Monday, July 23, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #2


Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #2

Ya ‘yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan makon domin cigaba da bayanin da muka somo a makon da ya gabata akan muhimmancin amfani da lokaci a cikin wannan wata mai dumbin falala na Ramadhan. Ya ‘yan uwa masu girma kamar yadda muka sani, yanzu tuni azumi ya fara samun waje yana baje kolinsa, gari tuni ya gama daukar haramar karbar wannan bako, alhamdulillahi bako ya sauka lafiya, kusan duk inda ka shiga acikin garuruwanmu zaka ga alamun cewar lallai akwai azumi a bakin mutane, domin yawan ciye-ciye da lashe-lashe da akeyi da rana kusan yanzu babu, masallatai sun cika da ambaton Allah, duk inda ka zaga sautin karatun Tafseer ne ke tashi, gidajen Radiyo da Talabijin kusan duk sun maida hankulansu kacokan akan wannan wata, muna fatan Allah ya sa muna daga cikin ‘yan tattun bayi.

Ya ‘yan uwa masu girma, ya zo a cikin ingantaccen Hadisi wanda Bukhari ya fitar da shi a cikin littafinsa, wanda sahabin Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam Huzaifa Ibnul Yaman Allah ya yarda da shi ya ruwaito cewa, naji Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam yana cewa “Fitinar mutum ga iyalansa, da dukiyarsa, da makwabcinsa yin sallah da Azumi suna kankare wannan fitina”. Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani yana daga cikin fituntunun wannan zamani, Allah ya jarrabi mutum da muguwar mata, ko kuma Allah ya jarrabi mutum a cikin dukiyarsa ko kuma Allah ya jarrabeka da mummunan makwabci. To idan Allah ya sanya ka tsinci kanka a irin wannan hali ka sani Manzon Allah ya riga ya baka mafita.

Lallai wannan lokaci na Azumi lokaci na da ake bukatar mu zage dantse wajen yin Ibada. Ibada ta Azumi da Sallah da kyauta da Sadaqa da sada zumunci, wadan nan sune abubuwan da ya kamata mu baiwa muhimmanci a cikin wannan wata, alhamdulillahi kusan yanzu idan ka je masallatanmu a lokacin sallar tarawihi ko kuma Asham zaka samu masallatai sun cika makil da jama’a, hakika wannan babban abin farinci ke ne kwarai; amma wani kuma abin mamakin da yake cikin wasu daga cikin matasanmu zaka samu suna tozarta sallar farilla, misali zaka samu wani tunda Allah ya wayi gari babu sallah ko daya da ya halarta a cikin Jam’I amma kuma yana gaggawar zuwa jam’in sallah Asham, kaga ko shakka babu wannan ya tozarta sallar farilla, domin ita ce ahakku akan ya yi ta cikin jam’I amma ya ki yin haka, lallai wannan babban kuskure ne ya ‘yan uwa lallai mu dage da yin dukkan salloli cikin jam’i.

Sannan kuma, akwai wani Nau’I na matasanmu wadan da su kuma suna Azumi amma ba sa yin sallar kwata-kwata. Wannan ma wani babban tashin hankali ne, ace mai azumi baya kiyaye sallah, lallai mu sani tozarta Azumi ne, mutum ya ki yin sallah dagangan, wasu sun dauka lokacin Azumi lokaci ne na a shafe tsawon dare anata kallon tashoshin Zee Aflam ko MBC2, MBC MAX, MBC Action, domin a shagaltar da idanu, wai saboda a samu damar yin dogon bacci da rana, wannan babban kuskure ne ya  ‘yan uwa masu girma, lallai yadda muke rayar da rana da Azumi da karatun al-qurani da zikiri, to haka ya kamata mu rayar da dare, domin samun dacewa da rahamar Allah acikin wannan wata

Yan ‘yan uwa masu girma, yana daga cikin kuskuren da muke aikatawa a cikin azumi da kuma bata lokacinmu shi ne, a duk lokacin da aka ce maka yamma tayi jama’a kowa na hanzarin ya koma gida domin buda baki tare da iyali, sai ka samu mutane suna warware ladan azuminsu ta hanyar zage-zage da cin mutuncin juna akan hakkin amfani da hanya, dan hakuri kalilan da mutane zasu yi, amma sai ka samu ana ta tayar da jijiyar wuya da maganganu marasa dadi, lallai wannan babban kuskure ne, kuma hasarar lokaci muke yi mai daraja, domin gab da faduwar rana, ko lokacin faduwar rana wannan shi ne lokacin buda baki, a kuma wannan lokacinne ake son mutum ya yi addu’ar buda baki bayan ya sanya wani abu a cikinsa, amma sai kaga muna hasarar wannan dama. Ya ‘yan uwa lallai mu guji aikata dukkan wasu ayyuka da zasu iya kaiwa zuwa ga warwarar azuminmu.

Ya ‘yan uwa, masu girma lallai ya kamata mu sani cewa lallai azumi garkuwa ne, a cikin wani hadisi da sahabin Manzon Allah Mu’azu bin Jabal ya ruwaito wanda turmizi ya fitar da shi yana cewa, wata rana Manzan Allah ya ce min Ya Mu’az shin bana nuna maka kofofin alkhairi ba, sai n ace e ya manzon Allah, sai ya ce Azumi garkuwa ne. lallai idan muka kalli wannan hadisi zamu gane cewar lokacin da muke dauke da Azumi a bakinmu ba lokaci bane da zamu tsaya muna bata lokaci ko cacar baki akan wani abu kankani ba.

Yauma zan dakata anan sai Allah ya kaimu mako mai zuwa zamu ci gaba da wannan bayani. Allah ya karbi wannan ibada tamu, Allah ya sa ba kishirwar banza muke yi ba. Allah ya sa muna daga cikin wadan da zasu samu rahamarsa subahanahu wata’ala.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment