Sunday, March 13, 2016

Ta'addancin Da Shiah Sukaiwa Mai Martaba Sarkin Hadejia


TA'ADDANCIN 'YAN SHIAH GA MAI MARTABA SARKIN HADEJIA

A ranar Juma'ar wannan makon mai karewa ne, 'yan Shiah suka yiwa fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia tsinke, inda suka aikata Ta'addqnci ga Mai Martaba Sarki. Rahotanni sun nuna cewsr 'yan Shiah sun shiga harabar Fadar sarki da nufin zanga zanga dauke da kwalaye da takardun bango da suke nuni da a saki Shugabansu da ke tsare hannun sojoji.

Wannan dalili yasa 'Yan Shiah sukaiwa Mai Martaba sarki ihu da jifan ayarin Dogaransa da duwarwatdu da kwalaye. Wannan kadan ne daga cikin irin ayyukan Ta'addanci da Shiah suka jima suna aikatawa a Duniya. Su din daman wasu mutane ne da basa kaunar zaman lafiya a ko da yaushe.

Dan haka muna kira ga mahukunta da su dauki mataki na hana yin duk wata zanga zangar 'Yan Shiah a ko ina a kuma ko da yaushe. Ba daidai bane, hukumomi su zubawa wasu mutane ido suna daukar doka a hannunsu suna yiwa mutane abinda suka ga dama ba tare da an taka musu birki ba.

Muna kara yin Adduah ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Hadejia, Allah ya kara masa lafiya. Ya kare shi daga dukkan sharrin masu sharri. Ya yi masa garkuwa da garkuwarsa. Allah ya daukaka darajarsa da masarautarsa. Allah ya karawa Sarki Lafiya. Wadannan Shedanun mutane Allah kai mana maganinsu a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale
13-03-2016

3 comments:

  1. Cure-cure baya hana mutuwa. Yan Shi'ah dai karshen ya zo

    ReplyDelete
  2. Yan shi'ah Kar shen ku yazo la'anan Nu tur da ku

    ReplyDelete
  3. Yan shi'ah Kar shen ku yazo la'anan Nu tur da ku

    ReplyDelete