Tuesday, January 31, 2012

Karya da Gaskiya a Tsakanin ‘Yan Najeriya

Karya wani mummunan laifi ne da yake maida mutum mai kima ya zama maras kima, haka kuma karya na maida babba ya koma karami. Ma’ana babu abin da zai zubar maka da kima cikin kankanin lokaci kamar karya ita ke bata tarihi da zuriyya, wannan cema ta sanya koda lokacin jahiliyya mutane kan kyamaci yin karya, da yawan mushurukai suna kyamatar karya a wancan lokacin saboda irin illar ta da suka sani ta zubar da kima da daraja da bata tarihi. Bayan da addinin musulunci ya zo ya sake tabbatar da haramcin karya ga wanda ya yi imani. Karya tana kai mai yinta zuwaga munafurci kamar yadda hadisi ya zo cewa alamar munafuki guda uku ce kuma karya ita aka fara ambata. Kaga wannan ya sake bayyana munin karya.

Menene ma’anar karya: karya dai ita ce bayyana abu sabanin yadda yake wato akasin abin da yake gaskiya ne, ko kuma mutum ya kudure wani abu a zuciyarsa na gaskiya amma ya bayyana sabaninsa. Ana iya yin karya ta hanyar Magana wato mutum ya fadi abin da yake ba haka ne zahirinsa ba. sannan kuma akanyi karya ta hanyar nune, hakana kuma kanyi karya ta hanyar sanya sutura da cin abinci da dukkan sauran fannonin rayuwa ana iya yin karya akansu. Zakaga wasu mutane sun yarda da tafiyar da rayuwarsu bisa karya komai nasu idan ka gani karyane daga maganarsu zuwa tafiyarsu kai hattana sutura da abin hawa da gidan zama wasu duk karya ne a rayuwarsu.

Domin zakaga a Najeriya talaka yana karyar talauci haka kuma mai kudi yana karyar arziki. Talaka bai yarda da talaucinsa ba haka shima mai kudi bai yarda da arzikinsa ba, zakaga mutum talaka mai iyali yana ta tunanin canza sabuwar wayar salula, kaga duk ya tada hankalinsa sai ya mallaki wayar Blackberry bayan ba wannan ne abin da ya dameshi ba, shi kuma mai kudi kaga yana ta hakilon canza mota sabuwar yayi al’hali shima ba wannan ne abinda ya kamaceshi ba. Na taba ganin wani talaka da yake rayuwa da kyar da wahala amma kuma tunaninsa shi ne ya samu kudi ya sayi talabijin samfurin Plasma kaga ko shakka babu wannan ya so yiwa kansa karya.

Karya a tsakanin al’umma: kusan yanzu karya ta zama ruwan dare musamman a tsakanin al’ummar Najeriya idan nima banyi karya ba ina iya cewa karya kusan ta rinjayi gaskiya a dukkan al’amuranmu na yau da kullum, domin idan ka dauki dukkan fannoninmu cike suke da karairayi da zancen banza, zakaga wasu sunfi gamsuwa kayi musu karya sama da kafadi gaskiya, don su zasu haska maka yadda zakayi musu karya. Kuma ita karya kusan zakace ana koyarta ne tun a gida, wato mahaifiya kan yiwa danta karya miji kanyiwa matarsa karya haka itama tana yi masa karya don haka a wannan yanayi sai ka samu yaro ya tashi ya koyi karya tun yana cikin gida. Musamman yanzu da mafi yawancin mutane suka mallaki wayar salula zaka ka samu tana daga cikin abin da ya sake mai da mutane makaryata, kusan kididdiga ta nuna cewa akwai layukan wayar salula miliyan 90 a Najeriya nasan a dukkan wadan da suka mallaki wadan nan layuka da wahala ka samu wanda baitaba yin karya ta hanyar wayar salularsa ba, mutum baya jin wata damuwa yana cikin daki a zaune ga matarsa ga dansa za’a doka masa kira amma sai kaji yace yana kasuwa ko yana kan hanya alhali kuma gashinan tare da iyalansa. Kaga kenan karara yana bada sako ga iyalansa cewa shidin makaryaci ne. gwari-gwari zaka iya cewa akwai makaryata miliyan 90 a Najeriya Allah masani. Kusan yanzu karya babu babba babu yaro wala mace wala namiji, ba malami ba jahili. Kusan kowa na sharata iyakar iyawarsa.

Bari mu dauki wani bangare mu buga misali da shi wato siyasa. Kusan a bayyane ta ke cewa duk ‘yan siyasarmu makaryata ne, domin da wanda yake tallar kansa da wanda yake tallata shi duk makaryata ne. Abin mamaki shi ne zakaji ana tallar mutum a kafafen watsa labarai ana baiyana wasu abubuwa wadan da duk mai hankali yasan karya ne hattana shi mai karantawar yasan karya yake fada amma kuma a haka ake rayuwa. Sannan wani Karin abin mamaki dan siyasa zai zo yana fadawa mutane karya shi yasan karya yake kuma suma jama’a sun san karya yake amma kuma a haka yake Magana har ake tafa masa, sai karasa gane shin wace irin al’umma cemu! Kusan duk dan siyasar da zai zo ya bayyana hakikanin manufarsa ta gaskiya da wahala kaga anyarda dashi amma idan ya yi karya sai kaji ana tafi harda fito. Duk da ban taba ji da kunnena ba amma naji jama’a na fada cewa a Najeriya akwai ‘yan siyasar da sukayiwa al’umma alkawarin famfon fura da nono, kaga da zaka ga wannan dan siyasar da sai ka bashi sunan shugaban makaryata ‘yan siyasa.

Idan muka kalli al’amari na baya bayan nan abin da shugaban kasa ya yi na janye tallafin man fetur na tabbatar da ya furta wannan a lokacin da yake yakin neman zabe da babu wani dan Najeriya da zai saurareshi, amma saboda munfi son a fada mana karya shima yazo ya shara irin tasa kuma ya zauna lafiya. A lokacin jam’huriya ta biyu Awolowo yana yakin neman zabe da yaje jihar Abiya inda a lokacin babu abin da yake tafiya a kasuwanninsu kamar gwanjo yace idan yaci zabe zai hana shigo da gwanjo Najeriya, wasu ‘yan siyasa suka ja hankalinsa me yasa zai furta wannan maganar bazai bari ba kawai sai yaci zabe sannan ya aiwatar da nufinsa; ya kada baki yace shikam Allah ya sawwake ya yiwa talaka karya don ya bashi kuri’a! kaji ‘yan siyasa masu gaskiya.

Haka kuma idan ka dauki fannin saye da sayarwa kusan zakace nanne babbar hedikwatar karya domin da mai saye da mai sayarwa duk sunyi tarayya wajen karya, kana da gaskiyarka kana saida abu mai saye zaisa kayi masa karya, misali ya tambayeka nawa ne farashin abu kaza tsakani da Allah ka gaya masa amma sai kaji ya nemi ragi kuma kayi masa kaga kenan duk sunyi musharaka cikin wannan karyar, kaji mutum yana ihu yana tallar hajarsa amman da ka bincikashi sai kasamu cikakken makaryaci yake. Ga al’gus ko tsoron Allah basaji.

Wannan ce ma ta sanya na tuna da wani labarin uba da dansa akan karya. Wani uba ne ya kira yaronsa cewa yazo ya tukashi a mota ya kaishi cikin gari domin yanada wani taro da zai halarta, bayan da suka iso cikin gari sai yace da dansa kaje ka kai wannan motar wajen gyara ya yi masa kwatance daman ya saba kai gyaran wajen yace masa ka dawo da wuri domin karfe 5 na yamma zamu koma gida, bayanda yaro yaje aka kammala gyara kawai sai ya nufi sinima inda ya shantake yana kallon kwallo bai tashi duba lokaciba sai da karfe 6 na yamma tayi nan da nan hankalinsa ya tashi ya garzaya inda ya tarar mahaifinsa yana jiransa ya tambayeshi a ina katsaya sai yace masa ba’a gama gyaran da wuriba sai yanzu, bai san cewa tuni mahaifin ya buga waya yaji ko angama gyaran aka shaida masa cewa tun karfe 3 na rana aka kammala gyaran, yace da yaron naji takaicin da ka kasa jure gayamin gaskiyar inda kaje amma wannan ba laifinka bane domin a matsayina na mahaifinka nine ban baka tarbiyyar da zaka iya jure gayamin gaskiyaba. A saboda haka zan ladabtar da kaina da komawa gida a kafa, saboda wannan kuskuren da nayi na kin koyarda dan da na Haifa yadda zai jure gayamin gaskiya.

Ya mai karatu ka kalli wannan labarin da kyau kaga cewa uba ya ladabtar da kansa a saboda laifin da dansa ya aikata, inda ya gano ashe tun asali shine bai koyarda dansa yadda zai gaya masa gaskiya ba, lallai akwai darasi acikin wannan labarin. To haka karya take maida mutum mai kima ya koma maras kima, sannan mutum mai mutunci ya koma marashi. Na tuna badakalar karyar da tsohon shugaban kasar Amurka Bill Williams Clinton ya yi lokacin yana shugaban kasa na gaskiyar alakarsa da Monica Lewinsky kusan wannan ce ta sanya Mr Clinton furfura a wancan lokaci. Ka duba yadda gaskiya take da kima a wajensu.

Babban abin da zai baka haushi da mamaki shi ne manyan mutane da malamai suna shara karya. Wani abu da zai tabbatar maka da wannan ka duba dukkan wasu taruka da ake shiryawa a Najeriya idan kaga anbuga takarda za’a fara taro 10 na safe insha Allahu sai karfe 11 ko 12 zakaji anfara alhali kuma ga jadawali anbuga kamar gaske, kaga wannan shi ne zai nuna maka isa matuka da mukayi wajen shirya karya hattana a takarda. Idan shugaban ya yi karyar fara taro akan lokaci inaga sauran al’umma? Ya dan uwana ka tsaya ka kalli kanka tsakaninka da Allah sau nawa kake yin karya a kullum wannan shi ne zai tabbatar maka da waye kai?

Gaskiya tayi karanci: malamai suka gaya mana cewa lokaci zaizo da sai anyi doguwar tafiya kafin a samu mutum mai gaskiya. Gashi dai tana da saukin fada a baki kusan kowa zai iya fada amma ba kowa zai iya aikata ta ba, mutane suna son gaskiya amma basa son ace kodai sufara ko kuma ta fada a kansu. Misali jama’a da dama suka bukaci gwamnati ta aiwatar da shari’ar Musulunci amma a kano a shekarar 2008 da hukumar Hizba tace ta hana mata hawa baburdin acaba jama’a suka ringa ihu akan basaso suna munanan kalamai akan hakan, ka duba babur fa kawai inaga sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum, ina zaton da za’a sami wata gwamnati tace dole kowane mai awo ya cika mudu kamar yadda shari’ah tace da sai kaji jama’a na korafin cewa ai ba su kadai bane macuta! Matsalarmu itace idan kace mutum ya yi gaskiya sai ya kafa maka hujjar ai ba shi kadai bane yake aikata badai-dai ba su wane da suwane duk suna aikatawa.

Ya dan uwa gaskiya itace ke maida yaro ya zama dattijo, ita ke sanya soyayya ta gaskiya a zukatan al’umma ga mai yinta. Wannan ce ma ta sanya ko a maganarmu ta yau da kullum baka tabajin ance wane gaskiyarsa ta kare ba, kullum sai dai kaji cewa wane karyarsa ta kare, Allah ka arzurtamu da fadar gaskiya da kuma aiki da gaskiya. Ka kalli yanayinmu komai da ka sani babu gaskiya acikinsa domin mai faskare zai yi maka karya mai nika hatsi zaiyi karya, abin tambaya shin wane mai gaskiya acikinmu? Kullum muna addu’ar Allah ya kawo mana masu gaskiya amma muda kanmu muke tona musu asiri kuma muke basu hanyar da zasu yi mana karya, sai kaga wasu suna yimaka mu’amalar da zasu kureka kawai su sanya kayi karya, ko kuma yawan tambaya marar amfani wanda da yawa wasu kanyi karya don su kare kansu.

Daga karshe ina addu’a ga kaina da sauran al’umma Allah ya bamu ikon fadar gaskiya da kuma karbar gaskiya komai dacinta, Allah ka sanya gaskiyarmu ta rinjayi karyarmu, Allah ka karemu daga sharrin da yake tattare da karya. Ina rokon Allah abin da na fada ya zama dai-dai wannan daga gareshi ne abinda kuma nayi kuskure ko tuntuben al’kalami ko kuskuren fahimta wannan daga gareni ne Allah ya yafemin.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@hotmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment