba da faruwa. Abin kam akwai ban tsoro matuka idan aka cigaba da tafiya a haka. 

Ga kadan daga abinda mai martaba Sarki yace,  "misali a lokacin da Babban Bankin kasa CBN yake sayar da Dollar akan farashin hukuma na 197 amma mutane na saya 300 a kasuwar bayan fage, idan na zauna a gidana na dauki sailula ta ina da adadin mutanan da zan kira da zasu samo min zunzurutun kudi har Dollar Miliyan Goma a farashin hukuma na 197 ni kuma na sayar a farashin kasuwar bayan fage na 300, kunga kenan zan ci kazamar riba a wannan harka, domin na samu riba sama da Naira Biliyan Daya. Haka na nuna cewar idan na samu Dollar Miliyan goma sau hudu na ci ribar sama da Naira Biliyan hudu, Bugu da kari zan yi haka ne fa ina dakina ba tare da naje ko ina ba.

To a irin wannan yanayi ne fa ake cewar an shirya tattalin arzikin Ć™asa domin ya amfani talaka. Ku gaya min ta ina Talaka yake amfana, idan ba masu kudi bane suke sake kudancewa? Ya zama tilas Gwamnati tayi abinda ya dace domin ceto tattalin arziki daga lalacewa. Idan ba haka ba kuwa, Talaka zai sake shiga matsanancin talauci masu arziki kuma na kara kudancewa." 

Wadannan sune kadan daga cikin kalaman Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi wanda Galibin jaridun yau suka wallafa. Don haka ya zama tilas Gwamnati tabi shawarar kwararru domin fitar da kasar nan daga halin da take ciki.

Allah ya taimaki Sarki ya kara masa lafiya da karfin fadar gaskiya komai dacinta. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-08-2016

1 comment: