Sunday, January 19, 2014

Mallam Ibrahim Shekarau: Jagora Na-gari Abin Koyi



MALLAM IBRAHIM SHEKARAU: JAGORA NA GARI ABIN KOYI

Malam Ibrahim Shekarau na daga cikin kalilan din mutane da Allah ya albarkaci 'yan Najeriya da su dan tsarkake dattin da ya gurbata koramar da ta ke gudana a Siyasar Najeriya musamman ta Arewa a wannan lokacin. Ba shakka tarbiyyar Siyasa irin wadda Malam Shekarau yake kokarin dora al'umma akai, ita ce siyasa ta gaskiya da ya kamata kafatanin al'umma su runguma domin fita daga halin kangi da wahala da radadin da ake fama da shi, da kuma maida al'umma cikin hayyacinsu, da saita mutane akan siyasar gaskiya da tsoron Allah. Al'umma, suna cikin halin kishirwar mutane nagari wadan da zasu daidaita musu sahu domin dora su akan hanya dodar wadda zata kaisu zuwa ga tudun mun-tsira, ta fidda A'i daga Rogo ta kuma raba yari da barawo, domin ceto su daga cikin mawuyacin halin da suke ciki na fatara da talauci da jahilci da kuncin tunani da koma baya.

Yana daga cikin bacin tafarkin siyasar wannan lokacin, kokarin tattabar da mugun nufi da cin-dunduniya da karya da yarfe a matsayin ginshikan samun ingatacciyar siyasa. Abinda Malam ke ta fadin tashin ganin an sauyawa al'umma tunani daga mummuna zuwa kyakykyawa, irin tsarin siyasar da su Malam Aminu Kano suka bar mana gado da wasu ke neman boye irin wannan muhimmin kayan gadon dan kada idon magada ya kai kansa, abar jama'a na ta funfum-fundum cikin mummunan tafarkin siyasa. Alhamdulillah, da Allah ya albarkaci wannan al'umma tamu da mutane irinsu Malam Ibrahim Shekarau domin saita tunanin mutane da shagaltar da su zuwaga Siyasa ingantacciya wadda idan akan yi katarin samun tsarkakkiyar niyya, na iya zamarwa mutum samun babban rabo a ranar sakamako.

A cikin shirin da ya gabatar kai-tsaye daga gidan Radiyan Tarayya Na Kaduna, ranar Lahadi 19 ga watan janairu, ya nunawa al'umma irin kwarewarsa wajen tafiya bisa tsarin siyasa na gaskiya, wadda ba ta dauke da wani mugun nufi ko bita da kulli. Malam yayi bayanai masu ratsa zukata da nuna kwarewa wajen sanin me ake nufi da siyasa ta gaskiya kamar yadda dumbin al'umma suka saurara. Ba shakka irin wadannan bayanai na tsage gaskiyar al'amura yadda suke ba tare da kari ko ragi ba, domin fitar da al'umma daga cikin rudun da wasu rudaddu suke neman jefa mutane a ciki. Irin wadannan bayanai da zasu kauda dukkan wasu shakku da jita-jita su ne irin bayanan da ya kamata managartan 'yan siyasar wannan zamanin su mayar da hankalinsu a kai.

Haka kuma, Malam Shekarau ya kunyata masu son assasa wutar gaba tsakaninsa da abokan Hamayyarsa a siyasa da son tabbatar da cewa lallai sai an tsananta gaba da kiyayya tsakaninsa da 'yan siyasa, Malam ya nuna shi dattijo ne, inda yaki baiwa wannan yunkuri gurbi a tsarin siyasarsa. Hakika, Malam Ibrahim Shekarau wata kyauta ce ta musamman da Allah ya yiwa al'ummar Najeriya da ita. Allah ya cigaba da yi masa jagora, ya kareshi da dukkan kariyarsa.

Yasir Ramadan Gwale
19-01-2014

2 comments: