Sunday, November 27, 2011

Sufurin Jirgin kasa a Najeriya: jiya ba Yau ba!

Sufurin Jirgin kasa a Najeriya: jiya ba Yau ba!

Jirgin kasa kusan shi ne abin sufuri da yafi kowace hanya ta sufuri sauki da kuma tabbas. Jirgin kasa shi ne abinda da zaka hau ba tare da fargaba ba ko zullumi, baka tunanin hadari ko ‘yan fashi ko ‘yan kwanta-kwanta. Sannan zaka hau jirgin kasa cikin kudi kalilan. Jirgin kasa ana yi masa kirari da dama, kamar yadda shugaban Amurka ya taba kamanta gwamnatin Amurka da cewa kamar jirgin kasa ta ke ba shida ikon sauya akalar jirgin sai dai kawai ya kara gudunsa ko ya rage gudunsa.

Jirgin kasa ya fara zurga zuraga ne a Najeriya ranar 4 ga watan maris din shekarar 1901, inda yake safara daga Legas zuwa Ibadan cikin sauki da kwan ciyar hankali a wancan lokaci ga kuma arha, jirginsa ka du mutum ka dau kayansa kamar yadda masu Magana suke cewa. Daga nan likkafa taci gaba inda a shekarar 1911 aka sauya jirgin kasa a Najeriya daga mai aiki da gawayi zuwa mai aiki da man dizal sannan kuma aka kara zangon da jirgin zai ci har zuwa Arewacin Najeriya inda yake cin zangon kilomita kusan 45,000 acikin kasar nan.

Duk wannan suna karkashin hukumar sufurin jiragen kasa ta wancan lokacin inda take da jiragen kasa kimanin guda 50 wadanda ke safara gabad da yamma kudu da Arewa. Jirgin kasa kan tashi tundaka ikko ta jihar Legas har zuwa Nguru a jihar Borno ta wancan lokacin inda daga nan yakan ratsa har tsohuwar rusasshiyar jihar Gongola ta wancan lokacin, gashi da manya-manyan tashoshi a kudu da arewacin kasar nan.

Kusan babbar moriyar da akaci ta jirgin kasa a wancan lokacin itace safarar kaya da yake daga kudu zuwa Arewa inda yake Daukar gyada da fatu da kiraga da hatsi da kayan gwari wato tattasai da albasa da attarugu ya kai kudancin kasarnan, sannan ya dauko kayan Marmari kamar ayaba da lemo da kwarar manja da da tufafi ya kawo kasar Arewa, jama’a na amfani dashi cikin kwanciyar hankali. Kusan duk lokacin da jirgi ke zuwa daga kudu zuwa Arewa idan ya yada zango a zariya jama’a kan samu Alheri sosai ta fannoni da daman gaske, haka har ya karaso kano inda nan ma zakatar wata kasuwa ce ta musamman a duk lokacin da akace maka jirgin kasa yazo jama’a na ta hada-hada abin gwanin ban sha’awa. Haka nan jirgin zai tashi har ya isa jogana inda nan ma yakan yada zango duk dai jama’a na ta kaiwa da kawowa ana ta neman arziki.

Kwanci tashi hukumar jiragen kasa dake da ma’aikata kimanin 3505 a duk fadin kasar nan da kuma makarantar koyar da aiki da tukin jirgin kasa dake legas duk suka fara sukurkucewa. Itadai wannan makaranta har yau har kwanan gobe tana nan kuma ana karatu ana yaye dalibai, amma hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya wadda akafi sani da Railway yanzu ta shiga wani hali na ha’u’lai inda kamfanin ya tarwatse baka ganin komai sai karafa da tarin shara da tsoffin gine-gine tun na turawan mulkin mallaka a duk jihar da layin dogo na jirgin ya bi.

A wancan lokacin da ake amfani da jirgin kasa zaka iske duk titunan kasarnan suna da kyau babu gargada tundaga badagari har zuwa baga duk inda kaga titi da kyansa da lafiyarsa, da wahalar gaske kaga mota tayo laftun kaya tana bin kwalta duk wani kaya mai nauyi da za ayi doguwar tafiya da shi yana tashar jirgin kasa; wata kila wannan shi ne dalilin da yasanya tituna suke da ingancin gaske a wancan lokacin.

Amma abin yanzu ba haka yake ba. Kusan kasar nan tafi kowace kasa bada mamaki a duniya domin bawai komawa baya kawai Najeriya ta ke yi ba kawai aguje a sukwane take komawa baya kuma a murgude. Yanzu maganar da muke dukkan wadan can jirage da suke safara daga kudu zuwa Arewa sun daina wato sun zama tarihi dukkan wata safara yanzu ana yenta ne adogayan motoci masu daukar kaya fife da kima.

Kusan ashekaru 1960 zuwa 1970 dukkan manyan gurare a Najeriya zaka iske da wutar lantarki inda alokacin nan Masallacin juma’a na kofar gidan mai martaba sarkin kano lantarki ake kunnawa a ya yinda masallacin dakin Allah mai alfarma da ke makka acibalbal ake kunnawa ballantana ma kayi tunanin jirgin kasa acan. Amma yanzu bazaka kamanta Najeriya da Saudiyya ba wajen wutar lantarki haka idan ka dauki sufurin jirage kasa sunyi mana fintinaku. Domin yanzu haka akwai irin jirgin nan mai tashi kamar kiftawar ido mai gudun tsiya yana yawo ko ina a kasar.

Alokacin marigayi tsohon shugaban Umaru kasa Musa ‘Yaradua ambayarda kwangilar gyaran hanyar dogo daga legas zuwa kano ga wani kamfaninkasar cana amma har yanzu wannan zance shima shiru ka keji. Ko yaushe sufurin jiragen kasa zai dawo ka’in da na’in a Najeriya? Oho; hana rantsuwa akwai kana nan jirage da suke safara misali a legas da kaduna da kano wanda suna yi ne iyakar jihohinsu. Allah ya kaimu lokacin da harkar jirgin kasa zata koma kamar da a Najeriya.


No comments:

Post a Comment