Saturday, January 25, 2014

Zuwa Ga Sani Aminu Yunusa (Bafille)

SANI AMINU YUNUSA: Ba zan manta lokacin da Sani Aminu Yunusa (Bafille) ya yi kokarin yin fasakwaurina zuwa Kwara House daga Kaduna House ba a lokacin da muke daukin yin Candy. Ba shakka yunkurin da Bafille ya yi na daukeni zuwa Kwara House bai yiwa abokan zamana dadi ba, musamman Umar Jafar (UJ) ya fito karara ya nuna min rashin jin-dadinsa akan yunkurin daukeni daga Kaduna House da Bafille da Malan (Aliyu Hasan) suka yi. Nakan kwana a Kwara House da safe na koma Kaduna House na cigaba da harkoki, Bafille ya nuna min kauna kwarai da gaske musamman a term dinmu na karshe a KARAYE.

Mukan je Kusalla tare mu yi wanki da wanka kuma mu debo ruwa. Ba kuma zan taba mantawa da tafiyar da muka yi ni da Bafille da Malan zuwa 'Yar-Medi zuwa Marori (Kabo) a kafa ba, ba shakka, a lokacin munyi tafiyar cikin jindadi da doki, duk kuwa da angaya mana cewa tafiyar tana da nisa. A garin 'Yar-Medi muka hadu da wani mafarauci inda ya bamu wata ciyawa da ake kira sugar-daji, yace mana indai wannan bawan bishiya yana bakinku kuna taunawa ba zaku gaji ba, daga "yar Medi har kuje Marori a karamar Hukumar Kabo. Bayan da ya bamu wani bararrakakken Zabon daji muka yi kalaci da shi, muka yi masa sallama muka kama hanya, muna tafe muna tauna sugar daji har Allah ya kaimu Marori.

A lokacin da muka je wani waje domin yin tambayar gidan wasu 'yan uwansu Malan, muka ga wani masallaci muka zauna mukai alwala muka yi sallah, a wannan lokacin duk mun manta mun yar da sugar daji. Bayan da muka je wata rumfa kusa da wata karamar tasha, muka samu wata yarinya mai sayar da Alala da Dan-wake, muka sayi ina zaton na Naira Talatin muka maida Yawu, muka ga dare zai yi mana ba tare da mun gane gidan 'yan uwansu Malan ba, mukai tunanin mu koma Kabo mu hau motar da zata maida mu Karaye, amma kuma duk cikinmu babu mai ko ficika, haka nan muke sake yanke shawarar Komawa ta 'Yar-Medi a kafa! Ba shakka mun dandana kudarmu da gajiya, mun koma makaranta a wahale bayan da muka dinga yin d'ane idan munga motar da zata bi hanya (Hitch-hike), haka har muka dawo makaranta bayan dare yayi sosai. Na tabbata Sani Aminu Yunusa (Bafille) da yake Angwancewa a wannan rana ta Asabar 25-01-2014 ba zai manta da wannan lokaci ba. Ina mai amfani da wannan dama wajen taya shi murna da fatan alheri. Ina kuma jan hankalinka ka rike 'yar mutane Amana kasancewarka dan KWANKWASIYYA na san ba zaka yi wasa da kalmar AMANA ba. Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya.

Naka Yasir Ramadan Gwale
25-01-2014

No comments:

Post a Comment