Sunday, November 27, 2011

Zuwa ga Marigayi Mallam Umaru Musa Yar’Adua

Ya mai girma tsohon shugaban kasar Najeriya ina yi maka sallama irinta addinin musulunci Assalamu Alaikum. Amincin Allah ya tabbata a gareka ina mai addu’a a gare ka da kuma fatan samun rahamar Allah da kuma addu’ar Allah ya gafarta maka zunubanka. Amatsayin ka na dan Adam kuma wanda ya rayu da mu a wannan duniyar kafin cikar wa’adinka ko shakka babu kai maikuskure ne kamar kowane bil’adama, kuma a halin da ka ke ciki ya shugaba baka bukatar wani abu daga garemu face addu’a da kuma fatan samun rahama daga madaukakin sarki wanda mulkinsa baya karewa haka kuma rahamarsa bata takaita ga wasu kawai ba shi ne da kansa yace ku rokeni zan amsa muku subuhanahu wata ala! tsarki ya tabbatar masa wanda ya dauke ka a dai dai lokacin da Najeriya da ‘yan Najeriya ke bukatarka.

Ya shugaba Mallam Umaru Yar’adua ko shakka babu a matsayina na dan Najeriya kuma mai kishin ta! kuma kasar da ka taba zama shugabanta lokacin da ka ke raye ko shakka babu ka tafi da burace-burace masu yawa, wanda masu magana suna cewa kana ta ka Allah ma yana tasa sai dai ta Allah ita ce tabbatacciya. Tabbas mun san katafi da burin ganin cewar rayuwar dan Najeriya ta kyautatu al’amura sun koma yadda suke; musamman wadan nan kudurori naka guda bakwai da ka sanya a gaba wadan da mukai ta daukin ganin ka cika wadan nan alkawura da ka dauka, kaico mai aukuwa ta kasance a gareka batare da Allah ya cika maka burinka ba. Ina mai yimaka albishir da cewa insha Allahu wadan nan kudurori naka zasu cika ko ba dade ko bajima kuma Allah yaga zuciyarka kuma ina sa ran zaicika maka ladanka.

Ya shugaba tun lokacin da ka kwanta rashin lafiya al’ummar wannan kasa sun tausaya maka kwarai da gaske birni da kauye kowa addu’a yake ta fatan alheri agareka da kuma nema maka sauki agurin Allah agaskiya ban taba ganin mutumin da ‘yan Najeriya suka tausaya masa ba kamar kai ya shugaba, tun kana kasar saudiyya muna ta yi maka addu’a har aka dawo da kai cikin wani hali mai cike da rudani ya shugaba lokacin da na samu labarin saukar ka afilin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe shida na safe a wata kafar watsa labari ni kadai ina kwance sai da na mike na yiwa Allah godiya! gaskiya nayi farin ciki sosai a wannan safiya, kwatsam daga baya sai labarin ya sauya cewa baka murmure ba. Amma lokacin da muka samu labarin wasu malaman addini da shuaban majalisar koli ta tabbatar da shari’a a najeriya Dacta Ibrahim Datti Ahmed sun kai maka ziyara munji sanyi a ranmu cewa kana nan kana samun sauki wannan ko shakka babu ya sa ran duk wani mai kaunarka yayi dadi.

Ranar 5 ga watan mayu da misalin karfe 6 da minti 3 na kunna radiyan Muryar Amurka abin da na faraji shi ne muryarka abinda ya fara zuwa raina shi ne cewa Shugaba ya samu sauki kawai sai najin an saka wakar mutuwa mai bantsoro daga nan hankalina ya tashi domin nasan ta Allah ta kasance agareka, tun a wannan lokaci hankalin ‘yan Najeriya ya tashi domin kuwa ka tafi alokacin da muke begen ganin irin halin da ka ke ciki ya kyautatu, domin kuwa jita-jita ta yadu sosai game da kai, kan kace kwabo jihar ka ta haihuwa Katsina ta fara daukar harami domin ‘yan uwa da abokan arziki da dangi da sauran ‘yan Najeriya suna ta tururuwa domin halartar jana’izarka Allahu Akbar yadda ka tafi haka dukkaninmu zamu taho kuma kasani wallahi kai da ka rigamu bakayi gaggawa ba kuma mu da muke raye ba mu yi jinkiri ba, kamar yadda Mamman shata ya fada a wata waka da ya yiwa chiroman Gwambe.

Ya shugaba bayan tafiyarka abubuwa da dama sun auku a kasarmu Najeriya abu na farko da aka farayi shi ne nada mataimakinka wanda kafin rantsar dashi cikakken shugaba ya rike mukamin mukaddashi, daga nan kuma abubuwa duk suka sauya domin kuwa ‘yan Arewa da yawa sukai ta rugawa Abuja suna kamun kafar neman kujerar mataimakin shugaban kasa, a karshe dai Allah ya tabbatar da ita akan Gwamnan jihar kaduna Namadi Sambo, bayan nan shugaban da ya gajeka yace zai dora daga inda katsaya, domin yadauki alkawarin cigaba da muhimman kudurorin nan naka guda bakwai. Sai dai yanzu babu su babu dalilinsu Bayan haka abin da kayi ta kokarin ganin yasamu shi ne wutar lantarki wadda sabon shugaba yace dakansa zai gyara.

Bayan haka kayi alkawarin aiwatar da karbabbe kuma sahihin zabe wanda nasan da kana raye ka aiwatar da wannan zabe akace baka ciba tabbas nasan da zaka bada mamaki ta hanyar mika mulki ga wanda ya yi nasara, shugaba yaje Washinton a kasar Amurka da Nice a kasar Faransa kuma duk ya yi alkawarin shirya karbabben zabe, inda ya dauko mutumin da kaso 90 na mutanan Najeriya suka kyautata masa zaton zai yi abin kirki a wannan hukuma ta zabe wato INEC mutumin kuwa shi ne farfesa Attahiru Jega wanda kafin dauko shi shi ne mataimakin shugaban jami’ar Bayero da ke Kano. Kuma sabon shugaban ya yi alkawarin cewa bazai bar duk wani mutum da yake dauke da katin wata jam’iyya ba yakasance a cikin wannan hukuma ta zabe. Sai dai anyi zabe kuma wanda yaci yaci wanda ya fadi ya fadi shin ya cika alkawari ko bai cika ba wannan ‘yan Najeriya su ne sheda

Ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa. Yanzu dai duk abin da aka shirya ya kasance. Don shugaban kasa na yanzu wanda tsohon mataimakin ka ne ya tsaya takara kuma wannan hukuma ta zabe karkashin jagorancin Jega ta tabbatar da cewa shi mutanan Najeriya kusan Miliyan 23 suka zaba. Sai dai babban abokin hamayyarsa tsohon shugaban kasa Gen. Muhammad Buhari da jam’iyyarsa ta CPC sun garzaya kotu da nufin kalubalantar wannan zabe; kamar yadda shi Gen. Buhari ya yi a baya na kalubalantar zabenka a karkashin tsohuwar jam’iyyarsa ta ANPP wadda tsohon Gwmanan Jihar Kano Mallam Ibarhim Shekarau ya yiwa takara.

Ya mai girma marigayi, kamar yadda ta faru a lokacin ka kotun sauraran kararrakin Zabe ta tabbatar da shugaba mai ci wato Goodluck Jonathan a matsayin wanda ya lashe wannan zabe. Kamar yadda ta faru a agareka. Ya maigirma tsohon Shugaban kasa na so nayi babbar mantuwa ta rashin shida maka abin da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasa.

Kusan bada sakamakon zabe ke da wuya sai rikici ya barke a kusan daukacin jihohin Arewa inda matasa suka fusata suka yita kone-kone musamman Gidajen sarakuna wadan da ake zarginsu da karbar toshiyar baki da kuma gidajen fitattun ‘yan siyasa kamar Alh. Bashir Tofa da Rt. Hon. Ghali Na’abba a kano haka abin yake a kaduna kai hattana tsohuwar ministarka ta ilimi Haj. Aishatu Dukku wadda ake kallo a matsayin wadan da suka raba gari da shugaba mai ci itama bata tsira ba daga wannan kone-kone, antafka asarar dukiya mai dimbin yawa. Bayan da Dantakarar jam’iyyar CPC Gen. Buhari ya barranta daga masu wannan kone-kone inda yace hattana shima an kona masa motoci abin ya lafa.

Daga nan kuma aka shiga batun hada-hadar rantsar da sabon shugaban kasa. Wanda wani abu mara dadin ji ya faru a yayin wannan hidima, ya maigirma tsohon shugaban kasa juma’ar da ta ta zo kafin ranar lahadin da a itane za a rantsar da shugaban kasa an tsaurara matakan tsaro a kusan ko wane gefe na babban birni tarayya Abuja, inda Musulmi da zasu tafi Babban masallacin kasa sallar juma’a aka tsananta musu ta hanyar sa su daga hannu sama da yin doguwar tafiya a kasa kafin sukai ga masallacin, ya mai girma shugaba lokacin da aka rantsar da kai bamu fuskanci wannan matsin lamba ba. Wannan ta sa limamin da ke fassara huduba da turanci Uztaz Abubakar Siddeeq ya nuna rashin jin dadin abin da akayiwa musulmi inda yace harda jakadun kasashen duniya sun fuskanci wannan wulakanci, wannan ta kai ga dakatar dashi akan wannan aiki da ba biyansa albashi ake yi ba.

Ya mai girma marigayi Umaru YarAdua, bayan rantsar da shugaban kasa ya sauya dukkan al’amura ba yadda aka tsammata ba. Sannan ya kafa kwamiti karkashin dattijo wato Sheikh Ahmad Lemu kan ya binciki musabbabin wannan rikici da ya biyo bayan zaben shugaban kasa, kwamitinsa ya yi bincike na gaskiya da adalci kamar yadda muka zata kuma ya mika rahotonsa! Rahoton ya kunshi muhimman abubuwa wadan da idan har ambisu za a samu kyautatuwar al’amura, wanda kuma suka tsoratar akan cewa matukar aka bi son zuciya aka kaucewa wannan rahoto kasar nan na iya fadawa wani mawuyacin hali da kasashen larabawa suke ciki a yanzu.

Bayan nan kuma, wasu muhimman al’amura da suka shafi tsaro sunyi ta aukuwa, kamar rikicin Jos wanda musulmi suka ji haushinka a lokacin da kake raye inda kaje ta’aziyar rasuwar Gbom Gom Jos da Victor Pam, amma ko ka tsaya ka jajan ta musu. Wannan rikici dai har yanzu da nake rubata maka wannan kasida yana nan kuma yana cigaba, shugaban kasa da gwamnan jihar plateau sun kasa shawo kan wannan al’amari, kisan rai kusan yanzu har ya zama ba labari ba a birinin Jos da sauran sassan jihar plateau.

Haka kuma ya shugaba, Rikicin nan na Boko Haram da ka bada umarnin gamawa da su kafin tafiyarka ta karshe zuwa neman magani saudiyya wanda shi ne ya kai ga halaka shugaban kungiyar mai suna Mallam Muhammad Yusuf, wannan rikici shima ya dauki sabon salo inda akayi ta tayar da bama bamai a garin Maiduguri abin ya wuce dukkan lissafinmu, har sai da ta kai ga rasa ran Dantakarar gwamna na jam’iyyar ANPP Alh. Madu fannami Gubio da wasu fitattun mutane da masu unguwanni abirnin na Maiduguri, babban wanda ya faru kuma ya girgiza mu shi ne wanda bom ya tarwatse a damaturu ta Jihar Yobe wanda rahoton ‘yan sanda ya nuna kusan mutane 100 ne suka halaka tare da daruruwa da suka ji raunuka.

Sannan kafin wannan na damaturu ya faru. Bom ya tarwatse a hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Abuja, ‘yan awanni bayan shugaban ‘yan sanda na yanzu wato Hafizu Ringim ya yi ikirarin cewar kwanakin ‘yan Boko Haram kididdigaggu ne. Sannan an sake samun wani Bom da ya fashe a ginin majalisar dinkin duniya da ke Birnin tarayya Abuja, duka wadan nan hare-hare kungiyar Boko haram ta dauki alhakin kaisu.

Sannan, gwamati ta nada kwamiti karkashin Giltimari na ya duba yadda za’a shawo kan al’amarin ‘ya ‘yan kungiyar ta Boko Haram sai dai wannan ma bai biya bukata ba domin kuwa ‘yan kungiyar sun zargi shi Giltimari da marawa tsohon gwamna Ali Shariff baya, yanzu dai shima giltimari ya mika rahoton sa zuwa fadar shugaban kasa.

Da yawan mutane suna ganin gwamnatin tarayya ta bayar da a huwa ga wadan nan matasa; kamar yadda ka cika kudurinka na farko wato samar da cikakken tsaro a yankin neja dalta ta hanyar yiwa wadan nan tsageru ahuwa da mayarda su makaranta da koya masu sana’o’i da basu jari, wanda wannan shugaban ya cigaba da wannan tsari ta hanyar kashe masu kudi makudai tare kuma da turasu kasashen Turai da Amurka da Malaysia da Afurka ta kudu wai duk da sunan yi musu ahuwa, wanda wannan shi ne abin da ke neman motsa ko kuma iza wutar kabilanci a zukatan ‘yan Najeriya inda da yawanmu ‘yan Arewa muke ganin bai kamata a fifita wadan nan tsageru da wannan ta gomashi ba abar miliyoyin matasa a yankin Arewa suna watan gaririya akan tituna, da yawa suna ganin irin wannan shi yake haifar da kungiyoyi irinsu Boko Haram da darul Islam da makamantansu a yankin Arewa.

Ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa, hukumar nan da ka tursasawa shugabanta na da sauka tare da mayar da shi makaranta a Kuru tare da kokarin kamashi da laifin da bai jiba bai gani ba wato Mallam Nuhu Ribadu wanda shi ma ya yi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a zaben da ya gabata, ka nada Uwargida Farida Waziri a matsayin wadda zata jagoranci wannan hukuma wanda ya gajeka shima ya barta don taci gaba da aiki a wannan hukuma ta EFCC, amma sai dai mafi yawan ‘yan Najeriya sun zarge ta da gazawa wajen aikinta bata iya kai banten ta ba kamar yadda magabacin ta Mallam Ribadu ya kai ta hanyar kame tare da kwato dukiyar da azzaluman shugabanni suka diba alokacin da suke rike da madafan iko. Yanzu dai itama madam Waziri ta kama gabanta a wanna hukuma kamar yadda shugaban kasa ya umarci kakakinsa Dr. Rueben Abbati ya bada sanarwar sauke ta daga shugabancin wannan hukuma da umarta Mallam Ibrahim Lamorde a matsayin wanda zai rike hukumar nan da wani lokaci .

Abubuwa da yawa sun faru, ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa tun bayan barinka wannan duniyar Musamman ma a inda kafi sani wato Najeriya, bazai yiwu gareni na baiyana maka dalla dallar abin da ya faru ba duk da nasan wannan sakona ba zai sameka ba, amma ina fata ya zama izna. Kamar yadda hausawa suke cewa “kukan kurciya jawabine amma......”

Daga karshe ya mai girma marigayi tsohon shugaban kasa, ina yi maka addu’a ta fatan alheri da samun rahama agurin mahaliccinka da kuma fatan can inda ka ke tafi nan. Allah ya tabbatar mana da alheri a kasarmu Najeriya ya azurtamu da shugabanni masu tsoron Allah.


No comments:

Post a Comment