Monday, January 27, 2014

Hattara Dai APC Hangen Dala Ba Shiga Birni Bane!!!

HATTARA DAI APC  HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BANE!!!

Kusan yana daya daga cikin abinda da dama suka dinga shakkar faruwarsa, shi ne cewar, wasu Jam’iyyu zasu iya dunkulewa su zama guda daya. Bayan zaben 2011 da jam’iyyun Hamayya, suka sha kashi a hannun jam’iyyar PDP mai mulki, aka shiga fadi tashin ganin hanyar da zata zamewa ‘yan hamayya mafita, domin darkake PDP a Mulkin Najeriya. Lokacin da aka fara batun cewa jam’iyyun ACN da ANPP da CPC zasu cure su dunkule su zama abu guda daya domin a kalubalanci jam’iyyar PDP mai mulki, da dama suka dinga ganin hakan ba abu bane mai yuwuwa, saboda mabanbamtan mutanen da suke cikin jam’iyyun. Amma cikin ikon Allah, wannan al’amari ya tabbata gaskiya, inda duk ‘yan wadancan jam’iyyu suka hakura da bambance bambancen da ke tsakaninsu suka dunkule kowa ya yarda jam’iyyarsa ta saraya domin samar da jam’iyyar Hamayya/Adawa guda daya wadda zata iya kalubanatar PDP a babban zaben badi mai zuwa.

Bayan da aka yi nasarar yin waccan Hadaka da ta samar da Jam’iyyar APC, wacce ake cewa irinta ce karo na farko a tarihin siyasar Najeriya, al’ummar Najeriya ciki da waje suka dinga nuna farin cikinsu da nuna goyon bayansu domin a zahiri ta bayyana cewa da gaske jam’iyyun Hamayya suke don kalubalantar PDP a zaben 2015. Shugabannin APC na riko da kuma jagororin wannan Hadaka sun bazama jihohi inda suka dinga kaiwa ‘yan siyasa da dama caffa domin tafiya tare dan a kauda PDP daga kan karagar Mulkin Najeriya. Wannan ta sanya sabuwar Jam’iyyar APC ta farauci wasu daga cikin Gwamnonin PDP da suke da matsala da jam’iyyarsu ta PDP, aka kuma yi dacen wafto wasu daga cikin ‘ya ‘yan PDP din da suke tayar da kayar baya a cikin jam’iyyar tasu.

Abinda tun farko APC suka kasa yi, ko kuma suka yi sake da shin shi ne batun hada kawunan Sabbin ‘ya ‘yan Jam’iyyar da ko dai suke da ra’ayoyi mabanbamta ko kuma suke tsananin Hamayya da juna. Tunda har wadannan jam’iyyu suka iya yarda su sarayar da Jam’iyyunsu su samar da APC babu shakka abu ne mai sauki su iya zama a kan tebur domin su warware matsalolinsu musamman da wadan da ake ganin akwai Hamayya tsakaninsu, wannan wani janibi ne mai muhimmanci da APC ya kamata ta baiwa kulawa ta musamman tun fil azal, amma sai aka yi shakulatun bangaro da al’amarin har Baraka ta bayyana kamar wata daren sha biyar.

Tun ran-gini tun ran-zane, inji Bahaushe, a lokacin da APC suka fara zawarcin Gwamnonin PDP, suna sane da cewar akwai hamayya tsakanin wadan da aka kafa APC da su, da kuma, wadan da ake kokarin yin zawarci. Sanin kowa ne a Kano akwai Hamayya tsakanin Gwamna Rabiu Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau; a Sokoto akwai Hamayya tsakanin Gwamna Aliyu Magatakarda Wammako da tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa; da kuma Adamawa inda Gen. Buba Marwa ke Hamayya da Gwamna Murtala Nyakko. Duk jagororin APC suna da masaniyar wannan hamayyar, wanda abinda ya kamata a yi tun farko shi ne a san hanyoyin da za’a bi wajen dinke wannan barakar kafin zabarin wadannan Gwamnoni. Amma sai idon jagororin APC ya rufe, inda sun san a jihohin da na fada a sama Akwai Bafarawa da Shekarau da Marwa, amma aka zabi wasu aka kaiwa gwamnonin wadannan jihohi ziyarar zawarci ba tare da ko da sanar da wadannan mutane ba, babu shakka, a Magana ta gaskiya, dole ko waye zaiji babu dadi ace jam’iyyar da kuka bata lokaci  wajen kafawa to zo har jiharka wajen zabarin mutane ba tare da wani ya sanar da kai ba! Abin akwai damuwa da rashin jin dadi, wannan ko da wanda za’a zawarta ba sa hamayya das hi.

Bayan da duk aka yi abinda aka yi, daga baya APC suka fahimci cewar sunyi kuskure, har suka kafa kwamitin da zai zagaya jihohin Kano, Sokoto da Adamawa domin baiwa Malam Shekarau, Bafarawa da Buba Marwa hakuri kan abinda aka yi musu na rashin sanar da su zuwan tawagar APC jihohinsu. Babu shakka, wannan abu ne mai kyau da APC ta yi. Amma kuma daga hakan ba’a yi komai ba, sai aka tsaya a wajen, maimakon a yi amfani da wannan damar wajen tuntubar wadannan mutane wajen ganin yadda zasu iya zama inuwa daya da abokan hamayyarsu a siyasa cikin jam’iyya daya, sai aka yi biris da zancen. Gwamnonin Kano da Sokoto da Adamawa suka ayyana komawa APC ba tare da APC din tana da wani shiri mai karfi a kasa ba wajen ganin ta sasanta ‘ya ‘yanta masu hamayya da juna.

Haka nan, wadannan Gwamnoni suka shigo APC ta sama ba tare da yin wani shiri na karbarsu ba a jihohinsu, da kuma kokarin zaunar da su da abokan hamayyarsu a sasanta su ba, kai kace daman da su aka kafa APC din. Aka yi ta rade-radi game da shigowar wadannan gwamnoni, shugabancin uwar jam’iyyar APC yana ji bai ce ko “bihim” ba akan lamarin, tun kan ya kazance. Aka yi ta turka-turka akan waye ya kamata ya zama jagora ko ba waye ba a wadannan jihohi amma shugabancin jam’iyya yaki yin katabus akai. Har aka zo kan wani mataki da ka iya zamarwa APC mai matukar hadarin gaske a 2015.

A makon da ya gabata Bafarawa wanda daya ne daga cikin jiga-jigan ANPP da suka sarayar da jam’iyyarsu ta ANPP wajen ganin kafuwar APC ya bayyana ficewarsa, amma maimakon a nuna rashin jindadi da damuwa, sai ya zama abin murna ga wasu, ana cewar Allah ya raka taki gona. Da dama suna fadin Da Bafarawa da Shekarau da Buba Marwa ko da su ko babu su APC zata iya cin zabe a jihohin Kano, Sokoto da Adamawa, wannan kam gaskiya ne. Ko babu wadannan Mutane APC tana da yakinin cin zaben shugaban kasa a jihohin, amma abinda akan manta shi ne, tun da aka fara wannan sabani jam’iyya mai Mulki PDP tayi amfani da wannan Baraka wajen kaiwa Malam Shekarau da Bafarawa da Marwa bara, inda take neman su shigo jam’iyyar dan basu damar da aka hanasu a APC. Abinda da dama daga cikin ‘yan APC suke ganin tafi nono fari idan Shekarau da Bafarawa da Marwa har ma da Bolgore suka koma PDP.

Yana da kyau mu sani, ita APC, it ace jam’iyyar Hamayya/Adawa burinta, fatanta, begenta shi ne ta ci zabe. Dan haka duk wata dama da zata iya kawo nakasu daga samun Nasarar APC ya kamata kar a bata kofa ko wace iri ba. Haka kuma, yana da kyau mu sani cewa, ita PDP ba yanzu suka saba cin zabe ba, dan haka duk wasu dabaru na sarari da na boye sun jima da tanadin kayansu. Ita PDP ba sai ta cinye Kano da Sokoto ko Adamawa kanan ta ci zabe ba, kawai abinda suke da bukata shi ne kashi ashirin da biyar (25%) da hukumar zabe ta ce sai jam’iyyar da ta samu a jihohi 23 sannan zata iya cin zaben shugaban kasa. Masu cewar Ko da Shekarau, Bafarawa, Marwa ko babu su APC zata iya cin jihohinsu, amma kuma sun manta cewar wadannan mutane zasu iya kawowa PDP 25% a jihohinsu! Anan matsalar take, domin a 2011 lokacin da ake Murna cewa Buhari ya samu kuri’u Miliyan Biyu a Kano an manta cewa PDP ta samu kashi 25 a kanon. To amma saboda doki da hangen dala, sai wasu suke ganin cewar ficewar Bafarawa da Shekarau da Marwa alheri ce ga APC.

Babu shakka idan APC ta cigaba da kame hannu, ‘ya ‘yanta na halak malak suna zurarewa ba tare da ta rufe bakin daurin ba, to tabbas a zaben 2015 za su sha mamaki. Domin mai gishiri ai baya wasan shiga ruwa da mai goro. Su PDP da yake da gaske suke son tabbata akan Dimokaradiyya, lokacin da Atiku Abubakar da Marigayi Abubakar Rimi suka yi zuciya suka bar jam’iyyar suna zaginta tare da yi mata jafa’I, uwar jam’iyyar bata barsu haka ba, sai da ta kafa kwamati akai ta rarrashinsu har suka hakura suka dawo domin sun tabbatar tafiya da Baraka ba zai zamar musu alheri wajen cin zabe ba. Yana da kyau mu waiwayi baya mu kalli yadda al’amura suka faro da yadda suka karke.

Amma saboda saurin mantuwa da rashin yin karatun ta nutsu sai wasu ke fatan da Shekarau da Bafarawa da Marwa har addu’ah ake musu Allah ya raka taki gona, shin masu addu’ar basa tunanin Allah ya amshi addu’arsu Taki ya isa gona lafiya, ayi shuka tayi yabanya har aci amfaninta? Sannan kuma, tsakanin APC da PDP wa yafi bukatar cin zaben shugaban kasa ido rufe? Na tabbata mai karatu zai yarda da ni cewa APC su ke da bukatar cin zabe ido rufe, shin ya dace su yarda da duk wata Baraka da ka iya nakasta samun nasararsu?

Ni a fahimtata, yanzu ta bayyana cewa babu wata jam’iyya mai tsarki da ta ke da mutanan kirki dari bisa dari, dan haka duk inda mutum ya tsinci kansa yayi kokarin kawo gyara da kyakykyawar niyya kuma gwargwadon ikonsa. Allah yana bamu ladan aikin da muka yi dominsa gwargwadon yadda muka kyautata niyya. Dan haka, yana da kyau APC su sani hangen dala daga nesa ba shi ke nuna an shigo biirni ba, kuma mai ma’di ai shi ke talla . . .!

Yasir Ramadan Gwale
27-01-2014

No comments:

Post a Comment